HANKALI KE GANI BA IDO BA, wani ya je Kano ya ce bai ga mota ba

Taken wannan mukalar ya kamata a ce Tsumagiyar kan hanya, amma sai aka kira ta da Hankali ke gani ba ido ba, wani ya je Kano ya dawo bai ga mota ba, ko kadan shi kan shi wannan maganar hankali ba zai dauka ba, domin babu yadda za a yi a ce mutum ya shiga birnin Kano idanun shi lafiya, shi ma lafiya amma a ce bai ga mota ba. Sau tari rashin ko in kula ke kai mu zuwa ga wani tafarki makaskanci, domin idan ba rashin lura ba, al’ummar Hausawa ‘yan Arewacin Najeriya, mu ne wadanda lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka suka same mu da suturarmu, makarantunmu, sarautarmu, sana’o’inmu, shugabancinmu, kokarinmu, sadaukartarwarmu.
Kusan babu wani abu da suka tarar da ba shi da tsari wanda al’ummar Hausawa suke yi. Amma a wannan lokaci sai ga shi an bar mu a baya ta fannoni daban-daban, musamman ta fannin abin da duniya ke ciki, za ka samu duk abin da ya shigo na zamani mutanenmu su ne kan gaba, amma ba wai suna kan gaba wajen gano yadda ake yin wannan abu ba ne, a a, sai dai yadda za su kara lalacewa, duk abin da bai kamata a yi ba ta Bangaren almubazzaranci da girman kai za ka samu malam Bahaushe shi ke kan gaba, kama daga abin da ya same muna rashin hadin kai da shugabanci, wanda ko da mun yarda da rashin shugabanci ai bai kamata mu yarda da kaskanci ba.
Za a yi hakuri tabbas da abin da sauran bayanai ‘a wannan makalar , domin a zahiri ba muna magana da kowa ba ne, face muna magana a kan abin da wannan al’umma ta mayar da kanta. Kuma mun yi wannan maganganu ba domin tozarci ba illa domin mu tashi yaranmu da manyanmu mazanmu da matayenmu mu gyara, domin idan muka gyara, dadin ba na kowa ba ne illa namu.
Kusan idan ka duba mutane goma da suke amfani da Computer, za ka samu bakwai daga ciki ba su san amfaninta ba, ban da jin wakoki babu wani amfani da suke ganin ta na da shi. Biyu daga cikin ragowar ukun za ka samu sun san muhimmancinta, amma ba su san yadda za su yi amfani da ita ba. Shi kuwa ragowar gudan shi ne kawai ya san ta, ya san muhimmancinta, sannan ya kuma iya amfani da ita. To, kai mai karatu kana wane Bangare ne?
Duba wayar tafi- da- gidanka, za ka samu ga shi mutum ya mallaki wayar amma abin takaici da ban haushi bai san yadda zai sarrafata ba domin ta yi mashi aiki kamar yadda aka tsara. Waya da muke gani ita ma computer ce, kuma kusan abubuwa da ake iya yi da Computer da yawa ana iya yi da ita waya, sannan kuma ita waya ba kira kadai ake yi da ita ba, ko kuma ajiyan karatu ko video ko kuma ajiyar hotuna a ciki ba, a a wasu wayoyin sun wuce da hakan. Saboda haka, za ka sa mu mutum ba shi da wata harka da yake yi da waya wacce ta wuce ya kira ko a kira shi sai ka tarar mutum ya sayi wayar dubunnnai wacce dalilin da yasa aka yi ta ba kawai a yi amfani da ita wajen kira ba ne amma shi sai ya Buge da yin kira kawai.
A misali duk wata waya da ta zamanto ana iya samun abin da ake cewa WAF a jikinta, to ita wannan wayar za ta iya zama maka wani abu da za ka iya amfani da shi wajen shiga Internet ko kuma duba Email, ko kuma amfani da ita wayar wajen gane hanyar wani gari idan ta Bace maka, da dai makamantansu.
Idan muka koma ta Bangaren makarantunmu, idan ka sami daliban da suke karatun Computer ko kuma suna karatun ‘Electrical Engineering’ ko kuma suna karatun ‘Architecture’ sannan a ce malam Bahaushe ne, kuma a yi sa’a ya mallaki wannan compter, ka ga ai ya sami kayan aiki wanda idan ya yi amfani da ita ta hanyar da ta dace za ta saukaka mashi.
Amma abin takaici da Bacin rai, sai ka samu banda kide-kide da wake-wake da kallace-kallacen bidiyo da kuma buga ‘Game’ babu abin da ya saka a gaba. Ina son ku dubi abokanan zamanmu wadanda suke zuwa karatu irin wanda kuke yi, za ka ga sun fi mayar da hankali ta kowanne fanni, sannan suna yin wasa su ma, amma da lokacin karatu ya zo za ka ga lallai sun nuna cewar ba wasa ya kawo su ba. Matsala ta farko da mu ka samu ita ce talasuranci da girman kai, idan ba ka san abu ba, wai kai kafi karfin a ce wani da bai kai ka ba, ya koya maka karatu. To, sai meye idan ka fahimta ya isa ya kwace daga wurinka ne? Ko kuma idan ka iya me ka ragu da shi.
Haka kuma da yawa daga cikin mutanenmu wadanda suke son su ga sun fahimci karatu za ka samu iri na ne wanda bai samu fandisho mai kyau ba, ya yi makarantar firamare ta gwamnati, makarantar sakandire ta gwamnati kuma a lokacin ba a san ciwon kai ba, sai da aka shiga jami’a sannan hankali ya zo ake son a fahimci karatu. To, a inda matsalar take a lokacin da ake karatun yana kokarin ya fahimci Turancin da ake yi mi shi, bai gama fahimtar Turancin ba ballantana ya fahimci abin da malami ya shigo koya masu, ga lokacin tashi ya yi, haka zai ta tafiya a cikin irin wannan yanayi har ya gama makaranta. Daman a wannan lokaci makarantu kadan ne ba su koma “Business Center” ba wato wajen hada-hadar kasuwanci, inda wanda ya iya ba komai ba ne, wanda bai iya ba, idan yana da kudi, to shi zai fito da sakamako mai kyau. A cikin kashi saba’in cikin dari na dalibanmu wadanda suke yin karatun fannin Computer sai ka sa mu ga shi sun yi karatun, sun fahimci Turancin amma matsalar ba su sami kyakkyawan gwaji ba (Practical). Domin sau da yawa in ban da yanzu da ake samun wasu gogaggun malamai wadanda suke kara bincike ta fannoni da dama, sai ka samu malami yana karantar da fannin computer amma bai taBa hada wani program ko da guda daya ba, ballantana daliban da yake koyarwa su ma su kirkiri nasu.
Idan muka dawo ta irin rashin sanin muhimmancin al’amura ko kuma an san su, amma rashin kulawa ne? Sai ka ga gwamnati ta ware miliyoyin kudade ta sayo Kwamfutoci masu yawa, amma sun zama ba su da amfani ko kadan. Domin a lokacin da hukumar makaranta ke sanar da ta kawo sababbin Kwamfutoci a lokacin wasu daga cikin masu kula da kayan suke murnar kakarsu ta yanke saka, domin sun san tun daga lokacin da hukumar makarantar za ta zube wadannan kaya ba ta kara komawa ta kansu. Malamai da dalibai da suke karatu a kan wadannan computer za ka samu su ma ba su damu da wadannan kayan karatunba. Hukumar makaranta takan yi asara mai yawa a lokacin da aka ce akwai wani abu da ya lalalce a makaranta, ba wai ina son in Bata garin ba ne, amma kusan kwangilar da ake baiwa masu gyaran kayan makarantu wani lokaci sukan ninka kudin sau biyar ko sau hudu a kan asalin farashin da ake siyarwa a kasuwa. Duk wadannan ba ci gaba ba ne ga al’ummarmu da kuma kasarmu.
Wani abin ban haushi sai ka samu wasu malamai da ba su fahimci fannin da suke karantarwa ba, idan a ka yi rashin sa’a suka sami dalibai masu hazaka, wadanda ko da wani lokacin ba su Internet ba su dakin karatu, sai ka sami wadannan malamai suna tsangwamarsu, idan wadannan dalibai ba su ba su hadin kai ba wajen nuna su daliban ba komai ba ne, to, wannan malamin zai sha alwashin sai ya sa wadannan daliban sun maimaita shekara guda.
Wadansu kuma dalibai matsalarsu malamai ne, domin idan aka samu wani malami wanda ya san abin da yake yi, sannan kuma ya samu wayewa ta fannin karatunshi, ya dau alwashin sai dalibai sun fahimci karatun ta hanyar da ta dace domin a sami ingantacciyar al’umma, a daidai wannan lokacin dalibai za su shiga zagin shi, suna kiran shi da sunaye na banza, sannan idan wadannan yaran iyayensu masu fada a ji ne, sai su kai karar shi malamin wurin hukumar makaranta, ita kuma hukumar makaranta ba za ta yi bincike ba sai ta fara tsangwamar malamin.
Nasan wani malami da ya cire makudan kudade ya dauko hayar Projector domin ya nunawa dalibai yadda za su koyi yin project, daliban daman babu wanda suka fi jin haushi kamar wannan malamin domin suna ganin ya takura masu, amma da hankali a yanzu ya zo masu, da tsarin da ya yi masu amfani da shi su ma suke kokarin tafiyar da rayuwarsu.
Ta fannin manhajin da ake karantarwa a makarantunmu na jami’o’i sai ka sami wannan manhajin karatun ya girmi shi kan shi malamin da yake karantar da shi, hukumar makaranta ba ta da hakkin yi wa shi manhajin garanbawul domin yin hakan, tsarin gwamnatin tarayya ne, sannan kuma za ka samu ta fannin Computer mafi yawan Programing language da ake amfani da su sai ka tarar wanda su Bill Gates suka yi amfani da shi ne, wanda ya kai shekaru ashirin da biyar zuwa talatin da fara amfani da shi. Dalilin haka za ka tarar da dalibai babu tserereniya tsakaninsu, domin daman abin da ake karantar da su bashi da wata nasaba. Akwai ‘project’ da ake baiwa dalibai wanda ya shafi programming wanda asalin wanda ya fara yin wannan program din, a wancan lokacin ya sha wahala kafin ya kammala shi, to tun daga wancan lokacin sai dai a yi ta jujjuya shi, daga wannan, zuwa wancan haka za a yi tayi ta juyawa har zuwa lokacin da Allah ya so.
Idan ka dawo ta fannin wasu daga cikin malami za ka samu dalibai ne suke yi masu karatunsu, domin da zarar malami ya koma karo karatunsa, kuma aka yi rashin sa’a malamin bai damu da karatun ba, to, daliban shi sun shiga uku da ‘assignment’ kenan, idan dalibi ya duba manhaja karatunsa zai ga babu shi a ciki, kuma irin wannan assignment ba za ka ga ya fito a cikin test ba ballantana a jarabawa. Sai wani abin bantakaici da malamai suke yi na matsawa dalibai da assignment domin su hada “Course Material” su dawo suna siyarwa dalibai a farashi mai dan karan tsada.
Idan kuma ka tara wadanda ake ce masu wizard ko guru koma hacker cikin kashi casa’in cikin dari ba su san komai ba, amma a gafarce ni, idan ka kwatantasu da wadanda suke kiransu da wandanan sunaye za ka samu lallai haka ne.
Amma idan aka dawo ga zahiri, za ka samu lallai ba su san komai ba, duk wanda za ka ji ana kiran shi da wannan suna, ba ya wuce ya san yadda zai sarrafa wani program ne a computer, haka idan aka samu mutumin da ya dan iya amfani da Microsoft Word, kamar zai iya rubuta wasika ya yi printing, sai kaji ana ce masa guru. Kuma idan aka samu ya iya cire program ko ya iya sanya wani program ko kuma ya iya installation sai kaji ana kiran shi da suna injiniya Wanda idan muka dubi abin da ido na gaskiya za mu gane cewar duk burga ce domin kusan wadannan abubuwan da za ka ba kan ka awa uku ka kuma natsu ka sa kaifin basira kafin awa ta biyar ta shiga za’ a fara kiranka da wannan sunaye kaima.
Kuma da za ka leka “Business Center” na mu sai ka sha mamaki, domin idan ka duba za ka samu wadanda suke fi kwarewa wajen sarrafa wani program ko application za ka samu ba su taBa karatun computer ba, ko kuma sun yi karatun, amma baya wuce ‘’yar diploma irin wacce muka yi ba. Gaskiya dole ka jinjina masu a lokacin da suke amfani da ita computer, yadda suke sarrafa ita kanta computer za su ba ka sha’awa. Abubuwan kusan hudu za su Bata maka rai idan ka tambaye su.
(1) Wani version suke amfani da shi? Zai ce maka bai sani ba, domin akwai wani da aka tambaye shi wane irin Operating System yake amfani da shi ya ce Antivirus.
(2) Da za ka ambaci sunan wani Bangare na jikin compter da asalin sunan ta ba zai ga ya maka ba, shi dai yana amfani da computer iya abin da yaga ana amfani da shi.
(3) Da za ka tambaye shi meye amfanin wannan program abin da ya ke ganin yafi kwarewa a wajen amfani da shi, shi zai ce maka shi ne amfanin shi, ko da kuwa ba haka ba ne.
(4) Abu na karshe idan ka tambaye shi ya kana binkice game da wannan harkar tashi? Zai gaya maka ai shi ko makaranta bai je ba.
Idan kuwa ka koma ta Bangaren cin banza a harkar computer, musamman ma a Abuja, tun da yaran sun fahimci iyayen su ba su san computer ba, za ka samu kashi saba’in cikin dari na yaran da suke zagaya ofisoshin manyammu ba su san komai ba, wanda banda bagun kwali babu abin da suke yi, su dai manyammu abin da suke yi shi ne idan yana son ya bude wani file bai gane ba sai ya ce computer ta sami matsala, shi kuma gogan naka da zarar ya ji wayar mai gidanshi ai ya san ta fadi gasasshiya, wasu ma yaran su ne suke installing wasu program da zai sa computer ta sami matsala a daidai wani lokaci, yadda dole a neme su, idan hakan ta faru.
Mafi yawan compter da ake kankare su, ba ita ba ce matsalar , bai wuce a ce a rage program da compter take tashi da su ba.
Kusan Kwamfutoci kashi casa’in da biyar cikin dari da ake ‘formatting’ a Najeriya ko kadan ba lalacewa suke yi ba, da zarar mutum ya ga na’urar shi ta fara wata ‘yar matsala sai ka ga injiniya ya ce sai an yi formatting dinta. Za ka ga wanda ya iya bude imel ko browsing a internet keyi mata fankama da cewar ya gama da ita, wanda da za ka tambaye shi wata matsala ‘yar karama za ka sha mamaki amsar da zai baka. Idan ka duba sai ka samu kwata-kwata abubuwan da ake amfani da su a computer bama iya sarrafasu kashi goma cikin dari na abin da ya kamata a sarrafa sai dai ‘downloading’, duk wani website da za’a sami kayan cuta mun kware a shigar shi, burin mu kullun mu dauko wani application da zai bamu damar rusa katangar da kamfanonin sadarwa na waya da suke yi domin mu samu damar yin browsing, kowa ya iya amfani a facebook da twitter, da yawa sun iya shiga torrent su yi downloading software.
Yanzu mu shi ke nan iya inda muka sa gaba ke nan? Duk wandancan suna ye da ake kiran mu guru ko hacker ko wizard da ake yi saboda mun iya sarrafa program kawai, to, wadanda suka kirkire su su kuma kira su da mene?
Don na iya installing program sai a kira ni engineer? Wadanda suka kirkiri na’urar a ce masu mene?
Ina rantsuwa da ALLAH wanda raina ke hannunsa, da za mu dawo daga harkar karBa mu komo harkar bayarwa da za mu fi samun daukaka.
Ka duba canji da ake samu a lokaci da aka bude makarantar informatics da take Kazaure a Jihar Jigawan Najeriya, kusan yanzu idan ka samu dalibai goma ‘yan’ Arewacin Najeriya wadanda suke amsa sunan su a harkar Computer. A wannan lokaci za ka samu biyu sun yi Informatics ne, idan kuma duka goman ka samu ‘yan makarantar ne, za ka samu takwas suna son su je karo ilimi, halin rashi ya hana su zuwa. Kuma da gaske ba kowane dan Informatics ba ne yasan abin da ya ke yi amma, saboda malaman da suka samu gogaggu, kwararru za ka samu da yawa daliban sun san abin da suke yi sannan suna son su ci gaba da karatunsu, kodayake a wancan lokaci, kafin a Bata al’amuran karatun.
Wani abin jin dadi shi ne, idan ka tafi kasahe irin su Malesiya ko Singafo za ka samu daliban da suke karanta fannin computer da fannonin kimiyya da fasaha da Bangarorin likitanci za ka samu mutanen mu ne. Alhamdu Lillah, da alama ana samun nasara, duk da cewa wasu daga cikin yaran iyayen su ne suka dauki nauyin kai su su yi karatu, wasu kuma gwamnatin jiha da ta taraiya su suka dauki nauyin su. Ana samun wasu daga cikin su sun mayar da hankali matuka kuma suna fahimtar abin da ya kai su. Wasu abin ban takaici ba su san ma abin da ya kai su ba, sun yi tsammani yawon shakatawa suka je yi da yawon bude ido, domin wasu daga cikin su banda shaye-shaye da harkar klob ba a bin da ya ke a gaban su. Wasunsu kuma komawa suke safarar miyagun kwayoyi abin dai babu dadin ji.
Amma duk da haka an samu canji idan ka danganta da baya lokacin da manya-manyan jami’o’inmu suke kokarin yaye hazikan dalibai, amma su daliban ban da confusion babu komai a kawunansu (a gafarce ni) wanda idan aka yaye dalibai dari uku, zai wahala a samu dalibai guda dari wadanda suka fahimci inda suka sa gaba.

Gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba.
Dukkanin wadannan bayanai da na jero, ko da wasa ba na yi ba ne domin in ci zarafin wani ba ne, kuma ban ambaci sunan wani domin wulakanci ko tozartarwa. Na yi haka ne domin mai karatu ya gane inda muka sa gaba, da kuma irin aikin da ke kanmu.
Koma baya ka tambayi kanka wace al’umma ce ta ci gaba a duniya wacce ba tayi amfani da harshen iyayenta ba. Kama daga kasar turai ka san mafi yawan ilimi da suke takama da shi na wasu ne, suka dauko shi suke canja shi ya koma yaren su, koma kasahen Faransa ka ga duk littattafai da suke karantar da ‘ya’yansu na (Physics da Chemistry) da makamantansu duk da yaransu ake rubutashi. Ko za ka gaya mini mutanen Jamus da Faransanci suke koyar da al’ummarsu? Da Jamusanci ne suke koya masu, koma kasar Itali da Rasha cikin su babu wanda yake jin yaren wani, amma sun sami ci gaba ta fannin kimiyya da fasaha, bani kasahen Larabawa da Canisawa ana ganin irin cigaban da suka samu su ma suna amfani da yarensu ne. Ballantana Indiya wanda suka yi wa duniya zarra ta fannoni da dama, Turanci shi ne yaren kasar amma mafi yawanci takardunsu da Hindu ake karanta su kuma dukkan wadannan kashashe dana ambata ba wai sun yi haka ba ne domin kabilarka ba ne sai domin wanda yake jin yarensu ko da bai iya karatu ba ya fahimci in da a ka sa gaba.
Ni ma ba nace a koma koyar da yaranmu da Hausa ba ne, ko Yarbanci, ko kuma Inyamiranci ba, amma abin da nake nuna mana shi ne, da za a mayar da hankali wajen koyar da yaran Turanci su sanshi so sai, gwamnati ta dauki nauyin koyar da shi tun daga Firamare yaro ya san shi sosai, ai ka ga ba illa ba ne. Shi fa wannan yare da ake kokarin a koyar da karatu da shi, daidai yake da kowane yare, idan har a makarantar Computer irin tawa zan karantar da yaran Hausawa ilimin computer su fahince ta kamar yadda wanda ya koya da turaci, koma ya fishi, banga dalilin da zai sa in koyar da shi da Turanci ba. Wannan ra’ayina ne, ba kuma dole ya zama ra’ayin mai karatu ba.
Koma Bangaren noma, akwai ci gaba da aka samu mai yawa ta fannin noma da kiwo a zamanance, wanda idan da abubuwan da ake karantar da mutanenmu a ‘department na Agric’ za a samu wasu su rinka koyar da iyayenmu na gida a yarukansu da za a ga ci gaba mai yawa. Da yawa daga cikin mutanen da suke za ka samu ba su taBa zuwa makaranta ba, amma tun da ya gaji noma kaka da kakanni zai gaya maka tsawon kwanaki da tumatiri yake yi kafin ya fito, ya kuma gaya maka kwana nawa yake yi idan ya fito kafin ya fara fure, ya kuma gaya maka kwana nawa yake yi idan ya fara ‘ya’ya har ya isa a cire shi. Wannan a takaice abin da muke nunawa a nan, shi ne gaskiya babu wayarwa a cikin abubuwanmu na yau da kullum, burinmu shi ne idan ka gane abu to baka son kowa ya gane, shi wannan ilimin na banza ne ba za ka ka je lahira a tambayeka ba, kuma duk ilimin da ka yi na zamani amfanin shi shi ne ka koyar da wani idan har ya koya duk lokacin da ya sami alheri zai tuna ka, kuma ya yi maka addu’a ko da baya so.
Saboda haka, ina kira ga duk wani mutum wanda yake kishin ci gaban al’ummar shi, da ya sa dammara wajen wayarwa da al’ummarshi ta fannin ci gaba a rayuwa, idan ya san abu, wani yazo tambayarshi ya sanar da shi, ba wai alfahari ba kusan duk abin da na iya ko na sani wani ya koya mini, ni kuma banga dalilin da zai sa wani ya tambaye ni, abu in ce ban sani ba, alhali na sani.
Daga karshe ina kira ga duk wanda zai karanta wannan mukala da ya yi mini adalci, sannan a sani dukkan wadannan bayanai da na fadi a cikin wannan mujallar, maganganu ne irin wanda Malamai, da dalibai suke yi a kowane lokaci a kowane lungu. Kiran sunan ‘Informatics’ da nayi, domin cancantane ba domin son kai ba, da na kira sunan makarantar da na yi, domin so-so ne amma son kai ya fi. Kuma irin wannan abu da wasu shuwagabanni suke yi na hangen nesa yaci a jinjina masu, kamar kirkiro irin wadannan makarantu da ake yi a jahohinmu na Arewacin Najeriya. Wanda a da sai dai ka ji labarin a makwabtanmu.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *