Gajiyawar Ahlussunna Wajen Cin Gajiyar Shugabancin Sheikh Bala Lau

Ba kasafai ake samu a cikin al’umma dace da shugaba mai hangen nesa da kuma ganin an ciyar da al’umma ba, musamman al’ummar Musulmai da suke yin da’awar Sunna a Afirka ba. Hasalima a wannan lokacin da shuwagabanni suke cikin ruɗani na rikice-rikicen matsayi da kuma ganin mai za su samu mai kuma za su riƙe da kuma ganin sun handame da kuma yin babakere a cikin al’amuran al’umma, sai ga shi ita Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Allah Ya amsa mata buƙatarta da addu’o’in da ta daɗe ta roƙon Allah na Ya azurta ta da shuwagabanni masu tsoron Allah, tausayi da kuma hangen nesa cikinsu har da Sheikh Bala Lau.

A cikin wannan dogon rubutu da zan yi ba zai iya wadatar da abubuwan amfani da ci gaba da wannan bawan Allah yake gabatarwa ba, da kuma irin ɗimbin nasarori da ya samu a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ba.

Kafin in fara magana a kan nasarori da kuma irin ci gaban da ya kawo sai na fara kawo mana abubuwa da dama da muka rasa da kuma dalilai da ya sanya Duniyar Computer ta ɗauki wannan jarumin shugaba ta kuma ce za ta yi tsokaci na musamman a kansa.

Ɗaya daga cikin matsalolin musulmin Najeriya ita ce, ina muka dosa, bayan kasancewar mun san cewar ga daga inda muka fito. Rashin sanin takamaimai wurin da muka dosa shi ne babban matsalar wannan al’umma. Hakan ta faru ne tun daga lokacin da muka rasa manyan jagororin al’umma kamar su Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (Allah Ya yi mishi rahama), Alhaji Ahmadu Sardaunan Sokoto (Allah Ya yi mishi rahama). Rashin waɗannan bayin Allah ya kawo taɓarɓarewar jagoranci da kuma sanin ina musulmai suka nufa.

Matsaloli ba su da adadi wanda wannan al’umma take fama da su, kama daga haɗin kai na al’ummar musulmai da kuma ƙoƙarin neman ganin an cike gurabun da ya kamata a ce musulman wannan ƙasar sun cike na wuraren ilimi da muƙamai da ma kowane irin fanni.

Shugaban Izala na Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau tare da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Izala na Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau tare da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Musulmai a wannan ƙasar ba su da wata babbar makarantar jami’a ta zamani da za ta ware wani bangaren na al’umma kodai maza zalla ko kuma mata zalla da zasu karantar da ‘ya’yansu ilimi na haƙiƙa da kuma tarbiya ta addinin musulunci.

Wannan al’umma ta rasa yadda za ta kawo wata hanya da zata iya dogaro da kanta na ganin ta kafu da ƙafarta wurin ganin an samu abubuwan more rayuwa da kuma abubuwan da al’umma zata riƙa dogaro da shi wurin tafiyar da al’amuranta na yau da kullum.

Idan muka dawo ta ɓangaren Ahlussunnah a wannan yanki namu na Arewa sai muga cewar mune koma baya matuƙa a cikin harkokin tafiyar da hanyar yin da’awa da kuma yadda ya dace ace muke tafiyar da al’amuranmu na yau da kullum.

Mas’alolin suna da yawa amma bari in taba mana wani bangare da yake damun duk wani Musulmi da yake cikin Arewa, shi ne maganar Asibitin Musulmai wanda ya amsa sunansa, kuma wanda lallai idan kana da kowace irin matsala idan ka je wannan wuri buƙatarka ta biya. Musamman idan muka ce za muyi maganar cakuduwar maza da mata da kuma samun kwararrun likitoci da kuma kayan aiki na zamani sai muga cewar lallai bamu da irin wannan asibiti.

Sheikh Abdullahi Bala Lau lokacin da yake bikin kaddamar da hannaye da kafafuwan robobi
Sheikh Abdullahi Bala Lau lokacin da yake bikin kaddamar da hannaye da kafafuwan robobi

Ya ake ɗaukar aiki, wa kuma ya dace a ɗauka wannan itama matsala ce mai zaman kanta da take damun musulmai kasancewar a baya saboda su Malam Abubakar Mahmud Gumi ana ƙoƙarin ganin an bai wa musulmai haƙƙinsu, amma bayan rasuwarsa sai aka rasa wanda ya damu da ganin an baiwa musulmai guraben da ya dace da su.

Su wane suke wakiltarmu a fannoni da muƙamai a wannan ƙasar, su wane ne suke yin magana da yawun musulmai da kuma ganin an magance ita irin wannan matsalar. Musulmai da suke Majalisar Wakilai da na Dattijai nawa muke da su, sannan suna yin abubuwan su domin kare muradun al’umma ne ko kuma suna yi domin ganin sun wakilci kawunansu da iyalan su da kuma iyayen gidajensu ne?

Ganawar Shugaban Kungiya ta Kasa Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau da Hukumar Wa'azi ta kasar Saudi Arabia a office dinsu dake Makkah ta Kasar Saudi Arabia.
Ganawar Shugaban Kungiya ta Kasa Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau da Hukumar Wa’azi ta kasar Saudi Arabia a office dinsu dake Makkah ta Kasar Saudi Arabia.

Wace hanya al’ummar nan take bi domin ganin mun sami guraben karatu a jami’o’in mu na cikin gida da waɗanda suke ƙasashen ƙetare. Wani irin abu ɗalibai masu ƙaro ilimi suke yi da kuma wani irin gudunmawa za su iya bayarwa a wannan ƙasar idan suka dawo. Wa ya damu da wane irin ilimi ɗalibai suke zuwa nema da kuma wa ce irin aƙida ce suke iya dawowa da ita wannan ƙasa.

Wane irin da’awa ta dace da wannan zamani, ina kuma ya kamata a ce an nufa, da su wa ya kamata a ce ana tafiya, wannan ita ma wata katuwar matsala ce da wannan al’umma ta Ahlussunnah suke fuskanta.

Kwatsam sai ga Bala Lau.

Bayan da Allah Ya ƙaddara rasuwar shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa’iƙamatis Sunna na ƙasa, Sheikh Maigandu Usman, kuma majalisar malamai suka yi ittifaƙin cewar babu wanda ya dace a bai wa wannan muƙamin sai Sheikh Abdullahi Bala Lau. Wannan matsayi da aka ba shi ya rikita shi matuƙa domin duk wanda yake wurin babu wanda bai tausaya mishi ba, wasu ma sai da suka taya shi kuka bisa abin da ya tsinci kansa yana yi na yin kuka a wannan lokaci, ba domin komai ba sai don yana ganin wannan matsayi na farko ba shi ya kamata a ce an bai wa ba, sannnan kuma yaya zai yi da irin waɗancan matsalolin da ita wannan al’umma take ciki.

Daya daga cikin kafanoni da Shugaba ya samar domin rage zaman banza
Daya daga cikin kafanoni da Shugaba ya samar domin rage zaman banza

Allah ba ya shawara da mutum, shi ya fi kowa sanin irin gudunmuwa da kariya da kuma juriya da wannan bawa na Shi zai iya yi a cikin wannan al’umma. Ba zan so in tsawaita bayanai ba game da shi Sheikh Abdullahi Bala Lau a karan kansa ba, domin ba ya bukatar a gabatar da shi kasancewar ko da wane lokaci shi baya ɗaukan kansa a matsayin mai mulki illa jagora.

Mai Son Haɗin Kan Al’umma Ne

Jama’a da dama a farkon sake rabuwar ƙungiyar Izala, suna zargin ɓangaren Sheikh Abdullahi Bala Lau a matsayin ɓangaren da ya zama na ‘yan santsi, amma daga bayan sai jama’a suka fuskanci wannan rabuwa ba ta da alaƙa da wannan ɓangare. Duk wanda yake tare da Sheikh Bala Lau ya san mutum ne mai son al’umma ta haɗu wuri guda, kuma mutum ne mai son ganin Ahlussunnah suna tafiya kan tafarki guda, kuma ya kasance musulmai suna da murya guda ɗaya.

Shugaba Bala Lau a Studio na Manara TV da Rediya a Abuja
Shugaba Bala Lau a Studio na Manara TV da Rediya a Abuja

Misalai da dama sun nuna wannan al’amari na Bala Lau, kasancewar shi ba wai magana kawai ita ce ke nuna son yin abu ba. Ayyukan da yake ya gabatar da kuma uzurori da ya bayar wanda ba a buƙatar faɗinsu a nan, ya isa. Shi kaɗai ne shugaban da ake hawa mimbarinsa a yi kira kai tsaye a kansa. Duk wani dattijon Malami idan ya hau mimbarinsa zai nuna mishi muhimmancin haduwar kai, kuma bai taɓa nuna wa kuma bai taɓa hanawa ba. Hasalima wannan abu yana daga cikin abin da ya fi damunsa.

Amma ya za ka iya, Da Allah Ya so da ya sanya al’umma guda, amma ba za su gushe suna saɓawa juna ba. Duk da irin hanyoyi da yake bi cikin sirri da na fili na ganin an samu haɗin kai ga al’ummar Ahlussunnah baki ɗaya a mataki na ƙasa tare da ‘yan majalisarsa, ya sanya dole ya canza salo tun da shi wannan haɗin kai ba wai Hausawa kawai ake magana ba, sai ya ga ya dace ya haɗa dukkanin Ahlussunnah na Najeriya baki ɗaya, tun daga Yarbawa da Inyamirai da Nupawa wanda Allah Ya duba zuciyarsa ya ga da gaske yake yi ya kuma tabbatar masa da haka.

A yanzu haka dukkan wani al’amari da ya shafi Ahlussunah da suke faɗin ƙasar nan Sheikh Bala Lau yana da masaniya a kai, tun daga kudu da yamma da arewacin kasar Allah Ya tabbatar mishi da haka.

Ba a Najeriya kaɗai ya tsaya ba, ya yi ƙoƙarin haɗa kan Ahalussunnah na Afirka gaba ɗaya, inda ya shirya taro irinsa na farko tun kafuwar wannan ƙungiya na ganin dukkanin Ahalussunah da suke Afirka suna magana da murya guda.

A taron da aka gabatar a makon jiya (17-03-2016) an yi shi ne domin ganin an tattaro Ahalussunah na Duniya su shigo wannan ƙasa domin ganin an tabbatar wa da Duniya cewar musulunci ba shi da alaƙa da ta’addanci kuma a kara ƙulla alaƙa tsakanin dukkanin Musulman Najeriya da kuma sauran Musulman Duniya baki ɗaya. Duk da cewar shi Shugaba ne International kasancewar a yanzu yaƙi ɗan zambo ne, bai bar musulmai ko Ahlussunah zalla su yi wannan taro ba ya haɗa da dukkanin wadansu kungiyoyin addinin musulunci da ma wadanda ba musulmai ba.

Idan kuwa aka zo maganar ɗalibai masu karatu a ƙasashen waje musamman masu karatun addini, kusan babu wata ƙasa da ɗaliban ilimi suke yin karatu da Sheikh Bala Lau bai ziyarce su ba, kuma bai basu wata dama ta a dama da su da yadda za a ƙara bunƙasa wannan tafiya ta sunnah ba. Abu na farko da ya fara yi, shi ne ƙoƙarin tattaro kan waɗannan ɗalibai da saka su cikin da’awa da wa’azi da kuma sanya su cikin jerin masu yin Tafsiri a Masallatan Ƙasar nan baki ɗaya.

Fatu, Fatar Rago da aka tara domin aikin Kungiyar Izala
Fatu, Fatar Rago da aka tara domin aikin Kungiyar Izala

Idan muka zo ga ɗalibai matasa samari, wannan bawan Allah ya yi ƙoƙarin haɗa kan dukkanin samarin malamai matasa wuri guda, wanda ya jawo ɗalibai masu da’awar Salafiyya cikin tafiyar sa, sannan kuma ya kusanto da su cikin jerin al’amuran da ake yi na yau da kullum a cikin wannan tafiya. Wanda ba ya son haɗin kan al’ummarsa ba zai taɓa damuwa da ganin haka ba.

Mai tausayin al’umma ne, da kare martabar su.

Sheikh Abdullahi Bala Lau shugaba ne mai sauƙin ra’ayi da kuma tausaya wa al’ummar musulmi. Wannan ɗabi’a da yake da ita, duk wanda yake tare da shi zai faɗa maka cewar Sheikh Bala Lau mutum ne mai tausayin al’ummarsa domin duk lokacin da aka shirya wani taro da za a tara jama’a burinsa shi ne ganin kowa ya samu abubuwa cikin sauƙi.

Tun daga lokacin da wannan bawan Allah ya tsinci kansa a cikin wannan shugabanci duk lokacin da ake son a shirya wani taro zai tabbatar ba a kaishi inda jama’a za su ƙuntata ba. Zai ga ya yi iya iyawarsa domin an kawo wa’azi ko taro cikin gari ba ƙauye ba domin ka da wadanda ake son su zo domin sauraron wannan wa’azi ko taro su wahala.

Duk wani abu da zai shafi lafiyar al’umma yana kaffa-kaffa da shi. Shi ya sa daga cikin sanarwa da yake bayarwa duk lokacin da za a yi wata tafiya mai nisa shi ne “don girman Allah direbobi ku yi tafiya sannu cikin hankali, ban da gudu banda yin tsere ku tsare rayukan al’umma” Wanann jawabi irin shi kuma zai sake yi lokacin da aka tashi taro. Allah cikin ikonsa an sami sauƙi matuƙa wurin yin haɗura wajen zuwa ko kuma dawowa daga wa’azi.

Idan kuwa ta Allah ta kasance har aka yi hatsari zai yi ƙoƙarin ganin waɗanda suka jikkata ya ɗauki ɗawainiyar kuɗaɗen asibitinsu da kuma zuwa duba so, ko dai shi karankansa, ko kuma ya tura a wakilce shi.

Wa’azi na ƙasa da aka shirya a kwanakin baya wanda aka so ayi a Jihar Kanon Najeriya ya bai wa mutane da dama mamakin wannan bawan Allah, kasancewar ana gobe za a yi wannan taro aka samu marasa tsoron Allah suka kai hari wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kasuwar waya. Wannan bawan Allah ya kira taro gaggawa na masu ruwa da tsaki a cikin wannan ƙungiya ya ce ba zai yiwu a ce jama’a na cikin jimami ba, mu kuma muna taro domin yin wa’azi ba.

Manara TV da Rediyo
Manara TV da Rediyo

A lokacin jama’a da dama sun kasa fahimtar haka, a lokacin aka samu wasu ‘yan uwa suna faɗin ai wannan nuna tsoro ne da kuma gajiyawa da kuma bada ƙofa. Sheikh Bala Lau ya nuna cewar da a ce a sake rasa ran musulmi guda ɗaya a sanadiyarsa gwamma a dakatar da kowane irin taro.

Allah Ya sani wannan bai kuma sanya shi mai rauni idan abin da ya shafi taɓa mutuncin musulunci da musulmai ba. Lokacin da a wannan ƙasa aka rasa ina al’umma za ta nufa idan aka taɓa mutuncinta, a daidai wannan lokaci Allah Ya kawo Sheikh Lau. Kuma ya yi ƙoƙari matuƙa wurin kare mutuncin jama’ar da yake jagoranta da ma waɗanda ba ya jagoranta.

Babu wani cin zarafi da ake yi wa musulmai a wannan ƙasa da bai fito kafafen yaɗa labarai ba ko na gida ko na waje domin nuna rashin jin daɗin sa a kai. Kodawane lokaci kunnesa na jin koke-koke da ƙorafe-ƙorafen al’umma. Wannan shugaba shi ne na farko wanda ya ke kallon mene ne waɗanda ba musulmai ba suke yi ga musulmai duk wani abu da ya kasance na zargi to sai ya bi bahasin abun kuma Allah cikin ikon Sa sai ka ga an sami waraka.

Yaɗa sunna ta hanyoyin sadarwa na zamani

Kasancewar sa wayayyen masani, malamin addini, attajiri, ɗan boko ya fahimci cewar irin kiɗan da ake yi na yaƙar al’ummar musulmi a duniya ya canza, domin a wannan lokacin yaƙin da ake yi ba yaƙi ba ne na makami kawai, ana amfani da kafofin watsa labarai da na sadarwar zamani domin tauye haƙƙoki da kuma faɗin maganganu na karya da kuma ƙage ga al’umma.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kakkafa abubuwa da dama na zamani wanda zai taimaka wurin isar da saƙon Allah da kuma ganin cewar an fahimtar da jama’a abin da yake na gaskiya a cikin wannan addini.

Kafin zuwan Shugaba, babu wata kafa ta zamani koda guda ɗaya da al’umma musulmin wannan ƙasa suka mallaka domin kare martabar addini, amma zuwansa a halin yanzu ya sanya akwai kafofifin yin da’awa sama da guda biyar da suke da’awa zallah ana kuma kallonsu a faɗin duniya ba wai Najeriya ko Afirka kawai ba.

Da farko ya fara ƙoƙarin buɗe shafi ne a Internet inda aka biya kuɗin shekara guda domin ganin ko shafin zai amfanar kamar yadda ake tsammani, ba a cika shekara ba aka samu ci gaba mai yawa, a lokacin ya biya maƙudan kuɗaɗe domin ganin an sabunta gina wannan shafi. A halin yanzu shugaba ya biya kuɗin mallakar sunan shafin da kuma ɗaki mafi girma da sauri a internet har na shekaru goma, wanda zai yi wahala ka sami wani shafi da yake mallakar ƙungiyar addini ce ta biya koda na shekara biyar ne.

Wanann shafi (JIBWIS NIGERIA) wanda ake iya samunsa a tashar http://jibwisnigeria.org ana samun rubutu da sauti da kuma video da harshen Hausa, wanda a ƙarshen shekarar 2015, Shugaba ya sake ganin ya kamata ace wannan ƙungiya tana magana da manyan yarukan duniya domin isar da saƙon Allah. Ya sake biyan maƙuden kuɗaɗe domin ganin an sake fitar da waɗansu shafuka da za su riƙa yin magana da harshen Larabci da Turanci da kuma Faransanci, wanda a halin yanzu a gama gina waɗannan gidaje kuma a na ƙoƙarin fassara abubuwan da suke cikin babban shafin zuwa sauran yarukan.

Daga nan ya sake ƙarfafa wannan tasha ta internet da mallakar shafukan sada zumunta irinsu Facebook da Twitter da WhatsApp da dai makamantansu. Waɗannan shafuka suna isar da saƙon na da’awa da kare ra’ayin addinin musulunci da sunnah baki ɗaya. Waɗannan kafafe a yanzu suna isar da saƙo ga miliyoyin musulman duniya baki ɗaya.

Gidan Talabijin na farko da aka fara yaɗa sunnah a faɗin duniyar nan da harshen Hausa shi ne, Sunna TV wanda wani bawan Allah daga ƙasar Benin Republic ya yi tattaki har zuwa wannan ƙasar domin ya sami bayin Allah jagorori da za su iya lura da wannan gidan talabijin. Allah cikin ikonSa wannan mutumin ya faɗo hannun shugaba kuma Allah Ya taimaki shugaba ya riƙe wannan gidan talabijin ba tare da an sami wata matsala ba.

Daga nan sai ya samu tunatin samar da wata sabuwar kafa wacce za ta riƙa watsa shirye-shiryenta na sauti zalla, inda ya ƙirƙiro da gidan radiyo na intanet mai suna Sunna Redio ko JIBWIS Redio, shi ma wannan gidan rediyo sai da ya biya maƙuden kuɗaɗe domin tsayuwar sa wanda ake iya saurare kowane lokaci ba dare ba rana. Shi ma wannan gidan radiyo ya biya mishi kuɗi har na tsawon shekara goma, baya da kayan aiki na zamani da aka kawo wanda ake turo karatuka da kuma watsa shi daga nan gida Najeriya.

Gina tashar talabijin na Manara Da jami’a ta ƙungiya ta hanyar taimakon kai-da-kai

Bayan da ya fahimci irin matsalolin da al’ummar musulmi suke fama da ita a wannan ƙasa da kuma a wancan lokacin an mayar da taruka da wurin wa’azi wurin tara gidauniya da sunan addini, shugaban da ‘yan majalisarsa suka yi kirari suka daɓa wa kansu wuƙa ba tare da cin maganin ƙarfe ba. Sun furta cewar sun soke duk wani taro da za su kira domin neman a tara kuɗi domin gini ko bunƙasa wani abu. Fahimtar yadda wasu da yawa daga cikin masu kuɗi ba su cika son suna shigowa bainar jama’a su faɗin abin da suka bai wa addini ba, da kuma ganin sau tari idan an tara wannan kuɗi shekara sai ta sake dawowa a sake tarawa ba tare da ganin abun a ƙasa ba.

Abu na farko da ya fara yi shi ne fito da shirin Manara wanda zai haɗa mishi dukkanin masallatan da ake salloli biyar da na juma’a na ƙasar nan baki ɗaya. Wannan shiri yana buƙatar gogaggu sannan ƙwararrun masana harkar kwamfuta da kuma masu ilimin taswira, a inda Allah Ya azurta shi da wasu haziƙan samari suka zo domin tallafa wa wannan tafiya.

Allah cikin ikonSa ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba sai da Kungiyar Izala ta san adadin masallatanta gaba ɗaya da suke cikin Najeriya. Daga nan shugaba da ‘yan majalisarsa suka fito da tsarin dogaro da kai ta yadda dukkan wani musulmi da yake wannan ƙasa zai iya taimakawa da kuɗin daga naira ɗari (N100) zuwa dubu goma (N10,000). Kasancewar yasan yadda aka sha jama’a suka warke ya sanya bai ce zai yi amfani da ofishinsa domin tara wannan kudi ba, sai ya naɗa kwamiti da za su lura da shiga da ficen wannan kuɗi.

Bayan da aka buɗe Account a Ja’iz Bank aka samar da waɗanda za su riƙa saka hannu domin fitar kuɗin sanna aka bayar da wa’adin lokacin da za a fara amfani da wannan kuɗi da al’umma za ta riƙa tarawa. Shi shugaba da ‘yan majalisarsa sun daɗe su na jin yadda jama’a suke ƙorafi game da rashin abubuwan more rayuwa suke ganin idan har al’umma zata bada haɗin kai to babu wani abu da zata nema wurin gwamnati ko kuma waɗansu jama’a.

A lokacin da aka fito da wannan tsari an ƙiyasta aƙalla mutane miliyan ɗaya Ahlussunah za su yi rijister da wannan shiri, wanda ake sa rai idan suka yi rijista za’a fara tara aƙalla miliyan ɗari wanda ake sa rai idan mutane miliyan ɗaya suka saka naira dubu ɗaya da ɗari biyu a tsawon shekara guda za a samu aƙalla naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari biyu.

Wannan shi ne tunanin da shugaba da ‘yan majajisarsa suka yi, wanda ko a lokacin da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yake da rai da aka so a yi irin wannan shiri ba a taɓa tunanin za a iya samun dabarar haɗa wannan kuɗaɗe ba.

Fara haɗa wannan kuɗi ke da wuya shugaba ya fara gabatar da waɗansu irin aikace-aikace wanda a iya tunanin jama’a ba zai yiwu ba. A farkon shekarar 2014 aka kai gudunmuwar kaya na abinci sama da tirela 10 waɗanda kuɗinsu ya kai sama da Naira Miliyan ɗari biyar.

Duk a cikin irin wannan shiri shugaba ya sami makeken fili a hanyar Kaduna zuwa Zariya a garin Rigachikun inda aka ɗora tubalin ginin babbar jami’a ta farko ta ƙungiya. Haka abin yake daga nan aka fara samar da wurin saukar baƙi a garin Abuja wanda a yanzu haka gini ma har an kammala shi.

Daga nan ya dawo garin Kaduna ya buɗe kamfanin ɗab’i wanda ake kiranshi da Manara Press wanda ya ke printers village a Doka Kaduna an sa injin Cord wada yake buga babbar takarda mai girman A2 wanda a wancan lokacin da aka siya ya haura sama da miliyan goma sha biyu.

Bayan da waɗannan ayyukan suka yi nisa sai Shugaba ya ga ya dace a ce ita ƙungiya ta mallaki gidan talabijin nata na kanta da kuma gidan radiyo. A wannan lokaci ne ya fara tunanin yadda za kafa gidan talabijin da radiyo na Manara wanda Allah cikin ikonSa aka samu gudunmuwa daga ɓangarori mabanbanta domin ganin an samar da wannan babbar tasha ta talabijin da radiyo.

Ana cikin waɗannan sai kuma ya zo da wani shirin da ya tallafa wa mutane kusan ɗari huɗu (400) waɗanda suka rasa ƙafafuwa da hannaye. Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sanar da cewar suna yin wannan shiri tare da haɗin gwiwar waɗansu ƙungiyoyi domin ganin an samarwa da waɗannan bayin Allah hannuwa da kafafu wanda wannan shirin tuni an gabatar da ɓangare na farko wanda a yanzu ake kan shirye-shiryen na biyu.

Waɗannan kaɗan kenan daga cikin irin aikace-aikacen alkairi da wannan bawan Allah kuma shugaba jagoran Sunna na Afirka Sheikh Abdullahi Bala Lau yake kan gabatarwa, wanda ba a magana a kan masallatai da ya giggina, da kuɗaɗen makarantu da ake biya, da tallafin abinci da kayan abinci da ake bai wa marayu da gajiyayyu da kuma tallafa wa duk wani matashi mai hazaƙa da ya sami labarin yana buƙatar gudunmuwa domin daurewar ayyukansa. Lallai wannan ba ƙaramin gajiya ba ce ga wannan al’umma.

Gajiyawar al’umma wajen cin gajiyar ayyukan Sheikh Bala Lau

Duk da irin wannan ƙoƙari da wannan shugaban yake yi na ganin jama’ar musulmai sun dogara da kansu har zuwa wannan lokaci akwai jama’a da dama da ba su mayar da hankali ga irin wannan kyakkyawan tsarin ba.

Ni ina ganin samun irin wannan bawan Allah da kuma ‘yan majalisun sa masu alkairi ba ƙaramin nasara ba ce ga wannan al’umma. Domin duk lokacin da aka ce shugaba ba shi da wani abu a zuciyarsa sai yadda zai ga ya sauke nauyin da ya rataya a kansa, kuma shugaba wanda ba shi da girman kai, ba shi da kyama, ba shi da damuwa ai abin da yake buƙata abu biyu ne, na farko taya shi da addu’a, na biyu kuwa taimaka masa da gudunmuwa kowace iri ce da zai san ya aikace-aikacen da yake son yi su tabbata.

Al’ummar Ahlussunnah sun nuna gajiyawarsu ga irin waɗannan ayyukan alkairi da wannan shugaba ya ke gabatarwa, idan muka ɗauki mas’ala guda zamu ga cewar da mun riƙe Manara Project wanda shi kati kawai ake siya da mun yi abubuwan ban mamaki.

Kullum muna ƙorafin cewar ba mu da babban asibiti amma kuma ga shi an fito da yadda za mu gina abin da ya fi asibiti amma kuma babu wanda ya mayar da hankalinsa a kai. Muna da matsalar jami’a ta mata zalla, idan muka riƙe Manara Project kawai kafin shekara biyar da yardar Allah za mu gina katafariyar jami’a ta mata zallah.

Na tabbatar Ahlussunnah da suke Arewacin Najeriya sun wuce miliyan 40 wanda idan da za mu ɗauki wannan hanya ta Manara Project kawai kafin shekara ɗaya za mu samar da kuɗi Naira Biliyan Arba’in da Takwas. Idan kuwa har muka tara wannan kuɗi, maganar yadda za a shiga garuruwa domin gabatar da wa’azi, tura malamai ƙauyuka da ɗaukan ɗawainiyar iyalansu duk an wuce wurin, ba a maganar samar da gidajen kula da marayu da marasa galihu.

Idan muka ɗauki wannan Project na Shekara biyar kawai muna da kuɗin da musulmai sun fi ƙarfin wulaƙanci. Amma gaskiya mun gaza. Domin za ka samu lokacin da wannan shugaba ya bayar da sanarwar cewar da Sallar Layya da ta gabata aka ce ana buƙatar kowa ya bayar da fata, sai da aka sa mu wasu da suke da’awar sunnah suma sun ce suna buƙatar wannan fatu a masallatansu.

Ina fatan wanann dogon tsokaci da na yi a kan wannan bawan Allah zai sa mutane su fahimci kyawawan ƙudurori na Shugaba Abdullahi Bala Lau, da kuma shin muna cin gajiyarsa kamar yadda ya kamata ko kuma mun nuna gajiyawarmu.

Haƙiƙa ba mu bada wata shaida a kan shi ba, sai da abin da muka sani, sannan kuma a kan abin da yake a ɓoye mu bamu zamanto masu sanin gaibi ba.

Allah Ya yi wa Sheikh Abdullahi Bala Lau jagora da ƙara masa lafiya da kuma ƙara taimakonsa da ‘yan majisalisar sa, da dukkanin Malamanmu na Sunna, Ya kuma gafartawa dukkanin musulmi maza da mata yara da manya. Idan tamu tazo Allah Ya sa mu cika da imani amin.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *