Duniyar Computer Institute – Yadda ake amfani da Makarantar

Gabatarwa

Jama’a barkan mu da wannan lokaci sunana Salisu Hassan daya daga cikin malamai a wannan makaranta taku mai Albarka wato Duniyar Computer Institute, ni zan dauke ku cikin wannan darussa wadanda zasu nuna muku yadda zaku yi mu’amala da wannan makaranta tun daga yin rijista har zuwa yadda dalibi zai shiga aji ya yi dukkan darussa da ya dauka da kuma yadda zai yi jarabawa har mallakar takardar shedar yin karatu a wannan makaranta. 

Ina fatan wannan bayanai zasu sanya dukkan dalibai su fahimci dukkanin tsari da dokokin wannan makaranta da kuma yadda zasu yi mu’amala da mu ba tare da samun wata matsala ba. 

Makasudin kirkirar wannan makaranta ta Online

Kamar yadda muka sani wannan makaranta ce da zata rika kawo muku dukkan fannoni da suka shafi ilimin kwamfuta a aikace da kuma baku damar samun ingantacce ilimi a wadannan fanni. 

Amma da farko ya kamata ku sani cewa wannan makarantace da take wakiltar makarantar Duniyar Computer Institute wacce take da matsuguni a Unguwar Sanusi dake garin Kaduna a tarayyar Najeriya. Inda muke karantar da kwasa-kwasai a harshen Hausa da kuma Turanci domin bayar da ingantaccen ilimin kwamfuta ga kowa da kowa. 

Amma kuma muna samun korafi da kiranye-kiranye daga dalibai dake sassan duniya game da son kasancewa cikin dalibai ga shi wadansu garinsu da nisa ba zasu iya zuwa ba. Hakan ya sanya muka ga dacewar bude wani bangare da kowa zai iya kasancewa dalibi kuma ya samu irin wadancan kwasa-kwasai da muke yi a zahiri. 

Muna fatan kashi 90% na dukkan karatukan da zaku samu a wannan makaranta ta Online ya zama da harshen Hausa yake a kuma kowane mataki kasancewar wannan al’umma ta Hausawa zasu samu damar sanin hakikanin ilimin kwamfuta ba tare da mishkila ba. 

Wani abun jin dadi mutum baya bukatar shaidar ilimin boko kafin ya zama dalibi a wannan makaranta. Matukar dalibin yana iya yin karatu da Hausa kuma zai iya mallakar na’urori da ka’idojin wannan makaranta za mu dauke shi. 

Muna fatan wannan makaranta ta zama wata hanya da duk wani malam Bahaushe zai yi amfani da shi domin zama gwani a fanni ilimin kwamfuta da kuma zama daya daga wadanda za a dama da su a fagen kimiya da fasaha. 

Dalilin yin wannan tambihi

Dalilin yin wannan tambahin domin dalibai da zasu yi karatu a wannan makaranta su san dukkan tsare-tsaren da aka shirya da yadda zasu yi mu’amala da wannan makaranta ba tare da samun kowace irin matsala ba. 

Wannan tambihi yana matsayin bayanai da shige – shigen da ya kamata dalibai su sani tun daga bude wannan shafin da kuma shiga cikin ajiye da yadda zasu dauki darussa da yadda zasu tabbatar da gama kowace irin darasi da kuma yadda zasu dauki jaraba har zuwa yadda zasu yi mu’amala da malamansu. 

Yaya Dalibi zai yi rijista

https://youtu.be/xuBsy4IHncQ

Dalibi yana iya yin rijisata da wannan makaranta ta hanyoyi guda biyu. 

Hanya ta farko shine mutum zai iya taba maballin da yake saman shafin daga gefen dama da alamar hoton mutum shafi zai fito da zai baka damar shigar da bayanai kamar haka. 

An kasa shafin kashi biyu akwai Login akwai Register 

Karkashin inda aka saka Register shine inda ake bukatar ka cike ramuka ne guda uku inda ake bukatar username sai email sai password. Ga yadda dalilin kowane rami da kuma yadda ake son dalibin da zai yi mu’amala da makarantar ya yi amfani da su. 

Username: ramine da yake bukatar ka saka sunan da zaka rika yin amfani da shi wurin shiga ajinka, wannan sunan dole yakasance kalma daya ake bukata. Kana iya amfani da kalmimi fiye da daya amma ba tare da bada tazara tsakanin su ba. Za a iya amfani da alamar rubutu ta ko _ ko . tsakanin kalmomin. 

Misali: salisuhassan ko salisu.hassan ko salisu-hassan ko salisu_hassan  

Kowanne tsari ka dauka yayi daidai. Amma ka sani idan wani ya dauki irin wannan sunan dole sai ka sake gwada wani har a dace.

Email: Wannan shine wurin da zaka yi amfani da imel adireshin ka wanda yake aiki kuma kake da damar shigansa domin ta wannan email din ne dukkan sakonnin wannan makaranta zai rika shigo maka. Kowane dalibi na bukatar email guda ga dukkan darussa. Sannan mallakar email wajibi ne ga kowane dalibi. 

Password: wannan rami ne da zaka rubuta wadansu kamlomi na sirri wanda sune zasu zama mukullin shigarka wannan makaranta wanda da ba a son ka bari kowa yasan abinda kake amfani da shi sai kai kadai. 

Ana son wurin kirkirar wadannan kalmomin sirrin dalibi yayi amfani da harrufa da lambobi da kuma alamomin rubutu duka a cikin kalma daya. 

Misali: salisu123! Ko Hass@n!#1  

Yin amfani da irin wannan damar zai hana kowa iya gane mene ne kalaman sirrin shigarka makaranta. Sai dai kai kanka kana bukatar samun wani kebabben wuri ka rubuta ka boye don kada ka manta kaima ka kasa shiga shafin naka. 

Hanya ta biyu 

Hanya ta biyu da ake iya yin rijista a wannan makaranta shine lokacin da mutum ya zabi wani kwas da yake son yayi kuma ya kai har wurin da zai cike bayanansa bayan ya aika da amincewar siyan wannan kwas yin hakan ya tabbatar da yin rijista da wannan makarantar. 

LOGIN DA CANZA HOTO

https://youtu.be/9uvlawIj44A

Dalibi yana da hanya guda ne ta shiga dakin bayanan sa inda zai iya yin dukkan wani abu da ya kamata dalibi yayi a cikin makaranta da yadda zai yi mu’amala da malamansa da makamantansu. 

Taba maballin da yake saman shafin daga gefen dama da alamar hoton mutum shafi zai fito da zai baka damar shigar da bayanai kamar haka. 

Bangaren da aka rubuta login shine inda zaka zuba bayanan ka domin samun shiga. 

Wurin da aka rubuta username or email nan zaka zabi kodai ka yi amfani da email dinka ko kuma username a cikin ramin. 

Ramin password zaka saka kalmomin sirrin nan da kirkira su zaka yi amfani da shi. 

Remember me idan kana son kwamfutar ta tuna da bayanan da ka yadda nan gaba idan zaka sake shiga baka bukatar ka sake shigar da su sai ka taba wannan shafin. 

Login: wannan shine maballin da zaka bata bayan ka shigar da komai domin neman izinin shiga, idan bayanan da ka saka daidai ne, shafin zai bude, idan kuma akwai kuskure  ba zai baka damar shiga ba. 

Lost your password?: Wannan hanya ce dalibi zai yi amfani da shi idan ya manta da kalmomin sirrin shiga shafinsa wanda za a aika mishi da sako cikin email dinsa da zai shiga ya bi shawarar da aka bashi domin canza wani kalmomin shiga shafin. 

TIMELINE DA GROUP DA FORUM)

SAMUN CONNECTION DA AIKA EMAIL