Categories
Daga Edita

Daga Teburin Edita – Mujalla Ta biyu

Da farko muna yi wa Allah maɗaukakin sarki da Ya nuna mana lokaci na biyu domin fitowar wannan mujalla ta mu ta Duniyar Computer, sannan muna bai wa sauran al’umma haƙuri na jinkiri mai tsawon gaske na rashin fitowar wannan mujalla kamar yadda muka faɗa a cikin manufofinmu. Mun sami matsaloli a fitowarmu ta farko […]

Mujallar Duniyar Computer fitowa ta biyu  a cikin kundi na daya
Mujallar Duniyar Computer fitowa ta biyu a cikin kundi na daya

Da farko muna yi wa Allah maɗaukakin sarki da Ya nuna mana lokaci na biyu domin fitowar wannan mujalla ta mu ta Duniyar Computer, sannan muna bai wa sauran al’umma haƙuri na jinkiri mai tsawon gaske na rashin fitowar wannan mujalla kamar yadda muka faɗa a cikin manufofinmu.
Mun sami matsaloli a fitowarmu ta farko wanda ya sanya dole muka sake yin ɗammara domin ganin In Allah Ya yarda ba za a sake samun irin wannan matsalar ba.
Mutane da dama sun yaba matuƙa da yadda aka yi wannan mujalla ta farko, amma kamar yadda muka faɗi cewar Ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, to, mun sami ƙorafe-ƙorafe daga ɗimbin masoya da kuma shawarwari na yadda za a inganta ita wannan mujalla, kuma dukkanin shawarwarinku abin karɓa ne da dubawa.
Mun yi alƙawari da kuma faɗa wa al’umma cewar fitowar nan za ta fito tare da faifai amma kuma hakan bai yiwu ba, kasancewar rashin kammaluwar ingantaccen faya-fayen da za mu saki ya ƙara taimakawa wajen tsaikon fitowar wannan mujalla.
A cikin wannan fitowa kamar yadda muka sani cewar dukkan wani ilimi yana farawa ne daga matakin farko, a wannan fitowar mun saka muku muƙaloli na ilimi wanda dukkansu babu abin yadawa, kuma kowanne sashe abin lura ne. A waccan mujalla ta farko babban muƙalar mu ita ce “Mece ce Kwamfuta” wacce muka warware ilmoma masu yawa a kan haka. A wannan fitowar mun zakuɗa gaba sosai domin mun kawo muku cikakken ilimi a kan abin da ya shafi cikin ita kwamfutar mai taken “MENE NE SYSTEM UNIT?”. Haka akwai muƙalar da take biye da ita wanda suka yi kama sai dai ita kuma ta shafi abin da ake buƙatar mutum ya sani ne idan yana son ya san yadda zai haɗa kwamfuta da kansa mai taken “KOYI YADDA AKE HAɗA KWAMFUTA DA KANKA A AIKACE”. Sannan kuma har ila yau a wannan fitowar mun koyar da “ILIMIN SANIN YADDA AKE ƊORA OPERATING SYSTEM”. Ga kuma cikakken bayanin “Banbanci Tsakanin Adobe Reader da Adobe Acrobat”, sannan daga cikin karatuka masu sha’awa akwai “Yadda za ka kashe Kwamfuta ba tare da amfani da maɓallin kashe ta ba”. Wannan da waɗansu bayanai masu yawa duka a cikin wannan mujalla ta ‘Duniyar Computer’.
Idan muka dawo ta ɓangaren ‘Duniyar Waya’ akwai muƙaloli masu ban sha’awa da ilimantarwar da ya kamata duk mai amfani da wayoyin Blackberry da Android ya kamata su sani a cikin muƙala mai taken “Abubuwa 10 da mai amfani da wayar BlackBerry ya kamata ya sansu” Sannan da muƙala mai taken “Tambayoyi 7 da mai amfani da Android ya kamata ya san amsarsu”. Haka mun warware taƙaddamar da ke tsakanin masu rikicin wayoyin Symbian da Android “Me ya sa Wayoyin Android suka fi Wayoyin Symbian?
Haka idan muka koma ta ɓangaren ‘Duniyar Waya’ mun samu rubutu masu zurfi da kuma ilimi mai gamsarwa dangane da abin da ya shafi ilimin “MENE NE NETWORKING” wannan ilimi ne da ya ƙunshi dukkan abin da mutum yake buƙata ya sani domin ganin ya ƙulla alaƙa tsakanin kwamfutoci guda biyu ko fiye. Har ila yau a cikin wannan ɓangare mun koyar da “Yadda Shafukan Internet Suke yin aiki” sannan kuma mun yi bayanin “Yadda ake amfani da Dandalin Twitter”. “Intanet A Matakin Farko” darasi ne da duk wanda yake shiga intanet ya kamata ya sani domin cikakken bayani ne game da abubuwan da ke faruwa kafin ka iya buɗe shafi a cikin Intanet. Daga ƙarshe mun yi ƙarin bayani game da “Hanyoyi guda biyar da za ka iya kare kanka daga Keyloggers”.

A sha karatu lafiya, Allah ya ƙara fahimtar da mu, amin

Salisu Hassan (Webmaster)
Babban Edita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *