HANKALI KE GANI BA IDO BA, wani ya je Kano ya ce bai ga mota ba

Taken wannan mukalar ya kamata ace Tsumagiyar kan hanya, amma sai aka kira ta da Hankali ke gani ba ido ba, wani ya je kano ya dawo bai ga mota ba, ko kadan shi kan shi wannan maganar hankali ba zai dauka ba, domin babu yadda za ayi ace mutum ya shiga birnin Kano idanun shi lafiya, shi ma lafiya amma ace bai ga mota ba. Sau tari rashin ko in kula ke kai mu zuwa ga wani tafarki makaskanci, domin idan ba rashin lura ba, alummar hausawa ‘yan Arewacin Najeriya, mu ne wadanda lokacin zuwan turawan mulkin mallaka su ka same mu da suturarmu, makarantunmu, sarautarmu, sana’o’inmu, shugabancinmu, kokarinmu, sadaukantarmu, kusan babu wani abu da su ka tarar da ba shi da tsari wanda alummar hausawa suke yi.. Amma a wannan lokaci sai ga shi an bar mu a baya ta fannoni daban-daban, musamman ta fannin abin da duniya ke ciki, zaka samu duk abinda ya shigo na zamani mutanenmu sune kan gaba, amma ba wai suna kan gaba wajen gano yadda ake yin wannan abu ba ne, a a, sai dai yadda za su kara lalacewa, duk abin da bai kamata ayi ba ta bangaren almubazzaranci da girman kai za ka samu malam bahaushe shi ke kan gaba, kama daga abinda ya same mu na rashin hadin kai da shugabanci, wanda ko da mun yarda da rashin shugabanci ai bai kamata mu yarda da kaskanci ba. Za ayi hakuri tabbas da abinda sauran bayanai ‘a wannan makalar , domin a zahiri ba mu na magana da kowa ba ne, face muna magana akan abinda wannan al’umma ta mayar da kanta. Kuma mun yi wannan maganganu ba domin tozarci ba illa domin mu tashi yaranmu da manyanmu mazanmu da matayenmu mu gyara, domin idan muka gyara, dadin ba na kowa bane illa namu.

Kusan idan ka duba mutane goma da suke amfani da Computer, za ka samu bakwai daga ciki basu san amfaninta ba, ban da jin wakoki babu wani amfani da su ke ganin ta na da shi. Biyu daga cikin ragowar ukun zaka samu sun san mahimmancinta, amma ba su san yadda za su yi amfani da ita ba. Shi kuwa ragowar gudan shi ne kawai ya san ta, ya san mahimmancinta, sannan ya kuma iya amfani da ita. To kai mai karatu ka na wane bangare ne?

Duba wayar tafi- da- gidanka, za ka sa mu ga shi mutum ya mallaki wayar amma abin takaici da ban haushi bai san yadda zai sarrafata ba domin ta yi mi shi aiki kamar yadda aka tsara. Waya da muke gani ita ma computer ce, kuma kusan abubuwa da ake iya yi da Computer da yawa ana iya yi da ita waya, sannan kuma ita waya  kira kadai ake yi da ita ba, ko kuma ajiyan karatu ko video ko kuma ajiyar hotuna a ciki ba, a a wasu wayoyin sun wuce da hakan. Saboda haka, za ka sa mu mutum ba shi da wata harka da yake yi da waya wacce ta wuce ya kira ko a kira shi sai ka tarar mutum ya  sayi wayar dubunnnai wacce dalilin da yasa aka yi ta ba kawai ayi amfani da ita wajen kira bane amma shi sai ya buge da yin kira kawai. A misali duk wata waya da ta zamanto ana iya samun abinda ake cewa WAF a jikinta, to ita wannan wayar za ta iya zama maka wani abu da zaka iya amfani da shi wajen shiga Internet ko kuma duba Email, ko kuma amfani da ita wayar wajen gane hanyar wani gari idan ta bace maka, da dai makamantansu.

Idan mu ka koma ta bangaren makarantunmu, idan ka sami daliban da suke karatun Computer ko kuma suna karatun Electrical Engineering ko kuma suna karatun Architecture sannan ace malam bahaushe ne, kuma ayi sa’a ya mallaki wannan compter, ka ga ai ya sami kayan aiki wanda idan yayi amfani da ita ta hanyar da ta dace za ta saukaka mishi. Amma abin takaici da bacin rai, sai ka samu banda kide-kide da wake-wake da kallace-kallacan bidiyo da kuma buga game babu abin da ya saka a gaba. Ina son ku dubi abokanan zamanmu wadanda suke zuwa karatu irin wanda kuke yi, za ka ga sun fi mayar da hankali ta kowanne fanni, sannan su na yin wasa su ma, amma da lokacin karatu ya zo za ka ga lallai sun nuna cewar ba wasa ya kawo su ba. Matsala ta farko da mu ka samu ita ce talasuranci da girman kai, idan ba ka san abu ba, wai kai kafi karfin ace wani da bai kai ka ba, ya koya maka karatu. To, sai meye idan ka fahimta ya isa ya kwace daga wurinka ne? Ko kuma idan ka iya me ka ragu da shi.

Haka kuma da yawa daga cikin mutanenmu wadanda su ke son su ga sun fahimci karatu zaka samu iri na ne wanda bai samu fandisho mai kyau ba, yayi makarantar firamare ta gwamnati, makarantar sakandire ta gwamnati kuma a lokacin ba a san ciwon kai ba, sai da aka shiga jami’a sannan hankali ya zo ake son a fahimci karatu. To, a inda matsalar take a lokacin da ake karatun yana kokarin ya fahimci turancin da ake yi mi shi, bai gama fahimtar turancin ba ballantana ya fahimci abinda malami ya shigo koya musu, ga lokacin tashi yayi, haka zai ta tafiya a cikin irin wannan yanayi har ya gama makaranta. Daman a wannan lokaci makarantu kadanne basu koma “Business Center” ba wato wajen hada-hadar kasuwanci, in da wanda ya iya ba komai ba ne, wanda bai iya ba, idan yana da kudi, to shi zai fito da sakamako mai kyau. A cikin kashi saba’in cikin dari na dalibanmu wadanda suke yin karatun fannin Computer sai ka sa mu ga shi sun yi karatun, sun fahimci turancin amma matsalar ba su sami kyakkyawan gwaji ba (Practical). Domin sau dayawa in ban da yanzu da ake samun wasu gogaggun malamai wadanda suke kara bincike ta fannoni da dama, sai ka samu malami yana karantar da fannin computer amma bai taba hada wani program ko da guda daya ba, ballantana daliban da yake koyarwa su ma su kirkiri nasu.

Idan muka dawo ta irin rashin sanin mahimmancin al’amura ko kuma an san su, amma rashin kulawa ne? Sai ka ga gwamnati ta ware miliyoyin kudade ta sayo computoci masu yawa, amma sun zama basu da amfani ko kadan. Domin a lokacin da hukumar makaranta ke sanar da ta kawo sababbin Computoci a lokacin wasu daga cikin masu kula da kayan suke murnar kakarsu ta yanke saka, domin sun san tun daga lokacin da hukumar makarantar  za ta zube wadannan kaya ba  ta  kara komawa ta kansu. Malamai da dalibai da suke karatu a kan wadannan computer  za ka samu su ma basu damu da wadannan kayan karatunba. Hukumar makaranta ta kan yi asara mai yawa a lokacin da aka ce akwai wani abu da ya lalalce a makaranta, ba wai ina son in bata garin ba ne, amma kusan kwangilar da ake baiwa masu gyaran kayan makarantu wani lokaci sukan ninka kudin sau biyar ko sau hudu akan asalin farashin da ake siyarwa a kasuwa. Duk wadannan ba ci gaba bane ga alummarmu da kuma kasarmu.

Wani abun haushi sai ka samu wasu malamai da ba su fahimci fannin da suke karantarwa ba, idan a ka yi rashin sa’a suka sami dalibai masu hazaka, wadanda ko da wani lokacin ba su Internet ba su dakin karatu, sai ka samu wadannan malamai suna tsangwamarsu, idan wadannan dalibai basu ba su hadin kai ba wajen nuna su ba komai bane, to, wannan malamin zai sha alwashin  sai ya sa wadannan daliban sun maimaita shekara guda. Wadansu kuma dalibai matsalarsu malamai ne, domin idan aka samu wani malami wanda ya san abinda yake yi, sannan kuma ya samu wayewa ta fannin karatunshi, ya dau alwashin sai dalibai sun fahimci karatun ta hanyar da ta dace domin a sami ingantacciyar al’umma, a daidai wannan lokacin dalibai za su shiga zagin shi, suna kiranshi da sunaye na banza, sannan idan wadannan yaran iyayensu masu fada aji ne, sai su kai karar shi malamin wurin hukumar makaranta, ita kuma hukumar makaranta ba za ta yi bincike ba sai ta fara tsangwamar malamin. Wanda nasan wani malami da ya cire makudan kudade ya dauko hayar Projector domin ya nunawa dalibai yadda za su koyi yin project, daliban daman babu wanda suka fi jin haushi  kamar wannan malamin domin suna ganin ya takura musu, amma da hankali a yanzu ya zo musu, da tsarin da yayi musu amfani da shi su ma suke kokarin tafiyar da rayuwarsu.

Ta fannin manhajin da ake karantarwa a makarantunmu na jami’o’i sai ka samu wannan manhajin karatun ya girmi shi kanshi malamin da yake karantar da shi, hukumar makaranta ba ta da hakkin yiwa shi manhajin garanbawul domin yin hakan, tsarin gwamnatin tarayya ne, sannan kuma za ka samu ta fannin Computer mafi yawan Programing language da ake amfani da su sai ka tarar wanda su Bill Gates suka yi amfani da shi ne, wanda ya kai shekaru ashirin da biyar zuwa talatin da fara amfani da shi. Dalilin haka zaka tarar da dalibai babu tserereniya tsakaninsu, domin daman abinda ake karantar da su bashi da wata nasaba. Akwai project da ake baiwa dalibai wanda ya shafi programming wanda asalin wanda ya fara yin wannan program din, a wancan lokacin ya sha wahala kafin ya kammalashi, to tun daga wancan lokacin sai dai ayi ta jujjuyashi, daga wannan, zuwa wancan haka za a tayi ta juyawa har zuwa lokacin da lokacin da Allah ya so.

Idan ka dawo ta fannin wasu daga cikin malami za ka samu dalibai ne suke yi musu karatunsu, domin da zarar malami ya koma karo karatun, kuma aka yi rashin sa a malamin bai damu da karatun ba, to, dalibanshi sun shiga uku da assignment kenan, idan dalibi ya duba manhaja karatunsa  zai ga babu shi a ciki, kuma irin wannan assignment ba za ka ga ya fito a cikin test ba ballantana a jarabawa. Sai wani abin bantakaici da malamai suke yi na matsama dalibai da assignment domin su hada “Course Material” su dawo suna siyarwa dalibai a farashi mai  dan karan tsada.

Idan kuma ka tara wadanda ake ce musu wizard ko guru koma hacker cikin kashi casa’in cikin dari ba su san komai ba, amma a gafarceni, idan ka kwatantasu da wadanda suke kiransu da wandanan sunaye zaka samu lallai haka ne.

Amma idan aka dowo ga zahiri, za ka samu lallai basu san komai ba, duk wanda za ka ji ana kiranshi da wannan suna, ba ya wuce ya san yadda zai sarrafa wani program ne a computer, haka idan aka samu mutumin da ya dan iya amfani da Microsoft Word, kamar zai iya rubuta wasika yayi printing, sai kaji ana ce masa guru. Kuma idan aka samu ya iya cire program ko ya iya sanya wani program ko kuma ya iya installation sai kaji ana kiran shi da suna injiniya Wanda idan muka dubi abin da ido na gaskiya za mu gane cewar duk burga ce domin kusan wadannan abubuwan da za ka ba kan ka awa uku ka kuma natsu ka sa kaifin basira kafin awa ta biyar ta shiga za’ a fara kiranka da wannan sunaye kaima.

Kuma da zaka leka “Business Center” na mu sai ka sha mamaki, domin idan ka duba zaka samu wadanda suke fi kwarewa wajen sarrafa wani program ko application za ka samu ba su taba karatun computer ba, ko kuma sun yi karatun, amma baya wuce yar diploma irin wacce muka yi ba. Gaskiya dole ka jinjina musu a lokacin da suke

amfani da ita computer, yadda suke sarrafa ita kanta computer  za su ba ka sha’awa. Abubuwan kusan hudu za su bata maka rai idan ka tambaye su,(1) wani version suke amfani da shi, zai ce maka bai sani ba, domin akwai wani da aka tambaye shi wane irin Operating System yake amfani da shi yace Antivirus.

(2) Da za ka ambaci sunan wani bangare na jikin compter da asalin sunan ta ba zai gaya maka ba, shi dai yana amfani da computer iya abin da yaga ana amfani da shi,  iya abin ya iyakera.

(3) Da za ka tambaye shi meye amfanin wannan program abin da ya ke ganin yafi kwarewa a wajen amfani da shi, shi zai ce maka shine amfanin shi, ko da kuwa ba haka ba ne.

(4) Abu na karshe idan ka tambaye shi ya kana binkice game da wannan harkar tashi? Zai ga ya maka ai shi ko makaranta bai jeba.

Idan kuwa ka koma ta bangaren cin banza a harkar computer mu samman ma a Abuja, tun da yaran sun fahinci iyayen su ba su san computer ba, za ka samu kashi saba’in cikin dari na yaran da suke zagaya ofisoshin manyammu  basu san komai ba, wanda banda bagun kwali babu abin da suke yi, su dai manyammu abin da suke yi shine idan yana son ya bude wani file bai gane ba sai ya ce computer ta samu matsala, shi kuma gogan naka da zarar yaji wayar mai gidanshi ai ya san ta fadi gasasshiya, wasu ma yaran sune suke installing wasu program da zai sa computer  ta sami matsala a daidai wani lokaci, yadda dole a neme su, idan hakan ta faru.

Mafi yawan compter da ake kankaresu, ba ita ba ce matsalar , bai wuce ace a rage program da compter take tashi da su ba.

Kusan computoci kashi casa’in da biyar cikin dari da ake formatting a Najeriya ko kadan ba lalacewa su ke yi ba, da zarar mutum ya ga na’urar shi ta fara wata yar matsala sai kaga injiniya yace sai an yi formatting dinta. Za ka ga wanda ya iya bude imel ko browsing a internet keyi mata fankama da cewar ya gama da ita, wanda da zaka tambaye shi wata matsala yar karama za ka sha mamaki amsar da zai baka. Idan ka duba sai ka samu kwata-kwata abubuwan da ake anfani dasu a computer bama iya sarrafasu kashi goma cikin dari na abin da yakamata a sarrafa sai dai downloading, duk wani web site da za’a sami kayan cuta mun kware a shigar shi, burin mu kullun mu dauko wani application da zai bamu damar rusa katangar da kamfanonin sadarwa na waya da suke yi domin mu samu damar yin browsing, kowa ya iya amfani a facebook da twitter , da yawa sun iya shiga torrent su yi  downloading software.

 Yanzu mu shi ke nan iya inda muka sa gaba ke nan? Duk wandancan suna ye da ake kiran mu guru ko hacker ko wizard da ake yi sabo da mun iya sarrafa program kawai, to, wadanda suka kirkire su su kuma kira su da mene?

Don na iya installing program sai a kirani engineer? Wadanda suka kirkiri na’urar ace musu mene?

Ina rantsuwa da ALLAH wanda raina ke hannunsa, da za mu dawo daga harkar karba mu komo harkar bayarwa da za mu fi samun daukaka.

Ka duba canji da ake samu a lokaci da aka bude makarantar informatics da take Kazaure a Jihar Jigawan Najeriya, kusan yanzu idan ka samu dalibai goma ‘yan’ Arewacim nigeria wadanda suke amsa sunan su a harkar Computer a wannan lokaci za ka samu biyu sun yi informatics ne, idan kuma duka goman ka samu ‘yan makarantar ne , za ka samu takwas suna son su je karo ilimi, halin rashi ya hana su zuwa. Kuma da gaske ba ko wane dan informatics bane yasan abin da ya ke yi amma, saboda malaman da suka samu gogaggu, kwararru za ka samu da yawa daliban sun san abin da suke yi sannan suna son su ci gaba da karatunsu, ko da yake a wancan lokaci, kafin a bata al’amuran karatun.

Wani abin jin dadi shine, idan ka tafi kasahe irin su Malaysia ko Singapore za ka samu daliban da su ke karanta fannin computer da fannonin kimiya da fasaha da bangarorin likitanci za ka samu mutanan mune. Alhamdu Lillah, da alama ana samun nasara, duk da cewa wasu daga cikin yaran iyayen su ne suka dauki nauyin kai su suyi karatu, wasu kuma gwamnatin jiha da ta taraiya su suka dauki nauyin su. Ana samun wasu daga cikin su sun mai da hankali matuka kuma suna fahimtar abin da ya kai su. Wasu abin ban takaici basu san ma abin da ya kai su ba sun yi tsammani yawon shakatawa su ka jeyi da yawon bude ido, domin wasu daga cikin su banda shaye-shaye da harkar klob ba a bin da ya ke a gaban su. Wasunsu kuma koma wa suke safarar miyagun kwayoyi abin dai babu dadin ji.

Amma duk da haka an samu canji in ka danganta da baya lokacin da manya-manyan jami’o’inmu suke kokarin yaye hazikan dalibai, amma su daliban ban da confusion babu komai a kawunansu (agafarce ni) wanda  idan aka yaye dalibai dari uku zai wahala a samu dalibai guda dari wanda suka fahimci inda suka sa gaba.

Gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba.

Dukkanin wadannan bayanai da na jero, ko da wasa bana yi bane domin in ci zarafin wani ba ne, kuma ban  ambaci sunan wani domin wulakanci ko tozartarwa. Na yi hakane domin mai karatu ya gane inda muka sa gaba, da kuma irin aikin da ke kanmu.

Koma baya ka tambayi kanka wace al’ummace ta ci gaba a duniya wacce ba tayi amfani da harshen iyayenta ba. Kama daga kasar turai kasan mafi yawan ilimi da suke takama da shi na wasu ne, suka daukoshi suke canja shi ya koma yaren su, koma kasahen faransa kaga duk littattafai da suke karantar da yayansu na (Physics da Chemistry) da makamantansu duk da yaransu ake rubutashi. Ko za ka gaya mini mutanen jamus da faransanci suke koyar da al’ummarsu? Da jamusanci ne suke koya musu, koma kasar Italy da Rasha cikin su babu wanda yake jin yaren wani, amma sun sami cigaba ta fannin kimiya da fasaha, bani kasahen larabawa da canisawa ana ganin irin cigaban da suka samu suma suna amfani da yarensu ne. Ballantana India wanda suka yi wa duniya zarra ta fannoni da dama, turanci shine yaren kasar amma mafi yawanci takardunsu da hindu ake karanta su kuma dukkan wadannan kashashe dana ambata ba wai sun yi haka bane domin kabilanka  bane sai domin wanda yake jin yarensu koda bai iya karatu ba ya fahimci in da a kasa gaba.

Ni ma ba nace a koma koyar da yaranmu da Hausa ba ne, ko Yarbanci, ko kuma Inyamiranci ba, amma abinda nake nuna mana da za a mayar da hankali wanjen koyar da yaran turanci su sanshi so sai, gwamnati ta dauki nauyin koyar da shi tun daga Firamare yaro ya sanshi sosai, ai kaga ba illa bane. Shi fa wannan yare da ake kokarin a koyar da karatu da shi, daidai yake da ko wane yare, idan har a makarantar Computer irin tawa zan karantar da yaran hausawa ilimin computer su fahince ta kamar yadda wanda ya koya da turaci, koma ya fishi, banga dalilin da zai sa in koyar da shi da turanci ba. Wannan ra’ayina ne, ba kuma dole ya zama ra’ayin mai karatu ba. Koma bangaren noma, akwai ci gaba da aka samu mai yawa ta fannin noma da kiwo a zamanance, wanda idan da abubuwan da ake karantar da mutanenmu a department na Agric za a samu wasu su rinka koyar da iyayenmu na gida a yarukansu da za a ga ci gaba mai yawa. Da yawa daga cikin mutanen da suke za ka samu ba su taba zuwa makaranta ba, amma tunda ya gaji noma kaka da kakanni zai gaya maka tsawon kwanaki da tumatiri yake yi kafin ya fito, ya kuma gaya maka kwana nawa yake yi idan ya fito kafin ya fara fire, ya kuma gaya maka kwana nawa yake yi idan ya fara ‘ya’ya har ya isa a cire shi. Wannan a takaice abinda muke nunawa a nan, shine gaskiya babu wayarwa a cikin abubuwanmu na yau da kullum, burinmu shine idan ka gane abu to baka son kowa ya gane, shi wannan ilimin na banzane ba zaka kaje lahira a tambayeka ba, kuma duk ilimin da kayi na zamani amfaninshi shine ka koyar da wani idan har ya koya duk lokacin da ya sami alheri zai tuna ka, kuma yayi maka addu’a ko da baya so.

Sabo da haka, ina kira ga duk wani mutum wanda yake kishin ci gaban alummar shi, da ya sa dammara wajen wayarwa da al’ummarshi ta fannin ci gaba a rayuwa, idan ya san abu, wani yazo tambayarshi ya sanar da shi, ba wai alfahari ba kusan duk abinda na iya ko na sani wani ya koya mini, ni kuma banga dalilin da zai sa wani ya tambaye ni, abu in ce ban sani ba, alhali  na sani.

Daga karshe ina kira ga duk wanda zai karanta wannan mukala da yayi mini adalci, sannan a sani dukkan wadannan bayanai da na fadi a cikin wannan mujallar, maganganu ne irin wanda Malamai, da Dalibai suke yi a ko wane lokaci a ko wane lungu. Kiran sunan informatics da nayi, domin cancantane ba domin son kaiba, da na kira sunan makarantar da nayi, domin so-so ne amma son kai yafi. Kuma irin wannan abu da wasu shuwagabanni suke yi na hangen nesa yaci a jinjina musu, kamar kirkiro irin wadannan makarantu da ake yi a jahohinmu na Arewacin Najeriya. Wanda a da sai dai kaji labarin a makwabtanmu.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. assalamu alaikum ma,aikata wannan shashi mai albarka ta duniyar kimiya da fasaha ina son amin bayani yadda ake general setting na yanan gizo gizo wato internent atakaice wanda idan nasa sim card na mtn zaiyi idan kuma nasa etisalat, glo,airtel, duk zaiyi amfani batare da wata matsala ba,kamar na sake setting na configuration. Saina ji diga gareku

  2. Godiya da wannan makala, kuma na gamsu da abubuwan da ka fada, duk ana yinsu a unguwanninmu da makarantunmu da ofisoshinmu, fata dai jama’a a farga a son dukkan amfanonin kwamfuta ba wai kawai a ji kida ba. Kuma a daina raina harshen uwa, don na tabbata da ace da harshen uwa ake koyar da mutanenmu fannonin ilimi da an yi gogayya da mu a ko’ina, amma duk da haka alhamdulillahi. Fata dai a kara himma tun da turanci ya zama shi ne harshen gwamna