Categories
Duniyar Computer

COMPUTER A MOTOCINMU: YAYA SUKE?

Rubutawa da bincike: Salisu Ibrahim

Computer na da matukar amfani a duniyarmu ta yau. A yau amfani da Computer ya wuce wurin rubuce-rubuce da lissafe-lissafe da kalle-kalle da koyar da ilmi da dai sauran ayyuka da muka fi sanin na’urar da aikatawa.
Abin da yawancin mutane ba su sani ba a yau shi ne; ana amfani da Computer a motocin da muke hawa domin zirga-zirgarmu ta yau da kullum. Kusan duk motar da ka gani a wannan zamani ta dogara ne da wani nau’i na Computer wajen gudanarwar ta. A kan yi amfani da wannan na’ura a motocin ne ta hanyoyi da yawa kamar yadda bayanin suke tafe
Na’ura mai kwakwalwa da ke aiki a jikin mota
Wadannan Computer na aiki ne domin tabbatar da aikin mota ba tare da wata matsala ba, da kuma tabbatar da tsaron matuki, da ma sauran mutanen da ke cikin motar, tare da tsare muhalli daga gurBata. Cikin irin wadannan na’urori akwai masu sarrafa inji da masu sarrafa kofofin mota da hasken wuta da makullai da masu sarrafa gudun mota da masu sarrafa Bangaren lantarkin mota da masu sarrafa aikin birki da dai sauransu.
Mafi muhimmanci cikin na’urori da ke jikin mota ita ce wacce ke sarrafa aikin injin motar. Wannan na’ura ta kunshi abin da ake kira ‘Engine Control Unit’ ko kuma ‘ECU’ a takaice, wadda yake shi ne kamar ‘Micro Processor ‘ a irin na’ura mai kwakwalwa da muka fisani. Sannan kuma akwai sauran makarrabai da ke karBo sakonni daga sassa-sassan mota wadanda su ne kamar ‘Input Devices’ a Computer da muka saba. Akwai kuma masu isarwa ko kuma aiwatar da sako wadanda su ne kamar ‘Output Devices’.

Masansana ko kuma ‘Sensors’ a Turance
Masansana su ne Bangarorin da suke karBo sako daga jikin mota domin aika wa zuwa kwakwalwar computer motar wato ‘ECU’. Misalan masansana su ne: abin da ke sansano yanayin zafin inji da abin da ke sansano yanayin iskar da ke zuwa cikin inji da abin da ke sansano yanayin taka totir (throttle pedal) da direba ke yi da abin da ke sansano yanayin zafin ruwa da ke sanyaya mota da dai sauransu. masansana su ne kamar ido da hanci ga injin mota.
motar wato ‘ECU’. Misalan masansana su ne: abin da ke sansano yanayin zafin inji da abin da ke sansano yanayin iskar da ke zuwa cikin inji da abin da ke sansano yanayin taka totir (throttle pedal) da direba ke yi da abin da ke sansano yanayin zafin ruwa da ke sanyaya mota da dai sauransu. masansana su ne kamar ido da hanci ga injin mota.
Daya daga cikin hanyoyin da za ka gano cewa wani daga cikin masansanan motarka baya aiki shi ne ta kamawar wata ja ko rawayar wuta a ‘Dashboard’ din motarka.

kwakwalwa ko ‘ECU’
‘ECU’ ne ke karBar sakonni daga masansana ya sarrafa sakonnin sannan ya aika da bayanin da ya dace ga Bangaren da ya kamata. Alal misali, idan abin da ke sansano yanayin zafin inji ya aiko da sako cewa injin mota na da wani nau’i na zafi, ‘ECU’ zai aika da sako zuwa abin da ke fesa mai cikin inji domin ya fesa yanayin man da ya dace da wannan nau’in zafin. Wani misalin kuma shi ne, idan abin da ke sansano yanayin yadda direba ya taka totir ya aiko da sako zuwa ga ‘ECU’ a kan cewa direba ya taka totir din sosai to ‘ECU’ din zai aika da sako zuwa ga abin da ke fesa mai da sauran wuraren da suka kamata domin bada mai da karfin wutar lantarki da ya kamata ga injin motar. Aikin wannan na’ura kan sanya injin mota ya yi aiki sosai ba tare da wata matsala ba.
Aikin Computer ga yadda injin mota ke aiki na da matukar muhimmanci. Tana taimaka wa sosai wajen rage shan mai a mota da kuma kare muhalli daga gurBata, ta hanyar rage yawan hayakin da mota ka iya fitarwa.
Na’ura mai kwakwalwa da ake aiki da ita don gyaran mota
Shigo da Computer cikin mota ya sanya dole ake amfani da ita na’urar wurin gyaran motar. A yanzu a kan yi amfani da Computer wurin gano matsala a mota, kai, wani lokacin ma har da a wurin gyaran motar. Kyera ita motar ko, a yanzu ba ya yiwu dole sai da injina da na’ura mai kwakwalwar ke sarrafawa.
Akwai motoci da dama a wannan zamani wadanda baya yiwuwa a gano me ke damunsu sai an yi amfani da Computer. Wannan ke nuna cewa akwai alamun kanikanci nan gaba zai gagari da yawa daga cikin kanikawanmu na yau, sai dai in har sun nemi ilmin Computer.
Ana amfani da wata na’ura da ake kira ‘OBD Machine’ wato ‘Onboard Diagnostic Machine’ wadda a kan jona a wani Bangare na mota sannan a jona ita na’urar a jikin na’ura maikwakwalwa. Ita na’urar za ta gano matsalar da ke damun mota sannan ta fito da abin da ta gano a fuska ko kuma ‘screen’ din na’ura mai kwakwalwar da aka yi amfani da ita.
Na’ura mai kwakwalwa da ake amfani da ita don ganowa da kuma sarrafa mota a kan hanya
Wani amfani kuma da za a iya yi da Computer a mota shi ne wurin sarrafa motar daga nesa, ma’ana sarrafa ita motar ba tare da mutum yana cikinta ba. Wannan fasaha kan ba wa mutum damar sanin yadda wani ke sarrafa motarsa daga wata uwa duniya. Ta yin amfani da wannan fasaha mutum zai iya gano wurin da wata mota da aka sata take in har motar na dauke da na’urar da muke magana a kai. Kuma za a iya amfani da wannan fasaha wajen kashe injin motar ko kum kulle kofofinta ko kuma kunna amsa kuwar tsaron motar. Wannan na’ura kuma kan taimaka wa mutum sanin wurin da motarsa take daga wata uwa duniya.
A kan yi amfani da wata fasaha da ake kira GPS wajen cinma wannan buri. Ana amfani da wata na’ura ne da a kan makala a jikin mota wadda ita na’urar kan aika da sako ga wata Computer wadda ita kuma kan shigar da sakon cikin yanar gizo ta inda shi kuma wanda ke son yin wani abu ga motar zai shiga yanar gizon ta yin amfanida na’urarsa mai kwakwalwa wajen cimma burinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *