Categories
Teburin Edita

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/

A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019 ne aka kaddamar da littafin Malam Salisu Hassan wanda aka fi sani da “Webmaster” a garin Kaduna. Malam Salisu Hassan dai Malami ne mai karantar da ilimin kwamfuta a shahararriyar makarantarsa da ke unguwar Sanusi mai suna: “Duniyar Computer”, kuma mawallafin mujallar “Duniyar Computer” dai har wa yau.  Wannan littafi nashi, duk da cewa akwai wasu littattafai da aka rubuta a baya kan kwamfuta cikin harshen Hausa, sai dai, a hukumance, ba a samu irin wannan ba. Hakan ya faru ne saboda dalilai da dama.  Na farko dai shi ne littafi mafi girma da aka taba wallafawa a wannan fanni.  Shi ne littafi mai dauke da lambar jerin littattafan da aka rubuta a kasar nan, wato: ISBN.  Kuma littafi ne da ya kandamo abubuwa masu muhimmanci kan ilimin kwamfuta da hakikanin abubuwan da ta kunsa.

Littafin, wanda aka yi wa suna da: “Kwamfuta – Ilimin da Kowa Ke Bukata”, mai shafuka 353, yana dauke ne da babuka 11, a karshensa kuma aka bibiyi babukan da jerin kalmomin kwamfuta guda 500 tare da ma’anoninsu. Ina daga cikin wadanda suka yi bitar wannan littafi makonni uku kafin kaddamar da shi.  Don haka na ga dacewar rairayo muhimman abubuwan da littafin ya kunsa, don fa’idar masu karatun wannan shafi.  Hakika kaddamar da wannan littafi ba karamin ci gaba bane ga al’ummar Hausa a wannan zamani.  Ko ba komai dai, zai kara fadada fahimtar al’ummar Hausawan wannan zamani kan fasahar sadarwa na zamani; domin kwamfuta ita ce asalin dukkan wani ci gaba da ake samu a wannan fanni a duniya yanzu.

Malam Salisu ya kasa littafin ne zuwa bangare uku, duk da cewa bai bayyana hakan ba a zahiri ko a rubuce.  Bangaren farko ya kunshi Mukaddima ne. Wannan shi ne babi na daya, kuma mawallafin littafin bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayanin ma’anar kwamfuta, da nau’ukan bayanan da take mu’amala da su, irin su “data” da “information”.  Wadannan su ne nau’ukan bayanan da kwamfuta ke mu’amala da su.  Ko dai ya zama bayanai ne da ake shigar mata, take sarrafawa don bayar da ma’ana; wannan shi ake kira “data”.  Sai kuma nau’ukan bayanai sarrafaffu, wadanda duk mai karatu zai iya gane me suke nufi kuma ya fitar da hukunci daga abin da suka kunsa.  Wadannan su ake kira “information”.  Daga nan ya yi bayani kan irin ayyukan da kwamfuta ke iya gudanarwa.  A karshen babin ya kawo tarihin kwamfuta a takaice.  A Babi na biyu kuma mawallafin ya yi bayani kan karkasuwan kwamfuta ne ta amfani da ma’aunai daban-daban – tun daga farkon kwamfutar da aka fara kerawa zuwa zamanin da muke ciki yanzu.

Bangare na biyu na daukene da babuka guda shida (babi na uku zuwa babi na takawas).  Wannan bangaren ne ya yi bayani filla-filla kan gangar-jikin kwamfuta, wato: “Hardware” Kenan.  A Babi na uku mawallafin ya yi bayani kan ma’anar kalmar “Hardware”, da bangarorinta irin su na’urorin shigar da bayanai, da na fitarwa, da na aiwatar da sadarwa, da ma’adana, da bangaren sauti da na wutar lantarki duka.  Bayan wannan gabatarwa kan gangar-jikin kwamfuta a Babi na uku, sai mawallafin ya bibiyi babi na hudu zuwa na takwas da bayani filla-filla kan wadancan bangarori da ya fara bayaninsu a babi na uku.  Misali, a Babi na hudu ya yi bayani kan bangarorin shigar da bayanai ne ga kwamfuta, wato: “Input Debices”. Wannan ya hada da allon shigar da bayanai (Keyboard), da beran kwamfuta (Mouse), da na’urar daukan hoton bayanai (Scanner), sai kuma na’urorin shigar da sauti ko murya.  A Babi na biyar kuma marubucin ya fayyace bayani kan bangarorin fitar da bayanai daga kwamfuta, wato: “Output Debices”. Na’urorin sun hada da talabijin kwamfuta (Monitor), da na’urar haskaka bayanai (Projector), da lasafika, da na’urar dab’i, da dukkan nau’ukan wadannan na’urori.

Don fahimtar da mai karatu tsari da hanyoyin sadarwa tsakanin kwamfuta da sauran na’urori da kayayyakin sadarwa, marubucin ya kulla taken Babi na Bakwai da suna: “Communication Debices”.  A nan ne mai karatu zai ga ma’ana da nau’ukan hanyoyin sadarwa da kwamfuta ke dauke da su, tare da tsarin musayar bayanai tsakanin kwamfuta da sauran kayayyakin sadarwa na zamani. A wannan babi ne har wa yau mai littafin ya yi bayanin matakan tsarin sadarwa a kwamfuta da suka hada da: shigar da bayanai da sarrafa bayanai, da fitar da bayanai, sai kuma adana bayanai. Wadannan su ne asalin ayyukan kwamfuta, kuma wadannan matakai take amfani da mu’amala da sauran kayayyaki da na’urorin sadarwa a babin sadarwa.  Daga cikin abubuwa muhimmai da marubucin ya tabo a wannan babi akwai hanyoyin sadarwa na zamani, irin su fasahar Imel, da fasahar Intanet da hanyoyin aikawa da sauti ko amo ta hanyar igiyar wayar sadarwa (Wired Connection) da ta wayar-iska (Wireless). Wadannan bayanai duk Malam Salisu ya yi su ne ta la’akari da na’urar sadarwa ta zahiri.

A Babi na Takwas wanda shi ne babi na karshe a kashi na biyu na littafin, mawallafin ya kawo bayani ne kan mahadar sadarwa, wato: “Ports,” kamar yadda ya ambaci taken babin a farko.  Fahimtar wannan babi na bukatar misalai sosai.  “Port” mahada ce da kwamfuta ke amfani da ita wajen karbar bayanai rubutattu ko na sauti ko bidiyo. Duk da cewa su ma bangarorin kwamfuta ne na zahiri, amma suna da lambobi da babbar manhajar kwamfuta ke amfani da su wajen karba ko mika bayanai ga mai amfani da kwamfuta. Misali, idan kana son hawa Intanet, kwamfutarka na amfani da dayar hanyoyi biyu ne na zahiri; ko dai ta amfani da igiyar wayar sadarwa ko ta amfani da tsarin sadarwa na wayar-iska. Da wadannan mahadai ne take isar da bukatarta ga kwamfutar da ke dauke da bayanan da kake bukata a wata jiha daban.  Da zarar sakon ya iso, babbar manhajar kwamfutarka kan yi amfani da lambar mahadar sadarwa ta 80 (Port 80), wadda ita ce mahadar da manhajar ka’idar sadarwar Intanet mai suna: “Hypertedt Transfer Protocol – http” ke amfani da ita wajen karba da aika bayanai a tsarin sadarwa ta Intanet.  Idan bangaren fasahar Imel ne, akwai ka’idar sadarwa ta Imel mai suna “POP3” ko “SMTP” da ke karbar sakonni ta mahada mai lamba ta 110 ko 25, misali. Wadannan lambobi suna da alaka da waccan mahadar sadarwa, wadda mai karatu na iya ganin ramukanta a jikin akwatin kwamfuta in ta tebur ce (Desktop), ko a gefenta (in nau’in Laptop ce). Kyakkyawan karatun wannan babi zai ilimantar da mai karatu matuka kan falsafar sadarwa ta kwamfuta.

A bangaren karshen littafi, kamar yadda na lura, marubucin ya gina babi guda uku ne, wadanda suka kunshi bayanai kan ruhin kwamfuta, wato manhaja ko masarrafar da take rayuwa a kansu ke nan. Dama manyan bangarorin kwamfuta guda biyu ne; bangaren farko shi ne gangar-jikin da muke gani kuma muke iya tabawa.  Bangare na biyu kuma shi ne ruhinta, wato bangaren da dan Adam ba ya iya tabawa sai dai ya gan shi a aikace.  Idan babu wannan bangare, kwamfuta ta zama kango ke nan.

Babi na Tara shi ne ke kunshe da mukaddima kan ma’ana da hakikanin manhajar kwamfuta, wadda marubucin ya kira da suna: “Software,” kamar yadda ya ayyana sauran taken babi-babin da suka gabace shi. A wannan babi har wa yau, ya yi bayani kan tasirin wannan bangare na kwamfuta, tare da bambance tsakanin manyan nau’ukan manhajar kwamfuta; “System Software,” da kuma “Application Software” don samun kyakkyawar fahimta ga mai karatu.  Ya kuma karashe ragowar babin ne da bayani kan ma’ana da nau’ukan “System Software,”,wato: “Utility Software” da “Operating System” da kuma “Debice Driber”.  A Babi na Goma kuma ya ci gaba da bayani kan daya nau’in manhajar kwamfuta, wato: “Application Software”. Wannan shi ne nau’in manhajar kwamfuta da galibin jama’a suke amfani da ita a kwamfutoci ko wayoyinsu na salula ko wasu kayayyakin sadarwa na zamani. Sai babi na karshe, wato Babi na Goma Sha Daya, wanda ya kunshi bayani kan fasahar Intanet: ma’ana da asali da tarihi da kuma fa’idojin da fasahar Intanet ke dauke da su.  Wannan shi ne babin karshe da ke littafin.

Tsokaci da ta’aliki

Wannan littafi ne mai girman gaske wanda marubucinsa bai yi kasa a gwiwa ba wajen taskance muhimman bangarorin ilimin da suka shafi kwamfuta musamman a wannan zamani da muke ciki.  Malamin ya yi amfani da salo uku ne muhimmai wajen karantar da mai karatu. Salo na farko shi ne tsarin fayyace ma’anar kalma ko wata na’ura da yake bayani a kanta. Wannan a bayyane yake ga duk wanda ya karanta wannan littafi. Salo na biyu shi ne amfani da misalai, wajen bayanin wani tsari na gudanuwa ko samuwa ko sarrafa wani yanayi na sadarwa.  Su ma ire-iren wadannan misalai a warwatse suke cikin littafin birjik.  Sai salo na uku wanda ya kunshi amfani da tarihi wajen fahimtar da mai karatu asali da samuwar wata fasaha ko na’ura.

Don tabbatar da kyakkyawar fahimta a kwakwalwar mai karatu, mawallafin ya sanya hotuna na na’urori ko kayayyakin fasahar da yake bayani a kai, a dukkan inda bukatar haka ta taso. Sannan ya yi amfani da jadawali (table) mai tsawo wajen kawo kalmomi 500 na Ingilshi masu alaka da ilimin kwamfuta tare da bayanin ma’anarsu.

Dangane da tsarin rubutu kuwa, Malam Salisu ya zuba harshen Ingilishi sosai a cikin littafin. A tunanina, dalilin hakan ba ya rasa alaka da abubuwa biyu: Na farko shi ne asalin wannan ilimi daga harshen Ingilishi ne. Don haka, rubuta littafi kan ilimin kwamfuta a harshen Hausa ba zai taba yiwuwa ba sai da tsofa kalmomin Ingilishi, tunda shi ne asali. Na biyu kuma, saboda da yawa cikin wadanda suke da ilimin kwamfuta cikin Hausawa a yau, za ka samu kashi 90 cikin 100 na kalmomin da suka san bangarorin kwamfuta da su duk cikin harshen Ingilishi ne.  Don haka, kusan dukkan babi-babin littafin an rubuta su ne cikin harshen Ingilishi ba da Hausa ba.

Ta bangaren ma’anonin kalmomi kuma, marubucin bai rike wani tsari guda wanda ya tabbata a kai ba. Da farko dai, galibin kalmomin da ya fassara bai ba su suna tilo ko murakkabi ba.  Galibi ya kan yi bayanin ma’anar kalmar ce, sannan ya kawo misali don mai karatu ya fahimci ma’anar.  Misali, a shafi na 75 inda mawallafin ke bayani kan ma’anar “CPU,” ya yi amfani da kalmomi sama da daya ko biyu tsakanin Hausa da Ingilishi, don fahimtar da mai karatu ma’anar wannan kalma cikin sauki.  Ga yadda ya sa abin nan:

CPU ko kuma a kira shi da Processor wani lokaci ma shi ake kira da ƙwaƙwalwar kwamfuta… shi ke kasancewa mai fashin baki da fassara ga duk abin da yake faruwa a cikin kwamfuta. Iyakar abin da za a iya maka misali shi ne mutumin da ya je ƙasar da ba sa jin harshensa kuma shi ba ya jin harshensu dole yana buƙatar  tafinta wannan tafinta shi ke jin harshensa kuma yana jin harshensu.

A wasu wuraren kuma yakan yi amfani da kalmar Ingilishi kai -tsaye ba tare da kawo ma’anarta ga mai karatu ba, musamman idan a baya ya ambaci kalmar.  A wasu lokuta kuma yakan yi haka tun kafin ya ambaci kalmar a wani wuri da ya gabata. Kyakkyawar misali na shafi na 94 a Babi na 4 (Input Debices), inda yake bayani kan ma’anar kalmomin “Input” da kuma “Debice,”  yana cewa:

Input na nufin shigar da data ko program ko umarni ta hanyar da ɗan Adam zai iya umartar kwamfuta da shi. Debice kuma na nufin kayan lantarki…

A baya ya kawo ma’anar “data” a Babi na 1, amma da ya zo Babi na 4 sai ya sake ambatar kalmar cikin harshen Ingilishi, maimakon harshen Hausa kamar yadda wadansu za su zata.  A daya bangaren kuma, ya ambaci kalmar “program” a Turance a nan, wanda bai riga ya ambaci kalmar a ko’ina ba kafin wannan wuri. Wannan salo ne da marubucin ya dauka saboda wasu dalilai.

Shawarwari

Bayan nazari da bita kan littafin “Kwamfuta” har sau uku da na yi, daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen kara inganta littafin shi ne, rage yawan kalmomin Ingilishi ta hanyar fassara su cikin gajerun jimloli. Wannan zai kara fahimtar da mai karatu cikin sauki.  Ta bangaren jimlolin littafin kuma, zai dace a rage tsayinsu. Saboda gajerun jimloli sun fi saurin isar da ma’ana, musamman ga littafin da ke kokarin isar da wani sabon ilimi irin wannan, wanda rubuce-rubuce ba su yadu a fannin ba, cikin harshen Hausa. Haka nan, zai dace idan aka ba da ma’anar kalma a farko cikin wani babi a harshen Hausa, to, idan aka zo ambaton kalmar a wani wuri a ambace ta cikin ma’anar da aka ba ta a harshen Hausa; in ya so sai a sanya asalin kalmar Ingilishin a cikin baka biyu, misali: “Beran kwamfuta” (Mouse).  Ko “Allon Shigar da Bayanai” (Keyboard). Hakan zai kara tunatar da mai karatu asalin kalmar da aka ciro kalmar Hausar.  Bayan haka, zai dace a yi bitar ma’anar wasu kalmomi. Misali a shafi na 231, mawallafin ya fassara kalmar “Internet” da “Web” da ma’anar “Yanar Gizo,” maimakon “Yanar Sadarwa,” wadda ita ce ta fi isar da ma’ana mai inganci. Haka kalmar “Script” a fannin gina manhajar kwamfuta, an fassara ta da: “Surkullen Yaren kwamfuta”.  Wannan ba zai bai wa mai karatu kyakkyawar fahimta kan sakon da kalmar ke isarwa ba. “Script” nau’i ne na yaren gina manhaja ko shafukan Intanet. Sannan kalmar “surkulle” tana ishara ce ga wani abin da ba ya da hakika; kamar rufa-ido ne. Wannan ya saba wa ilimin gina manhajar kwamfuta, wanda hakika ne shi, ba surkulle ba. Ba dukkan mai karatu zai fahimci asalin ma’anar ba. Ina ganin bitar ma’anar kalmar zai dace don isar da ma’ana mai inganci.

Kammalawa

A karshe, wannan littafi ne da duk mai son fahimtar yadda kwamfuta ke aiki da gudanuwa zai fa’idantu sosai da shi.  Duk da cewa akwai kalmomin Ingilishi da dama, kamar yadda na sanar a baya, hikimar hakan a fili take. Rubuce-rubuce a harshen Hausa kan fannin kimiyya da fasahar sadarwa, musamman na kwamfuta, ba su yadu sosai ba a kasar Hausa.  Daga cikin manyan kalubalen da ke gaban harshen Hausa wajen ci gaba a wannan fanni, akwai rashin daidaituwar ma’anonin kalmomin Ingilishi na wannan fanni. Ma’ana, samun daidaito A tsakanin masana kan ma’anar kalma, misali: “Click”- “Matsa” ko “Danna?”  Haka idan ka dauki kalmar: “Storage” – “Ma’adana” take nufi ko “Ma’ajiya?”  Ga kalmar; “Memory”-“Kwakwalwa” take nufi ko “Ma’adana?”  Da sauran ire-irensu.

Wannan kalubale ne da ya kamata masana harshen Hausa a jami’o’inmu su tunkara, tare da hada kai wajen ganin an tabbatar da abin da zai zama abin dogaro.  Lokacin da marubucin wannan littafi ya aiko mini don tofa albarkacin bakina, abu na farko da ya fado zuciyata ke nan. Shi ya sa a karshe da na gama bitar littafin, daga cikin uzurin da na ba shi na rashin tabo ko magana kan ma’anonin da ya bai wa galibin kalmomin Ingilishi da ya kawo a littafin, shi ne rashin daidaitaccen tsari abin dogaro. A yanayi irin wannan kuwa, hanya mafi sauki ita ce samar da daidaitaccen tsari da zai bai wa wadannan kalmomi ma’anonin da aka amince a kansu.  Kafin samuwar hakan kuwa, dole ne mu hakura da abin da ya samu.  A hankali, wata rana sai labari.

An wallafa wannan rubutu ne a jaridar Amina ta ranar 4 da 11 da 18 na watan Janairun 2020

zaku iya samun Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) ta aikawa sakon email a wasiku@babansadik.com ta karamin sako ta wannan lambar 08034592444 (tes kawai)

Categories
Social Media Teburin Edita

Social Media: Muhimmancinsu wurin Da’awah da masu yin Da’awah

Gabatarwa

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, Mabuwayi mai Hikima, wanda ya sanar da mutum game da alkalami, ya sanar da mutum abin da bai sani ba, ya fitar da zamani mabanbanta da kuma shiryar da mutanen da suke cikin wannan zamani da hanyoyin da za su yi kira zuwa ga tafarkinsa.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin Rahama wanda ya sanar da Sahabbansa cewar “Ku kuka fi sani ga al’amarin duniyar ku” tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Iyalinsa da Sahabbansa da wanda suka bi shi da gaskiya har zuwa ranar tashin Alkiyama.

Social media a wannan zamani na daya daga cikin hanyoyin da jama’a suke yin amfani da su domin isar da sakwanni ko kuma karantawa da karantarwa, da ji ko gani na abubuwan da suka shafi rayuwar mu ta yau da kullum. Kuma bunƙasar amfani da irin waɗannan hanyoyin sadarwar kullum kara ɗaukaka suke yi da kuma sake samun sabon salo.

A ɓangaren abin da ya shafi Addinin Musulunci, waɗannan hanyoyin sadarwa na zamani kullum kara samun karɓuwa suke yi ga mabiya, da kuma jama’ar da suke son su san yadda ake yin addini ko kuma neman mafita a cikin abubuwan da suka shige musu duhu, ko kuma ga waɗanda ma ba su san addinin ba, suna son su san shi ko kuma me wannan addinin ya ke fada, ko domin kafa hujja da neman tozarta shi wannan addini, ko kuma neman diddigin me wane ya fada?

Mafi yawan mutanen mu da suke amfani da waɗannan sababbin hanyoyi suna amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba, ko kuma suna amfani da su domin biyan buƙatunsu na yau da kullum a maimakon amfani da waɗannan hanyoyi domin bunƙasa addinin musulunci da yin da’awa mai kyau cikin hikima.

A karshen wannan taƙaitacciyar ƙasidar da zan gabatar (In Allah Ya yarda) zan yi magana ne a kan

 • Mene ne Social Network?
 • Tarihin Social Media
 • Amfani da Social Media
 • Musulunci da Fasahar Zamani
 • Banbanci Tsakanin Social Media da Gidajen Yada Labarai
 • Sawa Musulmai da Musulunci Ido a Duniya bayan harin 9/11
 • Daukakar Addinin Musulunci bayan 9/11
 • Dole Malamai su shiga social media
 • Aikin Malamai a Socail Media
 • Kiyaye harshe da alƙalami a intanet
 • Shafukan da ya kamata malamai su bude ko mu’amala da su a Internet

Mene ne Social Network?

Social Media (shafuka ne ko manhajoji) hanya ce da ake yin amfani da ita a zamanance ta wurin yin mu’amala da jama’a a intanet domin fadin albarkacin baki ta hanyar yin rubutu, hadin gwiwa tsakanin mutane, musayar ra’ayi, da dai makamantansu.

Irin waɗannan shafuka (websites) ko manhaja (apps) na social media waɗansu su suna mayar da hankali ne wurin bayar da damar kirkiran dandali (forums), ko tura ƙananan sakwanni (microblogging), bunƙasa harkokin kasuwanci ko mu’amala tsakanin ɗaiɗaikun mutane (social networking), ajiyar kalmomi masu amfani (social bookmarking), matattarar shafukan intanet (social curation), da shafukan ajiyar bayanan gaggawa (wiki).

Waɗannan shafuka ana amfani da su ta hanyar ilmantarwa, nishadantarwa da faɗakarwa, tare faɗin abin da kake so a kuma lokacin da ka ke so.

Waɗannan shafukan za su iya samun rubutu zalla a cikinsu, ko kuma rubutun tare da liƙa musu hotuna masu motsi ko marasa motsi, ko kuma su ba jama’a damar ajiyar su hotunan a cikin ma’ajiyar wannan shafin.

Tarihin Social Media

Social Media kafin 1900

Idan muka ce za mu ɗauko magana a kan samuwar hanyar yin mu’amala da mutane wacce ita maƙasudin ko ginshiƙin social media to abu ne mai tsawo. Amma idan muka ce za mu danganta shi da yin mu’amala da jama’a ta hanya mai tsawo kuma ba tare da suna tare a wuri guda ba to za mu iya yin magana a lokacin fitowar telegraph wacce aka ƙirƙiro ta a shekarar 1792.

Telegraph a wancan lokacin ita ce ake amfani da ita wurin aikawa da sako a rubuce zuwa wani wuri mai nisa wanda saurin tafiyar tafi aike da abin hawa irin su Doki da makamantan su. Duk da cewar rubutun da ake aikawa da shi a wancan lokacin ba shi da yawa.

Bayyanar Wayar Tangaraho a shekarar 1890 da kuma bayyanar Rediyo a 1891 ya sake kawo sauyi mai yawa wurin yin mu’amala da mutane da suke wuri mai nisa. Duk da cewar har zuwa wannan lokaci da muke wannan magana ba a daina amfani da waɗannan Rediyo da Wayar Tangaraho ba amma kuma an sani sauya sauyen tsari, da kuma fasali a cikin fasahar su.

Social media a karni na 20

Kimiyyar fasaha da ƙere-ƙere ta canza abubuwa da yawa a cikin ƙarni na 20 canzawar da bata misaltuwa. Supercomputer ta farko an ƙirƙire ta ne a cikin shekarun 1940, daga wannan lokacin ne inginiyoyi suka bazama domin samun hanyoyin da za su iya sanya kwamfuta sama da daya ta iya ƙulla alaƙa tsakanin ta da ‘yar uwarta, wanda dalilin haka ne ya sa aka samu abin da muke kira a yanzu intanet.

Intanet a wancan lokacin irin su CompuServe an kirkiresu ne a wuraren 1960, kamar yadda imel na farko shi ma ya fito a wannan lokacin. A wuraren 1970s ƙulla alaƙa tsakanin kwamfutoci (networking) ya kara bunƙasa a wuraren 1979, kamfanin UseNet ya fara ba jama’a da su mu’amala da juna ta hanyar amfani da takardun su ta hanyar kwamfuta wato (virtual newsletter).

A wuraren shekarun 1980 kwamfutoci irin waɗanda muke amfani da su a gidaje da ma’aikatun mu suka fara yawaita a gidajen jama’a wanda daga wannan lokacin hanyoyin mu’amala da mutane suka ƙara ƙazancewa da yawa da kuma zama abin amfanin yau da kullum.

A wuraren 1988 aka fara yin amfani da intanet ayi magana na rubutu tsakanin jama’a wanda a yanzu muke cewa chating wanda ya ci gaba da tashe har zuwa cikin shekarar 1990s.

Shafin farko na intanet da aka fara kiran shi da social media shi ne shafin Six Degrees (sixdegrees.com)  wanda aka ƙirƙire shi a 1997. Daga nan aka fara samun bayyanar shafuka a intanet waɗanda suke yin rubuce-rubuce a kan al’amuran yau da kullum.

Social Media a wannan lokacin

Bayan bayyanar shafukan rubuce-rubuce (blogging), daga wannan lokacin social media ta fara ƙarfi da bazuwa a shafukan intanet ba ji ba gani. Websites irinsu MySpace da LinkedIn a farkon shekarar 2000 suka fara shahara, kamar yadda website irinsu Photobucket da Flickr su kuma suka zama shafuka na farko da suke ba mutane damar daura hotuna. A shekarar 2005 shafin YouTube ya bayyana.

A 2006 shafin Facebook da Twitter suka bayyana ga mutanen duniya su yi amfani da shi. Wanda su waɗannan shafukan suka ci gaba da zama shafuka mafi shahara har zuwa wannan lokacin da muke ciki a yanzu.

Amfani da Social Media

A zuwa wannan lokaci kusan kullum ana samun ɗaruruwan shafukan sada zumunci wanda suke ɗauke da abubuwan ci gaba da kuma sake sabon salo na yadda jama’a za su samu sauƙi wurin yin mu’amala da jama’a.

Kamar yadda aka rubuta a shafukan ƙididdiga na brandwatch.com sun fadi cewar shafin Facebook shi ne shafin da ya fi kowane shafin zumunta yawan mabiya da kuma saka abubuwa a cikin sa wanda ya ke da mabiya sama da biliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai (1.7 Billion). Amma ta wurin ziyarta da duba abubuwan da ke cikin intanet, shafin YouTube wanda ya ke ajiyar hotuna masu motsi ana kallon bidiyo a rana guda sama da biliyan ɗari da biyar (105 Billion).

Shafin internetlivestat.com sun ƙiyasta sama da mutume biliyan uku da rabi (3.7 Billion) suke amfani da intanet a duniya, wanda ya ke nuna cewar kusan rabin mutanen duniya ke nan. A Najeriya kuwa sama da mutane miliyan tamanin da shida (86 Million) suke amfani da intanet, kamar yadda sama da mutane miliyan sha bakwai (18 million) ke amfani da shafin sada zumunci na Facebook.

Idan muka duba ta ɓangaren amfani da ake yi da irin waɗannan shafuka sai mu ga ana amfani da su ta hanyar jawo ra’ayin jama’a zuwa ga abubuwan da mutane ba su san shi ba, ko manufofin waɗansu jama’a. Kamar yadda kuma ake amfani da irin waɗannan shafukan domin samun bayanai game da mutum da abubuwan da ya fi mayar da hankali a kansu.

Ana amfani da su wurin nuna ɗabi’u da al’adun mutane, aikace-aikacen jama’a da kungiyoyi, manufofin jama’a da yada addinan su, fadin ra’ayin da kare ra’ayi da dai makamantan su.

Saboda haka yaɗuwar kafofin sada zumunci a wannan lokaci sun yi karfin da bai kamata a ce an bar masu hankali da seta hankula wurin shiga domin a dama da su ba. Kamar yadda musulmai bai kamata a ce sun yi baya-baya ba wurin yin amfani da waɗannan shafuka domin yaɗawa da kuma kare martaba ta Addininsu da kuma mutuncin jama’ar su ba.

A baya, duniyar musulunci masu bincike sun mayar da hankalinsu wurin yiwuwar amfani da irin waɗannan kafafe na social media, waɗansu kuma suna duba amfanin shi da kuma illolinsa. Amma a yanzu tuni al’ummar musulmai suka fahimci cewar lallai yana da kyau su kasance a cikin wannan tafiyar musamman domin a wannan lokaci da ake ƙoƙarin yabawa Addinin Musulunci kashin da ba nashi ba.

Musulunci da Fasahar Zamani

A baya, abubuwan da suka shafi addinin musulunci ana samun su ne kawai a cikin littattafai, kaset-kaset na sauti ko na bidiyo, wanda ake ajiyar su a cikin gida, masallatai, ɗakin binciken ilimi, wanda musulmi ko wanda ba musulmi ba, ba zai iya samun su ba sai idan sun kusanci inda suke.

A yanzu haka za ka iya samun dukkan waɗannan tsarin ilimin na Alkur’ani, Hadisi, Sunnah, Sirah, Fiqhu da duk wani ilimi da mutum ya sani a shafukan intanet. Ana iya samun su da harshen Larabci, ko Turanci ko Hausa, Yarabanci, Inyamiranci da dai waɗansu yare da jama’a suka fi amfani da shi. Haka za ka samu irin waɗannan karatuttuka a rubuce, ko a cikin sauti, ko kuma a hotuna masu motsi da marasa motsi, dukkan su kuma a cikin intanet.

Haka kusan dukkan waɗannan abubuwan da muka lissafa za ka same su a cikin irin waɗancan shafukan na social media. Mu sani miliyoyin mutane a yanzu, musulmai da waɗanda ba musulmai suna mayar da hankalinsu a yanzu wurin yin amfani da irin waɗannan karatuttuka da muke sakawa domin sanin addinin musulunci da gaskiyar magana game da shi, ɗabi’u, halayya da kuma me jama’ar wannan addinin suke ciki.

Banbanci Tsakanin Social Media da Gidajen Yada Labarai

A zamanin baya kana bukatar kashe kudi sosai wurin daukar ɗawainiyar saka wani karatu ko sanarwa a gidajen Talabijin ko Rediyo, wanda irin waɗannan saƙwanni ba dole ya kai ga waɗanda ake so ba. Matsalar ɗaukewar wutar lantarki a yanzu ya isa mutum yayi asarar kuɗin da ya biya ko kuma jama’ar da yake bukatar su sami wannan sako. Neman isar da wannan sako ya takaita ga inda kake, misali wanda yake a Sakkwato idan ya bayar da sanarwa a gidan Talabijin na Sakkwato to ‘yan Sakkwato kawai zamu gani wanda ya ke wani gari ba zai gani ba.

Idan kuwa kana son wanda yake wani gari ya gani to ko dai ka aika da shi kowace jiha, ko kuma ka biya babban gidan Talabijin na Kasa domin ya saka, wanda shi ma magana ce ta kashe maƙudan kuɗaɗe.

Amma idan muka dawo ta bangaren shafukan intanet, su ba za mu hada su da gidajen Talabijin ko Rediyo ba domin matuƙar abin da aka saka na saƙo ko karatu ba a goge shi ba, to idan aka koma za a same shi.

Social media irin su facebook wanda muka ce yana da mabiya sama da (1.7b), cikin minti kaɗan idan ka saka saƙo ko karatu miliyoyin mutane ne za su samu, kuma za su gani a kowane lokaci kuma za su iya aikawa masoyansu wannan sako, masoyan masoyansu suma za su iya gani.

Haka ba dole sai a daidai wannan lokacin da ka saka wannan sakon za su gani ba, duk lokacin da mutum ya shiga cikin ɗakin sa zai ga sakon cewar wane ko shafi kaza sun saka abu kaza kuma idan ka taɓa wannan sakon zai sake bayyana ba tare da wata matsala ba.

Shi yasa ba yadda mutum zai iya daidaita muhimmancin waɗannan kafafen sada zumunci na zamani da kafafen yaɓa labarai na da da ake da su.

Sanyawa Musulmai da Musulunci Ido a Duniya bayan harin 9/11

Tun bayan da aka kai harin babbar cibiyar kasuwanci ta Duniya dake kasar Amurka, a 11/9/2001 musulmai da ke faɗin duniya suka shiga cikin wani mawuyacin hali musamman wadanda suke zaune a kasashen turai.

Sama da musulmai dubu 200 zuwa dubu 500 suka shiga cikin matsatsin bincike da kuma tsangwama a ƙasar Amurka, sama da musulmai dubu 18 aka mayar da su garuruwan su, musulmai dubu 15 wasu aka ɗaure su a gidan yari wasu kuma an tsare su domin tuhumar su.

An rage daukar ma’aikata Musulmai da kashi 10% a cikin Amurka gaba daya. Musulmi shi ne karshen wanda za a ɗauka aiki kuma shi ne farkon wanda za a fara sallama.

Duk takardar neman aikin da ta fara da sunan Muhammad ko Ahmad ba ta zuwa ko ina ba, kamar yadda sauran sunayen da ba su ba na musulmai suna iya tsallakewa. An kiyasta kashi 40% na Musulmai da suke garuruwan Brookly da New York da Chikago da Devon Ave sun rasa aikin su.

Kusan kashi 75% na musulman da suke kasar amurka zai wahala wani yace maka bai fuskanci tsangwama, cutar wa, wulaƙanta wa ko jifa da duka saboda wannan harin da aka kai.

Wannan harin da aka kai ya sanya kasar Amurka ta yaƙi ƙasar Iraƙi da Afganistan da kuma yaƙi da ta’addanci a fadin duniya baki daya.

Gidajen yada labarai da gidajen shirya fina-finan kasashen waje, gidajen Rediyo da Talabijin, Mujallu da Ƙasidu da shafuka a Intanet sun taimaka matuƙa wurin yaɗa furofaganda cewar addinin musulunci addinin ta’addanci ne da kuma addinin rashin son zaman lafiya.

Daukakar Addinin Musulunci bayan 9/11

Duk da irin waɗancan abubuwa da suka faru da kuma takura da musulmai suka yi a cikin wannan ƙasar ta Amurka, bai hana wannan addinin ƙara ɗaukaka ba, domin kamar yadda aka rubuta a cikin wata ƙasida mai take “A Wave of Conversion to Islam in the U.S. Following September 11” cewa sama da mutane dubu 34 ‘yan ƙasar Amurka ne suka karɓi Addinin Musulunci bayan da aka kai harin 9/11.

Ƙoƙarin da Musulman ƙasar Amurka suka yi da kuma juriya da canza salon mu’amala da fito da haƙiƙanin karantarwar Addinin Musulunci da rubuce-rubuce a shafukan sada zumunci irin na social media sun taimaka matuka wurin kara fahimtar addinin musulunci.

Addinin musulunci a yanzu shi ne addini na uku da ya fi yawa a kasar Amurka, bayan kiristanci da addinin buda, kuma musulunci shi ne addinin da ya fi karbuwa a cikin wannan kasa a yanzu. A yanzu akwai sama da masallatai na salloli biyar sama da dubu biyu da dari biyar.

Kafin lokacin da yawan turawan yamma babu abin da ya shafe su da addinin, da yawa daga cikinsu mutane ne waɗanda ko imani da cewar akwai wanda ya hallici duniya ba su yi ba, ballantana su yi imani da kiristanci ko kuma addinin musulunci.

Irin rubuce-rubucen da suka cikin Intanet dangane da karantarwa ta Addinin musulunci ya taimaka wurin kara fahimtar musulunci da kuma me addinin yake karantarwa.

Dole Malamai su shiga social media

Kasancewar malamai suna suka fi kowa hankali da sanin abin da ya dace da al’umma da zamaninsu ya sanya wajibi ne kowane malami mai da’awa ya kasance a kalla yana da shafi a cikin wadannan shahararren gidaje a intanet domin isar da sakon Allah madaukakin sarki.

Kasancewar wadannan shafukan suna da yawa, kuma akwai abubuwan da ya kamata malamai su sani na shirme da shiriri ta da batanci ga addinai, da rashin girmama mutane, da rashin kamun kai, da rashin boye tsaraici da fito da alfahasha da abin ki.

Kasancewar daya daga cikin wadannan abubuwan da muka lissafo ya sanya wajibi ne malamai su shiga cikin irin wannan shafuka domin yin wa’azi da kuma gyara ta hanyar da ya dace.

Matsalar da muke fama da ita a irin waɗannan sababbin al’amura shi ne malami ya yanke wani hukunci cikin abin da bashi da cikakkiyar masaniya akai, musamman lokacin da yake son yayi gyara akan abu alhali bai san wannan abin ba ko kuma bai ma taba yin mu’amala da shi ba.

Aikin Malamai a Socail Media

‘Yancin yin magana:- Daya daga cikin cikin abin da ya fi shahara a cikin irin wadannan shafuka shi ne yar da jama’a suka cewar kowa na da ‘yancin fadin abin da ya ga dama ko da kuma zai ci karo da cin mutunci ko batanci ga wani ko kuma tozarta addinin wani.

A nan aikin da malamai za su yi shi ne su fadawa mabiyansu yin magana cikin abin da ya kasance maslaha ga al’umma da kuma fada musu cewar mutum musulmi ba shi da ‘yancin fadin komai da ya ga dama, kuma babu wani dalilin da zai sa saboda ka sada da wani a ra’ayi kace zaka fadi maganar da kaga dama. Musulunci shi ya zo da kame harshe mutukar mutum ya san ba alkairi zai fada ba.

Gyaran Tarbiyya:- Samari da yawa da ‘yan mata suna shiga cikin wadannan shafukan domin holewa da kuma samun sababbin abonkai da sanin abubuwan rayuwa. Daga cikin abin da ya fi damun mutane da social media shi ne rashin tarbiyya da ake yadawa a ciki, wanda kuma zai wahala ka samu irin wadannan yaran basu da alaka da wani shafi na wani sanannen malamin addini, ko kuma group na mutanen kirki wadanda suke fadakarwa da kuma yin nasiha ga irin wadannan dabi’u marasa kyau.

Batanci Ga Addini:- Wannan daya ne daga cikin matsalar da ake fama da ita cikin intanet da kuma social media. Domin idan ba wani wuri da ya kamata malamai su rika yin saurin yin magana da Musulmai irin mayar da martani a lokacin da aka yi batanci ga Addinin Musulunci ko kuma Ma’aiki SAW.

Idan muka duba yawan mutanen da suke cikin intanet musamman social media za muga cewar kusan mutane biliyan uku ne (3billion), to me kake tsammani zai faro a lokacin da wanda ba shi da ra’ayin addininka ya tashi yin wata magana ta batanci ga addinin?

A wannan wurin ya ke da muhimmanci malamai su shigo domin baiwa wannan addinin kariya cikin hikima da kuma bayar da gamsassun hujjoji domin kariyar wannan addinin. Domin da za ace abar wanda bashi da ilimi yayi magana a cikin irin wannan al’amari to zaka samu cewar abubuwan kara bace suke yi ba wai gyaruwa ba.

Idan muka duba irin yadda malamai turawa irin na kasashen waje musamman irin su, Zakir Nail, Yusuf Estes, Khalid Yasin, Muhammad Auwal zamu ga cewar duk lokacin da wani ya fito yayi batanci ga addinin musulunci su kuma suna shiga kafefen intanet domin su jawo hankalin mabiyansu da kasa su mayar da wani martani domin zai iya yuwuwa sun yi haka ne domin takalar musulmai da musulunci.

Rashin Girmama Mutane:- Idan kana bibiyan rubutu da ake yi a irin wadannan shafuka na sada zumunci sai ka samu mutanen da suke kiran kansu masu hankali sai ka samu suna kuma yin abubuwa na rashin girmama mutane ko kuma ra’ayin mutane.

Shafin sada zumunci cike yake da sabanin ra’ayi, duk inda mutum ya ke da kokarin yin bayani gamsasshe dole sai wani ya ji an saba mishi ta wani wuri, shi yasa zaka samu rashin girmama ra’ayin jama’a da kuma yin magana ta adalci ga wani mutum da ya kawo sabanin ra’ayi.

A nan malamai za su iya kawo sauyi wurin koyawa mabiyansu yadda ake yin magana da ta sabawa ra’ayi, da kuma kore zage-zage da aibace-aibace da ya cika wannan gidaje.

Rashin Boye Tsaraici:- Idan aka yi magana a kan tsaraici to ba a iya cewa komai a intanet ko social media, duk da cewar kamfanonin da suke da wadannan shafuka suna kokari matuka wurin tsaftace shafukansu daga irin wadannan hotuna na batsa ko tsiraici.

A nan malamai za su iya shigowa domin kawo sauyi ta hanyoyi da dama, kamar yin rubuce-rubuce da wa’azoji a shafukansu na hatsarin irin wadannan abubuwa da ba su dace ba.

Kiyaye harshe da alkalami a intanet

Yana da kyau malamai su sani cewar babu abin da ya fi intanet ko social media saurin yada abu a duniya, wannan ya ke nuna mana cewar ya zama wajibi malamai su san me zasu fada a lokacin da suke gudanar da muhadarorinsu ko wa’azi ko kuma wani rubutu wanda ba zai dauki wata fuska ko ma’ana ba.

Babu wanda zai fada malami mai ya dace ya fada, amma kuma kamar yadda ka san cewar magana zarar bunu ce, to haka rubutu a intanet ya ke, duk abin da ka rubuta miliyoyin mutane za su iya ganin cikin dan kankanlin lokaci, kuma nan take wadansu za su fara yada shi ba tare da ka basu umarni ba.

A wannan lokacin da musulmai suke neman hanyar da zasu gamsar da jama’ar duniya kyawawan dabi’un musulunci, yana da kyau su sani dukkan wani rubutu ko karatu da za su saka a cikin shafukansu to ya kasance bai bada wata kofa da zai kara dakushe karfin addini ba.

Malamai su sani cewar yaki dan zambo ne, duniya ta zare takobin yaki da musulunci da musulmai, saboda haka a wannan lokacin yana da kyau a kiyaye saurin yanke hukunci a cikin duk wani al’amari da aka ga wani ya yi dangane da batanci ko kuma soke wani ra’ayi ko hukunci na addinin musulunci da gaggawa.

Malaman da suka fahimci zamanin su sun san sau tari wani abu da ake yi a cikin social media ana yinsa ne domin a tunzura musulmi, saboda haka saurin yanke hukunci ko kuma yin gaggawar fadin magana zai iya kaiwa ga sake fito da wata matsalar ko kuma wata barna.

Lokacin da turawan faransa suke kokarin yin batanci ga fiayyen hallita Annabi Muhammad SAW, ta wurin zana shi ta mummunan hotuna, da shirya fina-finai na yara domin cimma wannan manufa ta su.

Daya daga cikin manyan malamai masu yin da’awa kuma limamin juma’a Muhammad Auwal ya ce ya kira sauran malamai irin su Yusuf Estes, Khalid Yasin domin su yi rubutu a kan kyawawan dabi’un Annabi Muhammad SWA. A wannan satin sai da suka sami karuwar daruruwan musulmai wadanda ba su taba sanin musulunci ba.

Duk lokacin da wani ya yi batanci ga addinin musulunci ko da masu da’awar musulunci ne wadadna suke kai hari domin kashe mutane babu gaira babu dalili, ko kuma ke zargin wani malami da ta’addanci gidajen yada labarai suna kokarin yadawa, wani lokacin ma sai ka ji kamar babu wani abin da wadannan gidajen jaridu suke yi sai hakan.

A gefe guda kuma, wadanda ba su da ilimi ko sani game da wannan addinin ko kuma abin da wannan malami ya ke yi, suna shiga shafukan intanet su yi ta bincike game da wannan al’amari wanda ya ke yanzu ra’ayin su suke koma addinin musulunci.

Shafukan da ya kamata malamai su kasance a ciki

Kasancewar su wadannan shafuka suna da yawa wanda sanin adadinsu sai Allah, kuma ba kowanne ba ne yake da muhimmanci kuma ba kowanne ba ne jama’a suka yin mu’amala da shi ba, ya sanya na zabo abubuwa guda bakwai da ya kasance malamai su shiga cikinsu domin su taimaka wurin isar da sakon Allah.

Website/Blog

Mallakar shafin malami na shi na karankanshi ya fi komai muhimmanci domin a nan ne za a iya samun rubutunshi ko wa’azozin shi, ko karatukansa. Shi mallakar wannan shafin ya na matakai masu dama, tun gaba mallakar suna, dakin da zaka adana bayanai da kayanka da kuma wanda zai kirkiri wannan shafin da kuma lura da abin da za a saka a cikinsa.

Facebook

Shafin facebook shine shafin da ya fi kowane yawan mabiya,wanda yake da mabiya kimanin,bilyon daya da dubu dari takwas,a najeriya yana mabiya kimani mutane miliyan goma sha takwas,wanda yana da kyau ace kowane malami yana da account a shafin facebook kuma yana da page din zuba bayanai  game da  addini (fans page).

Twitter

Shafin twitter shima shafine da yakamata ace malamai su mai da hankali akanshi, wanda shine farkon microbloging web site wanda yake ba mutane dama suyi rubutun wasika da bata wuce harufa dari da sit

YouTube

Youtube shafi ne wanda yake ba mutum dama ya daura video komin yawanshi komin nawinshi, wanda ake shiganshi sama da bilyon hudu a rana,

Sound Cloud

Sond cloud shafi ne wanda yake ba mutum dama ya dora ko wane irin karatu a cikin sauti

LinkedIn

Linkedin shafi ne da yake bamawa mutum dama ya rubuta game da shi,tarihinshi,inda yayi karatu,matsayinshi a fannonin rayuwa.

Wikipedia

Wikipidia shafi ne da ya shahara wurin  baiwa mutane damar warware mas’aloli akan  ilimi, mas’alolin da suka shafi tarihin wani.

Rufewa

Kamar yadda muka ji a yanzu yana da kyau malamai su fahimci cewar Social media yana da matukar muhimmanci gare mu, domin amfani da shi wurin wayar da kan alumma game da abin shafi addini na karatuttuka, da kara bunkasa harkokin addini, tare da fadakarwa da nasihohi ga alummar Musulmi

Categories
Teburin Edita

Mujalla Ta Farko – Barka da Zuwa Duniyar Computer

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Kai, muna yi wa alummar hausawa da masu jin hausa murnar gabatar musu da wannan Mujallar Duniyar Computer.

Mun riga mun yi bayanai na makasudin fito da wannan mujalla a manufofinmu da ke shafi na biyu. Wanda ya kunshi dukkanin bayanai da ya kamata wanda zai karanta wannan mujalla da ya fara karantawa. Amma dangane da abubuwan da yake kunshe a cikin wannan bugu na farko, da farko zamu bai wa mai karatu hakuri na yawan rubutu da zai gani da kuma shafuka masu yawa, wannan ya samo asaline saboda shawara da muka yanke na zubo muku dukkanin abubuwan da muka saka a shafinmu na Internet, da kuma dukkanin tambayoyin da muka amsa a shafin dandalinmu na Facebook.

A cikin wannan fitowa mun yi cikakun bayanai akan mahimmancin ilimin computer, sannan kuma mun saka wata makala wacce take mai mahimmanci mai taken “Hankali ke gani ba ido ba” wanda wannan makala ta taba kowanne bangare na zamantakewar al’ummarmu akan abinda ya shafi ilimi da kuma harkar Computer. Bayan haka mun yi gamsassun bayanai akan abinda ya shafi maganar Computer Virus da yadda yake shiga Computer ko kuma wayar tafi da gidanka, sannan kuma mun kara bayanan cututtuka guda biyar kari akan biyar da muka saka a shafinmu na internet a makalarmu mai taken “Wurare guda 17 da suka fi ko’ina hatsarin shiga a Internet”.

A wannan fitowa mun saka wadansu makalai wadanda babu su a shafinmu na Internet wanda suka hada da babbar mukala mai taken “Mece ce Computer” inda muka warware abubuwa masu yawa akan ita kanta computer daki daki. Sannan mun tattauna da wasu dalibai ‘yan Najeriya da suke karatu a kasar Ghana wanda suka yi gamsassun bayanai akan yadda rayuwarsu take gudana da kuma karatunsu. Duk a cikin wannan fitowa mun saka Cikakken Tarihin Bill Gates.

Sannan kuma mun saka dukkanin tambayoyin da muka amsa a shafinmu na dandalin Facebook, domin wanda yake da irin wannan matsaloli da muka warware ya karanta kuma ya fahimta. Kasancewar wayar tafi da gidanka tana da wani fage mai fadi a computer shima mun tsakuro muku bayanai akan “Yadda ake yin Flashing na waya” wanda ya warware zare da abawa akan abinda ya shafi waya.

Da yake wannan mujallar ta ilimice kuma makasudin mu shine yin bayanai akan abinda ya shafi computer a ilmance, kusan duk abubuwan da muka saka a cikin wannan mujalla sai da aka tabbatar da ingancinsu da kuma tabbacinsu. Sannan kuma mun yi kokarin gwada dukkan wani ilimi da muka saka mun kuma tabbatar da haka yake.

Daga karshe muna son mai karatu ya sani cewar abubuwan da ya gani a wannan mujallar kusan ba shi bane yadda mujallar za ta kasance ba, duk da cewar mun yi kokari wajen tsara makalolinmu akan tsarin Hardware, da Software da networking da portable devices, mun yi magana akan Yadda Akeyi da kuma Ra’ayi wadanda sune tsarin da muka bi a shafinmu na Internet .

Fitowa ta gaba shi ne wanda zai nuna maka shirin wannan mujalla na asali, amma wannna fitowa mun saka dukkanin abubuwan da suke cikin shafin mu na internet sai kuma wasu kare-kare da muka yi domin ku masu karatu. Mun san za a sami gyara a cikin hausa ko kuma rubutu, to, muna neman afuwa akan haka, muna maraba da dukkanin wane korafi da kuma abin ci gaba. Kuma muna maraba da masu rubutu daga ko’ina suke a fadin duniya. Allah yayi mana jagora Amin. A sha karatu lafiya.

Salisu Hassan (Webmaster)
Babban Edita