Categories
YouTube

Yadda ake saukar da video daga YouTube (2) : Amfani da hanyoyi mabanbanta wurin saukar da bidiyo daga YouTube

DARASI NA FARKO

Da Me Ake Amfani A Saukar Da Bidiyon Youtube A Kwamfuta Ko Kuma Wayoyin Hannu?

Ba zamu iya ƙididdigar yawan manhajoji manya da ƙanana da ake da su ba wurin samun saukin sauke bidiyo da suke kan shafukan intanet ko kuma shafin YouTube ba. Abin lura a nan shi ne, kasancewar duk lokacin da mutum zai shiga intanet, musamman shafin google ya rubuta wata tambaya ta neman sanin yadda mutum zai yi wani abu, amsosi daruruwa ne za su bayyana wanda idan mutum ba ya saba ba ne, sai ya rude ko kuma ya kidime, ya rasa wacce ce amsa ta gaskiya.

A wannan darasi ba za mu baku sunan manhaja ko guda ba, musamman manhajoji masu zaman kansu, saboda mafi yawansu ana biyan kudi ne wurin yin amfani da su, ko kuma a fake da su a cika maka kwamfuta da wadansu kananan manhajojin bogi wadanda za su fitine ka da cewar ko akwai virus a cikin kwamfutarka ko kuma tana tabiya ba cikin hanzari ba.

Akwai shafuka a intanet masu yawa waɗanda su aikinsu shi ne, idan mutum ya ziyarce su sannan ya ga wani bidiyo a intanet ya bashi sha’awa kuma ya na son ya saukar da shi sai ya kwafo link din bidiyo, ya daura a wancan shafin su kuma sai su bashi wani link din da zai yi amfani da shi ya saukar.

To suma irin waɗannan shafuka suna da yawa, kuma suma akwai abin lura, domin wadansu suna boye kananan manhajoji domin cutar da kwamfutocin mutane ko kuma wayoyinsu. Shi yasa a wannan gabar zan dauki shafi mafi sauki da kuma hanya mafi soyuwa domin in yi wa jama’a bayanai masu sauki ta yadda za a saukar da wannan bidiyo.

Iya Kudin ka iya Shagalin ka.

Daga cikin abin da masu sauke bidiyo suka fi ala’akari da shi musamman wadanda sababbin shiga ne, shi ne mene ne nauyin bidiyon da zan sauke? Wannan haka yake, domin duk lokacin da aka turowa mutum bidiyo ta WhatsApp sai ka ji yace wa zai sauke shi saboda ai ya kai MB (Megabyte) kaza.

To, lallai ya kamata duk wanda yake son ya sauke bidiyo a YouTube ya sani cewar MB na kuka, kuma wani lokacin ma kokawar da ya ke yi mai tsawo ce. Su dai YouTube suna da tsari na kyawun bidiyo tun daga 240p (prograssive scan) har zuwa 8K (Ultra High Definition), wanda wannan yake nuna mana cewar mutum zai iya lashe tun daga MB 3 zuwa abin da ya kai gig domin kallo ko kuma saukar da bidiyo daga YouTube.

Saboda haka ya danganci ya kake son kyau na bidiyon ka, idan kana son saukar da kyakkyawan bidiyo to ka sani kana bukatar MB da yawa, kuma iya yawan mintunan da bidiyon yake da shi, iya nauyin ko girman MB da zai iya lashewa.

Amfani da hanyoyi mabanbanta wurin saukar da bidiyo daga YouTube

Duk da dai wannan hanyoyin da za mu fada ana iya amfani da su wajen saukar da kowane irin bidiyo ne mutum ya gani a intanet matukar zai iya kallonshi kai tsaye, amma zamu kebe wannan zuwa ga shafin YouTube sai dai kuma idan kana son yin amfani da shi a wani shafi sai ka yi amfani da hanyar da muka ambata.

Amfani da SaveFrom.Net Helper

Wannan wata ‘yafr karamar karin manhaja ce wacce ake karata a kowace browser wanda aka fi sani da (add-ons). Wannan ‘yar karamar manhaja tana daga cikin manhajojin saukar da bidiyo daga YouTube wanda ya fi kwanne shahara a yanzu. Ana amfani da wannan manhajar domin saukar da duk wani bidiyo da yake shafun YouTube, Facebook, Vimeo da wadansu shafuka sama da 140 ta hanyar taba maballo guda.

 1. Zaka shiga shafin ta wannan hanya (en.savefrom.net/user.php).
 2. Shafin ya bude zai baka wani babban maballi da aka rubuta (Download) sai kawai ka taba shi.
 3. Zai saukar da ita wannan manhaja kuma zai fahimci wace browser ka yi mafani da ita wurin sauke shi. Tunda mun ce wannan manhajar kari ce ga browser wato add-ons bata da girma.
 4. Da zarar ya gama saukarwa, sai ka bude wurin da ya saukar ko kuma ka taba shi ta manuniyar cewar ya gama sauka daga jikin browser dinka, yin haka zai bayyanar maka da allon tabbatar da cewar kai ne kake son ka girka (installing) wannan manhajar ta hanya laba maballin yes.
 5. Daga nan zai daura shi wannan add-ons din ta hanyar kara shi a kan kowace manhaja ta browsing, kamar Opera, FireFox, Chrome, Safari, Internet Explorer da dai duk wata browser da kake amfani da ita a cikin kwamfutar ka.
 6. Zai nemi ya kulle duk wata browser da take bude, domin ya tabbatar da cewar girkawar da ka yi ta zauna daidai, sannan ya sake bude shi.
 7. Duk bidiyon da kake son ka sauke kawai bude shi za ka yi ya fara nunawa (playing), yana farawa zaka ga wani karin maballin a gefen yawan mutanen da suka yi subscribing din page kafin yawan wadanda suka kalli biyon an rubuta download da alamar kibiya na kallon kasa sai kawai ka latsa shi.
 8. Idan kuwa an lika bidiyon ne a wani gida kamar wani ya kai shi shafin zumunta na facebook zaka ga ya kara maka wani dan karamin labule a sama yana fada maka tsarin saukar da bidiyon tun daga zari FLV, MP4 a nan ma zaka ga maballin download amma wannan karon daga sama gefe babu kuma kibiya a jikinshi sai ka taba shi, zai fito maka da irin nauyi ko kyau na bidiyon da kake son saukar sai kawai ya fara sauka.

Wadannan kyawu (quality) na bidiyon da zaka saukar zaka iya saukar da tun daga tsarin bidiyo na FLV 240p, MP4 360p, MP4 720p, MP4 480p, WebM 360p, 3GP 144p, 3GP 240p da kuma sauti mai tsarin MP4 128kbps. Wadannan sune irin tsarin bidiyo da zai saukar, kana da zabi daya daga ciki, iya yawan lamba iya girman MB da zai ci, misali mafi kankanta a cikinsu idan muka cire na sautin MP4 128kbps ne, 3GP144p shi ne mara nauyi, wanda kuma ya fi kowanne kyau da nauyi shine MP4 720p.

Amma idan mutum yana son saukar da bidiyo mai tsananin kyau wanda ake kiranshi da HD (High Definition) ko kuma sauti mai tsarin MP3 tunda shi sauti na MP4 ba kowace kwamfuta ko waya ce suke iya amfani da su ba.

Amfani da Ummy Video Downloader domin sauke HD ko MP3 daga YouTube

Ummy Video Downloader ita ma karamar manhaja ce wacce ake karata a jikin browser kamar SafeFrom.Net Helper sai dai ita tana baka damar saukar da bidiyo mai tsananin kyau High Defination da kuma sauti na MP3

 1. Zaka shiga shafin Ummy Video Downloader ta wannan hanya (ummy.com), sai ka taba maballin saukarwa (Download).
 2. Za ka jira ya gama sauka sai ka girka shi (installing) a cikin kwamfutar.
 3. Idan ka bude shafin na youtube kuma ka zakulo bidiyon da ka ke son saukarwa sai ka kwafe link din biyon ka bude manhajar Ummy Video Downloader sannan ka saka wannan link din zai baka damar saukar da dukkanin tsarin kyau na bidiyon da kake buka ciki har da High Defination da kuma MP3.
 4. Wani lokaci kuma zai baka dama ce a kasan bidiyon da ka bude a karkashen SaveFrom.Net Helper sai ka zabi HD ko MP3.

Amfani da SSYOUTUBE.COM

 Wannan hanya tana daya daga cikin hanyoyin saukar da bidiyo a shafin YouTube da kuma sauran gidajen da ake ajiyar bidiyo a intanet. Ita wannan hanyar bata bukatar sauke kowace irin manhaja, kuma bata bukatar yin wani abu mai rikitarwa. Sai dai sharadi na farko shi ne:

 1. Ba za ka yi amfani da sananniyar manhajar bude YouTube ba misali idan kan amfani da wayar hannu kuma ka saukar da manhajar YouTube to ba zaka yi amfani da ita ba, za ka bude browser ce ka shiga YouTube kai tsaye.
 2. Ka bude bidiyon da kake son ka sauke.
 3. Daga saman inda ya ke nuna adireshin inda bidiyon yake sai ka share daga https://www. sai ka kara SS a wurin sai ka dannan maballin GO ko kuma Enter a jikin Keyboard dinka. Misali https://www.youtube.com/watch?v=M4w2uQVpTGM, sai ka mayar da shi ssyoutube.com/watch?v=M4w2uQVpTGM
 4. Da zarar ka yi haka wannan shafin zai fita daga shafin YouTube zai wuce kai tsaye zuwa SSYOUTBE.COM in da zaka ga shafin ya canza zuwa SafeFrom.Net nan take zai bayyanar maka da wannan bidiyo ya kuma baka damar saukar da kowane irin kalan bidiyo kake son saukarwa.

 Saukar da bidiyo daga kowane irin website

Idan ka ga wani bidiyo a wani website kuma kana son saukar da shi zaka iya amfani da wannan tsarin wurin saukar da shi wannan bidiyon da ma wadanda suke cikin wannan website ba tare da samun wata matsala ba.

 1. Ka bude shafin da akwai bidiyo a ciki
 2. Ba tare da ka sa ya fara nunawa ba, sai ka kara sfrom.net/ ko savefrom.net/ wannan ya sha banban da na ss domin na ss shi share http://www. a ke yi amma wannan shi kara shi ake yi a farkon http:// misali http://www.duniyarcomuter.com sai ya koma sfrom.net/http://www.duniyarcomputer.com ko kuma savefrom.net/http://www.duniyarcomputer.com
 3. Wannan zai bayyanar da dukkanin bidiyon da suke cikin wannan website din a shafin savefrom.net tare ba ka maballin saukar da bidiyon ba tare da ka sami wata matsala ba.

Saukar da bidiyo kai tsaye ta savefrom.net

Wannan shi ne hanya ta karshe da zamu nuna muku a cikin wannan darasi na yadda ake saukar da bidiyo daga YouTube ba tare da wata manhaja ba.

 1. Zaka bude sharin savefrom.net ta hanyar bude shi ta browser dinka ka rubuta http://www.savefrom.net
 2. Sai ka sake bude shafin ka na YouTube a wani falle na daban ko wata browser inda kana da sama da daya a cikin kwamfutarka ko kuma wayar ka, sai ka bude bidiyon da kake son saukarwa.
 3. Daga saman browser dinka, wurin address bar sai ka kwafe link din da bidiyon yake.
 4. Ka dawo wancan shafin da ka fara budewa na savefrom.net ka saka a cikin ramin da ake zuba link din sai ka danna maballin download.
 5. Nan take zai dauko maka bidiyon da yake cikin wancan shafin na YouTube, tare da kala-kalan nauyi da kyau da kake son saukarwa.

Wannan shi ne karshen darasin  da muka yi alkawari zamu kawo muku wanda ya shafi yadda ake saukar da bidiyo daga YouTube, sannan wannan hanyoyi musamman hanya ta uku da hudu duk ana iya amfani da su a kwamfuta da kuma wayoyin komai da ruwanka. Kodayake a wani lokaci nan gaba kadan zamu lissafo muku wadansu manhajoji da ake amfani da su a saukar da bidiyo ta wayoyin hannu.

Muna fata za ayi amfani da wannan ilimi wurin saukar da abin da ya dace ba abubuwan da bai dace ba. Allah ka shaida mun kubuta daga duk wanda ya ya saukar da abin da ka haramta a kalla.

Categories
Duniyar Internet YouTube

Yadda ake saukar da video daga YouTube (1)

Wannan darasin sabo da tsawon shi mun raba shi gida biyu

Matashiya

Kafin mu yi bayanin hanyoyi da ake bi domin a saukar da bidiyo daga dandalin zumunta na YouTube, ya na da kyau mu fahimci wadansu ka’idoji da dokokin saukar da abu daga shi wannan zaure na YouTube.

Su dai wannan kamfani na YouTube mallakar babban ma’aikatar nan na Google ne, a hanlin da muke ciki a yanzu babu wani daki ko shafi a duniyan nan da ya ajiye hotuna masu motsi kamar YouTube, haka kuma shi ne shafi wanda aka fi ziyarta domin kallon hotuna masu mosti, kuma shi ne shafi na uku a ziyarta a duk shafukan da suke intanet.

Domin an ƙiyasta sama da mutane biliyan daya (1 billion) suke amfani da wannan shafi na YouTube haka kuma a shekarar 2014 kamfanin ya sami ribar kudi zunzurutun dalar Amurka biliyon 4 (4 Billion USD), haka kuma kamar yadda kamfanin dubawa da yin hasashe na DMR (Digital Marketing Statistics) su ka fadi cewar a kullum ana kallon bidiyo biliyan 4 a kowace rana.

A wuraren Satumbar 2011, kamfanin yayi wani alkawari da har yau bai cika ba, na cewar za su saki wata manhaja wacce zata ba mutane masu amfani da wayar komai da ruwanka damar kallon bidiyo a YouTube ba tare da amfani da fasahar intanet ba, matuƙar ka bude shi bidiyon kafin ka kashe intanet din. Wannan yunƙuri na su, har yanzu bai tabbata ba.

Amma kuma idan ka dubi mafi yawancin bidiyon da yake cikin kwamfutocin mutane da wayoyinsu za ka samu cewar ana samun su ne daga YouTube. To, haka abin yake, domin kusan kafin a fara samun makarantu masu zaman kansu a intanet, mutane da dama suna daura karatukansu a shafin YouTube domin jama’a su kalle su. Shi yasa YouTube ya zama wani dausayin alheri da kuma tsibiri na sharri. Domin kusan dukkanin wani ilimi da mutum yake son ya koya zai yi wahala a shiga cikin shafin YouTube bai same shi ba. Wani lokaci ma shi wannan shafin manyan gidajen jaridu da gidajen yada labarai na talabijin suna amfani da shi wurin daura shirye-shirye domin jama’a su yi amfani da shi ko kuma su sake kallonsa.

Shi yasa kowane irin bidiyo ake samun shi a YouTube, kama tun daga na karatu, wasanni, nishadi, fadakarwa da dai makamantansu, kuma dukkaninsu ana samun masu tsawo da matsakaita. A wani lokaci zaka samu mutum daya ya daura bidiyo sama da dubu biyu a shafinsa, kuma ka samu yana da mabiya ko masu kallo sama da miliyoyin adadi.

Takaitaccen tarihin kafa YouTube

YouTube na daya daga cikin shafu a Intanet irin wadanda ake kiran su da video-sharing website, wato shafukan da ake saka bidiyo domin wadansu su kalla, ya na da Hedkwata a San Bruno da Jihar California ta kasar Amurka. Wadansu matasa su uku Steve Chen, Chad Hurley da kuma Jawed Karim su ne suka kiriro shafin a 14 ga watan Fabrairu 2005 bayan da suka bar aiki a wani kamfanin hada-hadar kudi a intanet mai suna PayPal. Tun daga shekarar 2005 zuwa 2006 su ne suke da alhakin mallakar komai a shafin YouTube har zuwa lokacin da kamfanin Google ya ga muhimmancin wannan shafi da yadda ya sami karbuwa a wurin mutane, ya siye shi da kudi wuri na gugar wuri har dalar Amurka Bilyan 1 da Miliyan 650 ($1.65 billion) a watan Satumba 2006.

 Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim
Daga dama: Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim

Shafin wanda yake ba mutane damar su daura bidiyo domin mutane su kalla ko domin su yada shi a shafukan intanet ko kuma lika shi a shafukan zumunta. Ana amfani da zarin abin kallo na kwamfuta da wayoyin domin iya kallon su, kamar tsarin WebM da H.264 da MPEG-4 da AVC da kuma Adobe Flash Player.

Ana samu bidiyo daban-daban kamar na wasanni, shirye-shiryen gidajen yada labarai, bidiyon wakoki, fina-finai, karatuka, bidiyo domin ilmantar da dai makamantansu.

Mafi yawancin bidiyon da suke YouTube gama garin mutane ne suka daura shi, amma kuma ana samun gidanjen yada labarai manya sanannu suna amfani da shi, kamar irin su CBS, BBC da VOA da dai makamantansu.

Wanda bai yi rigista da YouTube ba zai iya kallo ne kawai, amma wanda yayi rijista zai iya kallo, zai iya daura shima na shi bidiyon domin wadansu su kalla, zai iya kulla alaka da wani mai daki a YouTube duk lokacin da ya daura wani sabon bidiyo a sanar da shi kai tsaye (Subcribe), sannan zai iya yin tsokaci (comment) ga bidiyon da aka bayar da damar yin tsokaci a kai.

Dukkan bidiyon da yake YouTube babu matsala wurin kallonsa matukar bai dauki hotuna na tsaraici ko na wanda yake dauke da hotuna masu hatsari, kamar kisa ko kuma abin da bai kamata masu karamin kwakwalsu kalla ba. To irin wadannan bidiyo dole sai ka fadawa YouTube cewar kai ka wuce shekaru 18 kafin ka ga irin wadannan bidiyoyin.

Shafin na YouTube yana samun kudaden shigar shi ta hanyar saka talla da yake yi a kan bidiyo da mutane su kallo, kuma sun ba masu bidiyon damar mallakar kashi 55% na kudin da ake biyansu. Misali a shekarar 2013 kamfanonin da suke ba YouTube talla su na biyan su dalar Amurka $6.60, idan aka kalli bidiyo ko kuma tallansu har sau 1000, wanda yake nuna cewar duk wanda ya amince da YouTube su saka talla a kan bidiyon da ya daura a shafinsu zai iya samun 0.5x$7.60×55%=N2.09 wannan tsarin an yi amfani da shi a shekarar 2013.

Shafin na YouTube yana iya kokarin ya ga ya hana mutane daura bidiyon da baka da hakkin mallaka, wato irin na satan safage wanda kusan da yawa daga cikin bidiyoyin da suke YouTube wadanda suka daura shi ba su suke da hakkin mallakar shi ba.

Shin daidai ne mutum ya saukar da Video a YouTube?

Babu laifi idan mutum ya saukar da bidiyo daga YouTube domin yayi amfani don karan-kansa ba tare da juyashi ba ko kuma ya canza shi zuwa wata hanya. Amma laifi shi mutum ya saukar da kowane irin bidiyo a YouTube sannan ya yi amfani da shi a wani gidan talabijin ko kuma ya gurza shi ko kuma domin sayarwa.

Kamar yadda kamfanin na google ya fadi a shafin shi na sharadin amfani da bidiyon YouTube sun rubuta kamar haka, “Ba a yarda kayi amfani da Video nan ba sai domin amfanin kanka, ba na neman kudi bane, ba za a diba ba (copy), ba sake gurzashi, ba rabashi, ba nuna shi a gidajen talabijin, ba yin kasuwanci da shi, kada ayi amfani da wani bangare nashi sai da izini rubutacce zuwa ga YouTube”. Daga jin irin wannan sharadi yake nuna mana cewar idan mutum zai saukar da bidiyo daga YouTube kuma yana son yayi amfani domin nishadantar da kansa ko kuma ilmantan da kansa, to babu laifi.

Haka idan muka dubi zuwa ga amfani da shi ta wadansu kafafe, sai muga hatta yadda mutanen mu suke saukar da bidiyo daga wannan gida kuma suyi ta gurzashi, wannan kai tsaye laifi ne. Shi ya sanya daga cikin dokokin amfani da shi, sun fadi cewar idan mutum ba zai yi amfani da intanet ba ne, ya kalla kai tsaye, to shima ba su yarda ya saukar da shi ba domin kallo.

Saukar da bidiyo daga YouTube yana kawo wa wannan kamfani cikas ga harkokin kasuwancin su. Mutane da dama su na yawan tambayar mu shin, irin waɗannan shafuka kamar google, ko facebook, ko YouTube mene ne ribarsu? Sai mu fada musu cewar shigar da muke yi suna amfani da shafukan su, shi ne ribar su, domin manyan kamfanoni na duniya suna yin la’akari da yawan mutanen da suke shiga dakuna a intanet, kuma wannan dalilin yake sanyawa a basu talla.

Mene ne dalilin da yasa ba maballin saukar da bidiyo kai tsaye a shafin YouTube?

Kamar yadda muka fadi cewar a shekarar 2014 kamfanin google ya sami ribar dalar Amurka biliyan 4 wanda yake daidai da Naira Biliyan Dari Tara (900,000,000,000) ta su bidiyoyin da ake kallo a shafin YouTube. Wannan ribar ta samu ne saboda talla da yake bayyana a jikin bidiyo lokacin da mutum yake kallo.

Wannan shi ne ma dalilin da ya sanya wani lokaci idan mutum yana son kallo a YouTube sai ya jira na ‘yan dakikoki biya domin kallon talla kafin ya baka zaɓin ko ka ci gaba da kallo ko kuma ka wuce zuwa ga shi bidiyon da ka nemi ka kalle shi. Matsalar nan ita ce, idan mutane suka sauke shi bidiyon kun ga babu yadda za ayi kamfanin su sami kudi, dalilin haka ya sanya su kamfanin basa so mutum ya ce zai saukar da shi.

Ko ba mu yi dogon bayani ba, kasan cewar da dukkanin bidiyoyin da suke cikin wayoyinmu za a barsu a shafukan da suke sai dai kawai mukalla a sama da kudaden da za su samu sai ya ninka wanda suka samu a shekarar 2014. Amma dai duk da haka mutane da yawa suna ta ƙoƙarin su ga yadda za ayi su saukar da wadannan bidiyoyi a kwamfutocinsu da wayoyin domin su iya amfana da su a wani lokaci.

Mene ne ya sa bidiyo yake da cin MB?

Dalili kuwa shi ne domin bidiyo hotuna ne aka tara su a wuri guda. Yadda abin ya ke shi ne, duk wani bidiyo da mutum ya gani tun daga dakika daya zuwa awanni daga hoto daya ne zuwa hotuna 25 zuwa hotuna 60. Idan ka duba na’urar daukan hoto misali Camera ta wayarka, zaka ga daga bayan an rubuta lamba a gaban lambar an rubata Pixel, misali 2 Mega Pixel. Wannan megapixel sinadari ne da ake auna kyau da girman da Kamara zata iya daukar hoto da shi.

Idan aka ce kamarar wayar ka ta na da 5-megapixel to ana son ka sani cewar wayar ka zata iya daukan hoto guda wanda sai an sami digo miliyan biyar a jikinshi. Shi daman Pixel a ilimin daukan hoto na nufin digo duga ko kuma rami guda da kala zai iya zama na hoto a cikinsa. Saboda haka, idan aka ce wayar mutum ko kuma kamarar shi tana daukar hoto mara motsi guda daya wanda ya kai nauyin 2Mb, to idan zata dauki bidiyon dakika guda sai ka hada 2mb x 25 = 120mb.

A takaice duk mafi yawan bidiyon da muke kallo suna da zubu iri biyu ne, PAL da NTSC, bidiyon da aka daukeshi da fasahar PAL a kwane dakika ana samun hotuna 25 ne, wanda kuma aka yi amfani da fasahar NTSC ana samun hotuna 29 zuwa 30 a kowane dakika guda. Ba a maganar cewar lokacin da kamarar take daukan hotunan tana kuna hadawa tare da sauti wanda shima yana da nasa nauyi.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya bidiyo ya ke nauyi kasancewar tarin hotuna ne da sauti a hade a wuri guda.

KARANTA DARASI NA GABA

Categories
YouTube

YAYA ZA A YI IN YI AMFANI DA YOUTUBE A WAYAR HANNU

Rubutawa: Dahiru Saleh

A wannan ɗan takaitaccen rubutun zan yi magana a kan abin da mutane da yawa suke yin tambaya a dandalin muna facebook da kuma wuraren karatun a kan matsalar da suke fuskanta idan suna son su kalli wani video a youtube ko kuma dai su kalli video a internet da wayar tafi da gidanka.

Wanann kuwa tana daga cikin matsalolin da mu kanmu a Duniyar Computer muka fuskanta da mutane da yawa suna son kallon videon da muke yi wanda suke warware matsaloli daban-daban game da abin da ya shafi computer da waya baki ɗaya.

To, shi dai kallan video da waya musamman a dandalin youtube abu ne mai wahala idan aka yi la’akari da yana yin tsarin da su youtube suke da shi na yadda ake kallon video a gindan. Suna da tsari guda biyu wanda kuma yake goye a kan tsari guda.

Youtube sun ta’allaƙa videon na su a kan za a iya kallonshi a computer ga wanda yake amfani da browser ta zamani wacce kuma take da player ta adobe flash wanda duk wanda ba shi da wannan abubuwa guda biyu to, ba zai yiwu ba ya iya kallon video a youtube.

Sai hanya ta biyu ita ce sabon tsarin da su youtube suke fito da shi a sakamakon sabuwar fasaha ta HTM5 wanda yake iya baka damar ka kalli video da aka saka a internet ba tare da adobe flash player ba. Duk wanda ya saka video ɗin shi a youtube kuma ya zaɓi tsarin cewar HTML5, to dole sai browser ta zamani wacce kuma take da alaƙa da HTML5 zata iya duɗe wannan videon har kuma a iya kallon sa.

Hanya ta ƙarshe kuwa ita ce wadda tsarin da kamfanin youtube suke da shi ga waɗanda suke son su kalli video amma da wayar hannu, wanda shi ba kowane video ba ne, sai video da aka saka shi da tsarin .3gp wanda daman shi shi ne tsarin da waya take iya buɗewa.

Masu amfani da iPohne da android:

Idan ba wai kana da waya ta zamani ba ce kamar wayar da ke da fasaha ta IPhone ko android to suna da zaɓi ɗaya kacal da za su bi domin kallon video a youtube amma shi ma wannan video sai waɗanda muka ce an saka su ne da tsarin .3gp.

Amma masu tsari wayoyin da suke da fasahar zamanin na IPhone ko android su suna iya kallon kowa ne irin video a youtube ta hanyar amfani da application da kamfanin YouTube suka yi domin masu irin waɗannan wayoyin. Da farko dai idan kana son ka ji daɗin kallon video a internet dole sai idan kamfanin la yinka suka bada goyon bayan tsarin 3G, wanda shi ne kawai hanyar da kamfanonin layukan waya za su iya badawa domin kallon video domin kallo da sauri. Shi karan kan shi application din da youtube suka kirkiro suna buƙatar aƙalla kana da damar shiga internet ta ɗayan hanyoyi guda biyu, ko dai 3G ko kuma Wi-Fi.

Masu amfani da Nokia da Sony Ericsson da  windows da makamantansu kuwa:

Idan kuwa kana buƙatar ka kalli video a youtube da ɗaya daga cikin waɗannan wayoyin da muka ambata a sama, to ka biyo wannan matakai.

Ka shiga website ɗin youtube da wannan adireshi http://m.youtube.com/app da wayarka.

Bayan ka shiga zai fito maka da application ɗin da wayarka take dubaka domin ka iya kallon video a youtube, bayan ya bayyana sai ka sauke shi (downloading)

Sai ka yi Installing shi wannan application a cikin wayarka.

Idan ka samu damar yin haka to, video daga youtube zai riƙa kalluwa a wayarka.

A wasu lokuta sai ka ɗan daidaita tsarin shigarka internet idan ka sami matsala da buɗewar video ɗin.

Java Midlet

Ga waɗansu wayoyin Nokia da Sony Ericsson za ka iya amfani da Java Midlet wajen iya kallon video daga youtube.

Waɗansu fa’idoji

Idan har za ka iya kallon video a youtube ta wayarka, to, za ka iya:

Ɗaura video kai tsaye kai ma zuwa ga youtube. Ma’ana kai ma za ka iya daura video ta wayarka zuwa youtube website domin mutane su kalla.

Videon da kake kallo za ka iya watsa shi ga sauran mutane su ma su kalla.

Za ka iya recording na dvd ka watsa shi.