Game da mu

Barka da Zuwa
MAKARANTAR DUNIYAR COMPUTER

Barka da zuwa Makarantar Duniyar Computer inda aka ware wannan shiri domin ya wakilci dukkan ilimomi da muke karantar da dalibai da suke zuwa makarantar domin koyon fannoni na Computer. 

Wannan shafin an bude shi ne domin baiwa mutane samun damar sanin karatuttuka a fannoni da dama na bayanin ilimin computer ga masu iya rubutu da karatun da harshen Hausa. 

Makaranta ce da zata dukufa wurin kawo ilimi daban daban a bangarori mabanbanta domin saukake muku wannan ilimomin. 

Haka muna fatan mafi yawan ilimin za’a karantar da shi ne da harshen Hausa domin kaiwa ga inda ake sa ran mutanen mu su kai. 

Kuma muna fatan dukkan bangarorin ilimin zamu karantar da ku kai tsaye ba tare da samun wata matsala ba. 

Mun gode.