Google zai soma fassara zuwa Hausa

Shafin matambayi baya bata wato Google na shirin kara wasu harsunan Afrika ciki hadda Hausa, Igbo, Zulu da Swahili cikin jerin harsunan da yake fassarawa a ‘Google Translate’.

Wata sanarwa da aka buga a shafin Google na ‘Africa Google+’ ya nuna cewar ana bukatar masu fassara ‘yan sa- kai wadanda za su taimaka wajen fassara zuwa harsunan Afrika.

Hakan na nufin cewar wadannan harsunan Afrikan za su shiga cikin jerin harsuna 71 da Google ke fassarawa.

Duk wanda ke sha’awar shiga cikin masu yin fassarar ana tura shi zuwa wani shafin inda zai tantance wata fassara a bisa ma’auni don tabbatar da fassarar ta yi ko kuma a’a.

Wannan zai kasance labari mai dadi ga ‘yan Afrika musamman mazauna kasashen Turai dake fuskantar matsala wajen fassara zuwa harsunan Afrikar.

Daga BBC HAUSA

Related Articles

Yadda ake yin Bincike (search) da Google Search Engine (1)

A wannan rubutu da zan yi, zan raba shi kashi uku, kashi na farko bincike mai sauki, wanda ya ku san kowa shi yafi amfani da shi, sai dai kuma ana amfani da shi cikin kuskure, shine zamu yi dan gyara akai. Kashi na biyu kuwa zamu zurfafa binciken ne, ta wajen amfani da zurfafan hanyoyin yin bincike a shi google search engine, ta yadda yin amfani da wannan hanyar zai saukaka matuka da kuma fitar da sakamako mai inganci. Kashi na uku wanda kuma shine na karshe shi kuma zamu yi bayanin hanyoyin da ake bi a binciken hotuna, video da kuma wurare a dduniya baki daya.

kamar yadda mafi yawa daga cikin mu suka sani, duk wanda yake da waya ko kuma yake da computer da yake son yayi bincike shine ya shiga google. wanda kuma bai san yadda zai yi ba to, zai rubuta www.google.com a wurin da ake rubuta adireshi shafukan internet wanda aka fi sani da Address Bar, da zarar ya rubuta zai bude mishi shafin farko.

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *