Categories
Software Tsaro

Spy App: YAYA SUKE YIN AIKI?

A yanzu yana da wahala a kasar da aka ci gaba ka samu a wayar yara da ‘yan mata babu manhajar bibiyar wayoyi a cikinta ko dai don tsaron shi wannan yaron ko kuma tsoron kada wani abu ya faru da shi

Manhajojin leken asiri da ake sakawa a waya (spy app) wadansu application da suke zama a cikin wayar mutum ba tare da saninsa ba domin satar wadansu bayanai daga cikin ita wannan wayar. Irin wadannan manhajoji suna iya nado dukkan kiran da ya shigo wayar mu ko ya fita, haka suna ina kwace sakon kar-ta-kwana na SMS ko wasu muhimman bayani. Dukkan abin da irin wadannan manhajoji suka dauka suna aikawa cikin babbar kwamfutar wadanda suka kirkiri shi wannan manhajar. Shi irin wannan application yana aiki a cikin wayar mutum ta karkashin kasa ba tare da kai mai wayar kasan yana aiki ba ko ma fahimtar an saka maka shi a wayar ba.

Banbancin aikin da kowane application na neman sirri yake yi ya danganci da irin abin da wadanda suka kirkiro shi suka ce yayi. Zaka saka wannan app din a wayar mutum sannan ka saka shi application din lasisin da ka biya a hannun masu app din, daga nan shi application din sai kawai ya ci gaba daga inda aka tsaya.

Yadda ake saka shi (Installation)

Dole kana bukatar a kalla koda sau daya ka samu damar rike wayar mutumin da kake son ka saka irin wadannan application, ke nan dole sai mutum ya bayar da wayarsa ta shiga hannun mutumin da zai kasa application din kafin wannan application yayi aiki. Wannan yake nuna cewar ba a iya tura wannan application ta intanet.

Application irin su Hoverwatch suna da sauki wurin sarrafa su, sannan ana iya girke su a cikin waya cikin dan kankanin lokacin. Yana aiki a karkashin kasa ba tare da me wayar ya sani ba. Da zarar an gama sakawa, zaka iya sani da kuma bibiyar dukkan abin da ke gudana a cikin wayar wannan mutumin da ka saka wannan application ba tare da kana kusa da wayarba ko kuma ma a ce ka taba wayar. Dukkan abubuwan da wannan application yake nadowa da kwasowa yana aikawa da shi a wani mazubi na musamman da yake sama ta hanyar harbawa ta intanet, sannan ana amfani da browser wurin ganin su wadannan abubuwa.

Jaibreaking da Rooting

Idan kana son ka saka irin wadannan application masu aiko da sirrin mai amfani da waya sai ya kasance wayar idan ta iPhone ce dole sai an fitar da ita daga bursunar ta (jailbreaking). Jailbreaking na nufin baiwa wayar iPhone damar amfani da manhajojin da kamfanin Apple ba su amince da su ba. Baka bukatar rooting idan wayar android ce amma kana bukar yin rooting idan har kana son yin amfani da irin wadannan app domin aiki mai zurfi, misalin shiga cikin harkar kiran mutum ko sanin wane iri tattaunawa ta rubutu (chat) muke yi na rubutu kai tsaye.

Amma idan kana jin tsoron yiwa iphone din jailbreaking to zaka iya amfani da mSpy no-jailbreaking solution wanda shi yana amfani da browser ne wurin bibiyar kiran waya (call logs), bibiyar rubuce-rubuce kamar iMessages da text nessages har da WhatsApp. Haka zaka iya amfani da wannan app domin ganin irin shafukan da yake shiga a intanet duk ba tare da anyi jailbreaking ba.

Abin da kawai kake bukata shine ka samu Apple ID da abubuwan sirri na shiga wayar, sannan ka bada damar iCloud Backup yayi aiki duk akan wayar.

Masarrafin ta Intanet ne

Ana amfani da masarrafin Intanet wurin kallon abubuwan da aka shirya ita wayar ta rika turowa wanda ya hada da kiran waya, sakonni na sms, email, hotuna, bidiyo, lambobin cikin waya, abubuwan da mutun yake yi a browser da makamantansu.

Daga jikin dandarin allon browser zai baka damar gabatar da abubuwa kamar haka:-

 1. Saukarwa da bibiyar abubuwan da aka gabatar a wayar da ake leken asirinta wanda ya hada da nadar sauti, hotua da bidiyoyin da ke cikin wayar, duba sakwannin dake kan wayar kai tsaye daga kan taka kwamfutar.
 2. Samun damar sarrafa wayar tamkar tana hannunka ta hanyar rufewa ko bude wayar, fara nadar abin da ake tattaunawa kai tsaye, katse wayar da mutum ke yi har da iya goge ita kanta manhajar a cikin wayar mutum.
 3. Shirya alat ko amo na shigowar sakwanni ta hanyar zabar wadansu kalmomi da idan aka yi amfani da su a wayar ko rubutu kai tsaye zai turo inda kake son sakon ya je.
 4. Samun damar sarrafa dukkan shirye-shiryen kundinka har da yadda zaka iya biyan kudi.

Karfin Manhajojin Leken Asiri

Mafi yawancin irin wadannan manhajojin leken asiri irin su Mobile Spy da mSpy da Highster da FlesxiSPY suna aiki a wayoyin Android da iOS. Kafin ka siya daya daga cikin su yana da kyau ka bibiyi shafukansu domin sanin wayar da kake son ka rika bibiyar abubuwan cikinta zata iya aiki da shi manhajar ko a a.

Amma mafi yawancin wadannan wayoyin Android masu zubin 4.0 zuwa sama suna aiki da manhajojin amma wadansu basa baka cikakkiyar damar sarrafa wayar sosai sai idan an yi rooting dinta.

Damar shiga Intanet

Su irin wannan manhajoji dole suna bukatar intanet domin su yi aiki sosai, mutukar babu intanet a jikin wayar wanda ake son leken asirinsa to wancan software ba zata yi aiki ba, duk da cewar wani lokaci wadansu daga irin wadannan manhajoji kan tara bayanai a wani bangare na waya da zarar ka samun sinadarin shiga intanet sai su ci gaba da aika sakonni ba tare da sanin ka.

Rufewa

Mu sani su wadannan manhajoji na leken asiri Spy App an tsara su ne domin bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikin wayoyin tafi da gidanka (Smartphones) domin nadar dukkan abin da ke faruwa a cikinsu.

Wadansu iyaye sukan yi amfani da irin wadannan manhajoji a wayoyin yaransu domin lura da abin da yaro yake yi na shige da fice da wayarsa. Haka suma ma’aikatu sukan saka irin wadannan manhajoji a wayoyi mallakarsu su baiwa ma’aikata domin sanin meke faruwa da ma’aikatansu kamar a imel dinsu ko abinda suke yawan yin browsing.

Kafin ka sayi kowane irin Spy Software, ka tabbatar zata iya shiga cikin wayar wanda kake son yi leken wayarsa sannan suna aiki ne a wayar Android da aka yi rooting dinta, idan kuwa iOS ce ta wata tana bukatar sai an fitar da ita daga kurkuku wato jailbreaking.

Categories
Social Media Software

ABUBUWA GOMA DA BAI KAMATA MUTUM NA YI BA A ZAUREN MUHAWARA (GROUP CHAT)

Mafi yawancin mutane a yanzu sun fi amfani da manhajoji sada zumunci ko kuma na yin muhawarori win tura sakonni a cikin wayoyinsu, a maimakon amfani da hanyar da aka sani ta aikawa da karamin sako wanda aka fi sani da (SMS).

Hakika group chat ya kawo sauki wurin tura sako ga dumbin mutane a lokaci guda, domin a cikinsa bayan rubutu da muke iya turawa, za kuma mu iya tura hotuna, bidiyo wani lokaci ma har takardu ana iya turawa, da wannan dalilin nag a ya dace mu fadawa mutane abubuwa guda goma wadanda bai kamata muyi amfani da su ba a lokacin da muke mu’amala da mutane a wurin tattaunawar.

 1. Kada ka kirki zauren muhawara mai mutane dayawa.

Mafi yawan manhajoji na tura sako (messaging applications) suna bada adadin mutanen da zaka iya aikawa sako a cikin zauren muharawa (group chat). Duk da wasu suna bada damar kari da kauda ido  daga adadin da suka kayyade bai zamo dama garemu ba mu yi ta kirkiran gidaje da dakunan muhawara barkatai ba. Kasancewar a misali dandalin WhatsApp ya baka damar saka mutane 190 a matsayin mambobi ba shi ke nuna cewar sai ka saka kowa da kowa a ciki ba.

Ko da ka kirkiri wannan zaure domin ka rika sanar da wani taro ko Muhadara ko wa’azi, wani lokaci abin zai baka mamaki idan ka sanar da wani sako da kake bukatar ayi magana gamsasshiya sai ka samu wadanda ba su san muhimmancin wannan zaure ba suna iya aikawa da sakon ‘k’ ko kuma ‘okey’.

 1. Kada ka saka mutanen da baka sani ba ac ikin group chat din

Ya fi muhimmanci ka saka mutane sanannu wanda kowa a zauren muhawaran (group chat) ya sansu. Bana son in rika yin magana da kai haka kuma ba na son ka samu lambar wayata, wannan na daya daga cikin dalilin da ya sanya bai dace ka dauki duk wanda kake da su a cikin akwatin ajiyar lambobin wayarka ka saka su a cikin grouph chart ba. Kasancewar lallai duk wanda ka saka shi a chart to yana da damar ganin lambar kowa da ke ciki wanda wannan ba zai yi wa wadansu dadi ba.

 1. KADA AKYI CHARTING DA MUTUM DAYA KACAL:

Yana da kyau kasan muhimmancin yin magana da kowa da kowa a cikin  zauren muhawara (group chat) ba tare da kebance mutum guda daya ba. wurin yin maganar da ta shafe ku  biyu yafi kyau ace ku kebance  a wajan zauren muhawarar (group chat) din. Maganar da kowa a zauren yake bukatar ji ita ake yi ac ikin zauren.

 1. KADA KA KAWO ZANTUKAN DA BA MUHALLINSU BA:

Yana da kyau ga me charting ya rin ka kawo zantuka gamsassu da suka dace a inda suka kamata, shi chating ana yin shi ne da abin da ya shafi aikace aikace hadin kai, taimakon juna da dai makamantansu. Zaka ka iya fusakntar aikin da aka baka ta yadda zaka kai ga cin masa, zaka iya zama ka nutsu ta yadda zaka cin ma maufarka.

Shin ko kana tattaunawa game da abin da ya shafi makaranta ta yadda za ku kara samun jituwa a tsakaninku? Ko kuma hirar dayanku ne a kan abin da ya shafi zaman ku na karshe, duk abin da bai shafi maudu’in da aka tsara ba, bai kamata mutum ya shigo da wani magana in ba ta maudu’in ba.

 1. KADA KA TURA KARYA KO ABIN DA BAI KAMATA BA:

Idan kana chating kayi takatsantsan da zantukan daka ke rubutawa tare da tabbatar da duk abin da ka rubuta ka samo shi daga mattabbata mai inganci. Ka da neman sauki ya sa ka rika dauko ruburu daga wadansu zaurukan ko kuma shafuka kana sakawa a cikin naku zauren ba tare da ka tantance gaskiyar maganar ba.

 1. Kada karubuta banza da

Duk da shafin muhawara ya baka dama ka rubuta abin da ka ga dama, hakan  ba dama bane a gare ka kayita rubuta banza hofi ko maimata abin da wani ya fada ba. Bai kamata a rubuta abin da bai kamata a cikin wurin da aka kebance domin tattauna wadansu abubuwa mamu himmanci ba. Misali za ka ga zaure na addini ne amma sai a sako maganar kwallo, ko kuma zauren tattaunawa a kan yadda za a bunkasa harkokin lafiya sau kaga wasu suna saka magana a kan soyayya ko makamantan haka.

 1. Kada Kayi shiru

Yin shiru a lokacin da ake tattaunawa a kan abubuwa masu muhimmanci matsala ce ga mutane da yawa a cikin zaurukan, duk lokacin da aka bijiro da wani maudu’i mai muhimmancin kuma ake bukatar kowa ya fadi ra’ayinshi to yana da kyau ka fadi naka ra’ayin, domin kada a zartar da wani abu da bai kamata ba kuma ka zauna kana korafi daga baya.

 1. Kada katura kalma daya a matsayin amsa

Domin neman saukin rubutu kada ka tura rubutu kalma daya saboda za ta iya daukar ma’ana da yawa ko kuma ayi mata wata fahimta daban da abin da shi kake nufi ba.

 1. Kada ka aika da sako a lokacin da bai kamata ba 

Idan ba zaka kira mutum da safe ko da ran aba mai zai sa ka kira shi can da daddare yana bacci. Idan kasan bai dace a tura sako a lokacin da ba yini ba ko kafin lokacin bacci yayi, to kayi amfani da wannan dubara ga manhojojin tura sako.

Mutum zai iya tura sakone kawai alokacin da bai dace ba idana  abune da yashafi gaggawa wanda ya shafi rayuwan wani. Sannan kuma ka ka sake ka tura sakon da zai hana ko bata ma wani barcin shi.

 1. Fita da ga zaure da zarar an gana abin da aka bude domin shi.

Wannan shi ne abu da mutane da yawa ba su fahimta ba, lallai a na bude zaurukan ne na wani dan lokaci musamman wadanda ake bude su domin ganin an gudanar da wani gidauniya domin tallafawa wadansu jama’a ko kuma irin wanda dalibai za su bude domin ganin sun tattauna tsakaninsu. To da zarar makasudin da ya sanya aka bude wannan zauren ya kare sai kowa ya fita daga cikin wannan zaure, ma’ana sai a rufe wannan zauren domin dalilin bude shi ya riga ya kau. Idan kuma ana ganin cewar ya dace a ci gaba da yin magana akan wadansu bayanai to yana da kyau a sanar da mambobi ko kuma a rika haduna ta zahiri ba wai komai a yi shi a boye ba.

Categories
Software

Blackberry – Abubuwa guda 10 da mai amfani da ita ya kamata ya sani

An ce kasar Nigeria tana daga cikin kasashen da aka fi amfani da wayar hannu kirar Blackberry ba domin komai ba sai domin a farkon farawa mutane suna amfani da ita saboda isa da mallaka, wasu kuma suna amfani da ita saboda yin kuru da kuma neman ace ina da ita. Wasu kuma sun sayi wayar Blackberry ne domin kawai zamani da kuma abubuwan da ake amfani da su wanda ba kowace waya bace take bayar da irin tsarin shi yasa suka mallake ta. Amma duk da haka sai na lura matuka bayan tsawan lokaci da na mallaki wayar Blackberry kuma tana hannuna amma kuma ban san amfanin ta ba. Sai dai kawai in amsa waya ko in kira, ko kuma aika da sakon SMS da dai kuma daukan hoto. Wannan dalili yasa bayan na sami wani kanina yana da wayar blackberry ya fadamini abubuwa masu amfani wanda na ga ya dace a ce duk mai waya yayi amfani ya sansu.

1.      PIN lambarka da ke jikin Blackberry

Kowace Blackberry da muka ganta tana da wata lamba ta musamman wacce ta kebantu da ita wacce masu amfani da wayar suka sani da PIN Number. To, daya daga cikin abin da ya kamata mu sani cewar wannan lambar ta wayar blackberry da ke hannunka ne kawai kuma babu wayya da za a yi a canza ta. Koda kuwa ka canza wayar ko kuma ka canza SIM din ka to wancan PIN yana can waccan wayar.

Haka idan ka sayi sabuwar blackberry abu na farko da ya kamata ka sani shine mene ne PIN dinta, sannan kuma ya za a yi in gano lambar PIN dinta? Ya danganci wane irin Theme ka ke amfani da shi amma kusan ana samun inda za a ga PIN a wurin da aka rubutu Option a karkashin folda da ke fuskar blackberry ko kuma ka shiga setting sannan ka shiga personal Identification a nan ma zaka iya ganin lambar wayarka.

Wani abu da mafi yawa daga cikin masu amfani da blackberry ba su fahimta ba shi ne a duk lokacin da aika da sako ko da na mene ne to ka sani kana amfani da wannan PIN lambar ne, haka kuma koda kana browsing ko kana aikawa da email ne duk kana amfani da wannan lambar ne. koda yake ba dole bane ka san irin wannan bayanai amma kuma yana da matukar amfani ka san lambar blackberry na abokanka da kuma wadanda kuke yin hulda da su.

Idan ka san PIN number ta abokin ka to za ka iya aika mishi da sako kai tsaye ba tare da wani matsala ba. Duk lokacin da ka aikawa da wani mai blackberry sako ta hanyar yin amfani da PIN din shi to sakon yana zuwa cikin sauri da kuma hanzari. Sabanin email wanda idan ka aikawa da wani sakon imel dole sai imel din nan ya je zuwa ga kwamfutar wani sannan a aika da shi cikin akwai wanda ka aikawa da shi. Irin wannan hanya da ake amfani da ita ta wajen aikawa da sakon daga blackberry zuwa blackberry kamar yadda ake da “PIN Message” yafi kowane irin sako da mutum zai aika saurin isa. Shi yasa a duk lokacin da ka aika da irin wannan sako da zarar sakon ya isa zuwa wurin wanda aka aika zai sa harafin “D” a gefen makin da ke nuna cewar sakon ya isa. Wannan harafi na D shi ke nuna maka cewar wannan sakon ya isa kuma wanda aka aikawa ya ga sakon.

2.      Amfani da Setup Wizard lokacin farko

A lokacin da mutum ya sayi sabuwar Blackberry idan ya kunnan ta abu na farko da zai fito a jikinta shine Setup Wizard. Shi setup wizard wata hanya ce da aka tsarawa mai amfani da wayar blackberry domin  saukaka mishi wajen shirya yadda ya ke son yayi amfani da ita wayar. Amma mafi yawa daga cikin masu amfani da ita wannan wayar sai basu cika da muwa ba wajen su tsaya su cike tambayoyin da shi wannan Wizard din ya ke yi. Rashin tsayawa a cike wannan Wizard din na barin wadansu gurabu da ya kamata a ce ka ciresu ko kuma ka toshe su. Kamar duk lokacin da wayar Blackberry ta zo tana zuwa da yaruka da yawa da mutum baya bukatarsu. To idan a misalin kana son ka rika amfani da yaren turanci ne, to a lokacin da wannan wizard ya zo ya tambaye ka wani yare kake so ka zabi Turanci, to zai cire dukkanin ragowar yarukan da suke cikin wayar. Wannan ciresun da yayi zai taimakawa wayarka wajen rage mata nauyi da kuma kara maka girman ma’ajiyarka a cikinta.

Har ila yau a wurin shirya wayarka akwai abubuwa masu amfani da zaka koya kamar yadda zaka iya shige da fice a cikinta (Navigation) haka a wurin ne zaka iya shirya imel da kake son ka rika amfani da shi a ita wayar taka ta blackberry.

3.      Yi amfani da babban yatsa ba kumba ba

Daya daga cikin kuskuren da masu amfani da blackberry su ke yi shine wajen yin rubutu da maballan blackberry a lokacin da zaka samu mutum yana amfani da kumba wajen yin rubutu maimakon tafin babban danyatsa. Yadda aka tsara maballan da ke jikin blackberry an tsara su ne ta yadda komai fadin babban dan yatsa zai iya hawa kuma yayi rubutu ba tare da ka rubuta harafin da ba ka yi niya ba. Duk wanda ya ke kokarin kiyaye yin rubutu da tafin babban dan yatsar sa to zaka samu ya fi saurin yin rubutu. Amma yin amfani da tsinin dan yatsar ko kuma yin amfani kumba na kawo rashin sauri ga mai rubutu.s

4.      Rage bata lokacin wurin amfani da AutoText

AutoText daya ne daga cikin abubuwan da suke cikin blackberry wanda suke saukakawa wanda ya sani wajen yin rubutu. Domin AutoText shi wanda ya ke lura da mutum a lokacin da mutum ya ke yin rubutu a blackberry. A misali a duk lokacin da mutum ya ke son ya rubuta kalmar can sai yayi kuskure ya rubuta acn to AutoText zai canza ta kai tsaye zuwa can.

Haka shi AutoText yana karawa mutane saurin yin rutubu saboda yana cike wadansu alamomin da mutum ya ke bukatar sai yayi amfani da maballin alt kafin wannan alamar ta bayyana. A misalin idan mutum zai rubuta kalmar can’t dole sai ya latsa maballin alt sannan ya maballin k kafin alamar ta bayyana. Wannan yana kawo cikas wurin yin rubutu da kuma nawa. A blackberry duk lokacin da ka zo rubuta wata kalma wacce akwai alamar (apostrophe) a kanta ka rubuta shi ba tare da ka saka ba, da zarar ka bata maballin space zai saka maka wannan alamar.

Haka har ila yau akwai wadansu karin abubuwa da AutoText ya ke yi fiye da wancan da muka ambata. Domin akwai wadansu abubuwa da aka yi a blackberry wanda zasu kara maka sauri waje yin rubutu. A misali sai kana rubutawa wani sakon imel sai kana son ya kiraka a lambarka. To, idan ka tashi rubuta lambar taka a cikin wayar blackberry baka bukatar ka rubuta ta. Abinda ka ke bukata shine ka rubuta mynumber kana rubuta haka AutoText zai canza ya rubuta lambar wayarka a wurin. Haka idan kana son wani ya rubutawa wani lambar PIN dinka na blackberry to a wurin sakon zaka rubuta mypin kawai shi kuma zai cire ya mayar da lambar PIN din ka ne. sannan idan mutum ya son ka gaya mashi wane irin blackberry kake amfani da shi a halin yanzu kawai zaka rubuta mishi myver wannan zai canza ya fadi irin wacce kake amfani da ita.

Wadanann da muka ambata kamfanin da ya yi blackberry ne ya tsara su. To, kaima da ka samu wannan wayar zaka iya shiga cikin AutoText ka tsara abubuwan da kake son idan ka rubutasu ga yadda kake son fito. A misali sai ya kasance kana yawan amsa tambayoyin mutane amma kuma wani lokacin abubuwa su na cakude maka ya zaman to ba zaka samu damar bayar da amsa a nan take ba. To zaka iya shiga AutoText ka kirkiri wani rubutu da duka sanda ka rubutashi zai fadi kamar haka. Misali ka rubuta llll sai ka rubuta na sami sakon amma a halin yanzu ina cikin uzuru nan gaba kadan za a sami amsa. To duk sand aka rubuta IIII to zai sai canza zuwa ga wancan maganar. Wannan zai taimaka kwarai wajen yin rubutu da sauri.

5.      Karamar hanya wajen yin rubutu (shortcut)

Ana amfani da karamar hanya wajen yin rubutu a blackberry kodayake wannan karamar hanyar ba su da yawa, sai dai yana da kyau mai amfani da blackberry ya sansu domin ya samu saukin rubutu

 • Space bar: wanda ya danna space sau biyu zai sa mashi alamar tsayawa na (.) a lokacin da yake rubutu
 • Rike maballin harafi: wanda ya rike maballin harafi to harafin zai canza daga karamin rubutu zuwa babban rubutu.
 • Rubuta adireshi a internet: idan mutum yana rubuta adireshin wani gida dake internet idan ya gama rubutawa sai ya zo inda zai sa alamar tsayawa idan ya danna maballin space sau biyu zai sa mishi alamar tsayawa ta (.)
 • Rubutun adireshen imel: idan kana rubuta adireshen imel a blackberry inda zaka sa alamar @ to idan ka danna maballin space to zai saka maka wannan alamar idan kuwa ka sake danna maballin zai saka maka alamar tsayawa.

Amma mu sani cewar wannan yana aiki ne kawai a blackberry da kuma application dinta da wanda yayi application din ya bada wannan dama.

6.      Ka sayi memory card

Yana da kyau wanda yake da blackberry ya sayi memory card domin amfanin sa a jikinta yana da yawa. Kasancewar memory da take zuwa da shi ba yawa gare shi ba, ga shi kuma kusan wayoyi suna da tsarin baka damar da saka hotuna da kuma sauti da bidiyo a cikin su. Idan kace za ka yi amfani da wanda yake cikinta to zai kasance ya cika da wuri kuma idan ya kusa cika dukkanin tsofaffin kayayyakin da ka ajiye zasu rika sharewa da kan su.

Shi yasa ya ke da kyau ka sami memory koda dan karami ne ka saka mata domin yin hakan zai ba ka damar zubawa da kuma ajiyar isassun abubuwa a cikin ta.

7.      Kayi amfani da blackberry a matsayin wani ma’ajiya

Idan mutum ya hada wayar sa ta blackberry ta USB da kwamfutarsa to abu na farko da zai fito shine ya tambayeshi ko yana son yayi amfani da blackberry a matsayin wurin ajiya?. To idan mutum ya zabi e to blackberry zata bayyanar da kwakwalwar da take ajiyar abubuwan ka ta hanyar bude wani drive. Idan hakan ya faru zai baka damar da zaka iya dauko kaya kai tsaye da kwamfutar zuwa memory na wayar ko kuma daga wayar zuwa computer ba tare da wani wahala ba. Sannan kuma ta wannan hanyar zai baka damar ka iya diban abubuwan masu mahimmanci daga kwamfutar zuwa wata kwamfutar.

8.      Ka saukar da  software na blackberry (Blackberry Desktop Software)

Zaka iya yin amfani da blackberry ba tare da wani software da zai taimaka maka ba kuma babu matsala. Amma amfanin wannan Blackberry Desktop Software yana da amfani matuka musamma ga wanda yake son yayi wadansu abubuwa da suka shafi amfani da bayarsa a matsayin hanyar samun internet ga kwamfutarsa. Domin kamar wanda ya sami damar shiga internet a wayarsa to zai iya mayar da wayar ta koma a matsayin abin shigarsa internet (modem). Yadda idan kana son ka yi browsing a kwanfutarka ba sai ka nemi wani modem ba, to wannan software zai baka damar mayar da wayarka a matsayin modem sannan kuma ka iya shiga internet ba yi browsing kamar yadda kake yi da wayarka.

Haka ana amfani da wannan software wajen sakawa ita wayar sauti da bidiyo wanda a lokacin daya daga cikin amfanin da yake da shi shine yana iya canza maka tsarin bidiyon ko saution zuwa wani tsari na daban da blackberry. Haka zai baka damar ka ajiye dukkan abubuwan da ya ke cikin wayarka zuwa cikin kwamfutarka. Tun daga sunayen cikin layin wayarka, da wanda yake cikin kan wayar, da sakwannin SMS da ka samu dama dukkan wadansu abubuwa da suke kan wayar taka. Wanda daga baya idan wayar ta lalace ko ta bace zaka koma kan wannan application ka saukar da su.

Haka da wannan software zata iya dubawa ka ga ko kamfanin blackberry sun sake sakin wani sabon Operating System domin ya baka damar ya canza. Domin mafi yawan lokaci kanfanonin waya sukan canza manhajan wayarsu to, da wannan software kawai zaka iya mayar da ita blackberry ta samu sabon manhaji.

9.      Zubawa blackberry software masu amfani

Akwai wadansu software ko kuma application masu amfani da mai blackberry ya kamata ya saka su a cikin wayarsa wadannan application suna da yawa wadansu kyauta ne wadansu kuma na kudi ne. da farko dai idan kana son ka shiga gidan da ake samun irin wadannan application da suke amfani a wayoyin blackberry dole sai ka shiga gidan ajiyar application na su wanda ake kira da App World.

Da zarar ka bude menu dinka zaka ga hoton da yake wakiltar app world wanda da zarar ka taba shi zai bude maka babban shafin nasu. Idan ka shiga zai nuna maga wadansu dakuna kamar guda biyar wanda suka hada da dakin

 • Games a wannan dakin ake samu application na wasanni
 • Apps wannan daki ne da ake samun application kawai
 • Theme wannan daki ne da ake samu themes (riguna) da zaka iya canzawa blackberry dinka.
 • My World idan ka shiga wannan dakin shi kuma zai nuna maka dukkanin application da ka riga ka sakasu a cikin wayarka
 • My Account shine dakinka da zaka iya sharia yadda zaka sarrafa yadda zaka rika biyan kamfanin blackberry kudi a lokacin da ka ga application na saidawa kuma kana son ka siya

10. Mayar da Blackberry ta koma taka

Hakika mutum zai iya mayar da Blackberry din shi ta zama kamar tashi, an baka dama kamar kowace irin waya a blackberry shima zaka iya canza theme da yadda kake son ka ga wayar ta zama yadda kake bukata. Kamar canza sautin kira da sautin shigar sakon SMS da wani irin launi kake son idan an aiko maka da sako ya nuna maka ko kuma ya kake son idan ka bude Bluetooth wani irin launi kake so, da dai makamantansu.

Categories
Software

REMINDER APPLICATAION! Amfaninsa ya fi a wurin Musulmi

Rubutawa: Adamu Abdullahi AAADAM36

A cikin wayar hannu da computer akwai wani abu mai amfani ga mutane mai suna Reminder musamma ma Musulmi wajen tabbatar da kai a cikin sahun da addini yake buƙata. Da kuma fitar da kai daga abin da Allah da Manzonsa suka bayyana a matsa yin munafunci. Malam Bature ya ƙirƙiri reminder ne don tunatar da ‘yan uwansa wasu abubuwa na rayuwa, amma kuma amfanin reminder ga Musulmi ya fi masa amfani.

Duba da yadda Allah Ya faɗa da kanSa cewa “KU CIKA ALƘAWARI. DOMIN LALLE SHI ALƘAWARI ABIN TAMBAYAWA NE” (Isra’ 17:34).

Cikin hikimar Allah, Ya kawo mana wannan abu mai amfani don tabbatar da alƙawari da sauran uzirori na rayuwa.

AMFANIN REMINDER A WAYA

·               Yana taimaka wa wajen cika alƙawari tsa kanin al’umma.

·               Yana tabbatar da kamalar mutum ta cika alƙwari.

·               Yana haɗa kan al’umma ta wajen halattar taro.

·               Yana tunatar da mutum ƙananun ayyuka da sauran su.

SIFFOFIN REMINDER

·               Yana ɗauke da kwanan wata,

·               Yana ɗauke da watanni goma sha biyu, da kwanakin cikin mako,

·               Yana ɗauke da lokaci da kalanda dan tabbatar da lokaci

·               Yana ɗauke da setin ƙararrawa

·               Yana ɗauke da wurin rubuta abin da yake ranka na daga abin da za ka yi.

YADDA AKE SETA REMINDER

Ana seta reminder ta hanyar zaɓar rana da lokaci da wata da kuma suna abin da za ka yi ko za ka je a wannan lokacin. Wanda da zarar lokacinsa ya yi na bugawa da kansa zai aiwatar da abin da aka umarceshi, ya yi.  Yana ɗauke da ƙararrawa (alarm) da sunan abin da za ka aiwatar a kan waya ko computer. Yana tuni kafin lokacinsa ya cika ta hanyar ƙararrawa.

Categories
Software

YAYA AKE YIN FILASHING NA WAYA?

Da za ka tara masu amfani da waya, ka tambaye su mene ne filashing? Za su gaya maka cewar filashing shi ne idan wayarka ta sami matsala a kai ta wajen gyara a gyarata. To haka abin yake a ilmance ko ba haka ba?

A nan kasar tamu ta Najeriya idan ka ce a yi maka filashing ko ka ce wayar ka ta sami matsalar OS nata, kana ganin masana suna hada ta da wata ‘yar bakar waya, su kuma hada ta da Computer, sannan su kuma yi wasu ‘yan siddabaru, sannan su baka ita ka gani ta dawo dai dai kamar babu abin da ya taba samunta.

To Me Ake Nufi Da Filashing Na Waya?

Gaskiya mu a Najeriya da kuma sauran makwabtamu da ke Afirka za ka samu bamu da tsari irin tsarin da sauran kasahen da suka ci gaba su keyi, a kasa irin su America ko England irin su Saudi Arabiya da dai makamantansu suna da wani tsari da, za ka sayi waya ne da kuma layi a hade . Amma kuma filashing shi ne ka canza tsarin da waya ta zo da shi na amfani da  service zuwa amfani da wani service.

ABIN DA SAUKI?

Yi wa waya Flashing ba wai  abu ba ne da kawai za ka shiga nan take domin ka karanta mukala kawai ka ce za ka yi, Kana bukatar akalla a ce kasan computer a dan mataki na tsakiya, misali kamar ka san yadda ake daura program ko kuma kasan yadda ake cireshi, kuma a kalla ka san yadda ake shiga a gano wane driver ne babu a jikin computer kuma za ka iya yin wasu abubuwa fiye da haka.

Saboda yi wa waya filashing yana da nasaba da misalai dana kawo, domin dai dole farko ka yi amfani da program na musamman da ake yiwa waya Flashing sannan kuma a ce kana da wayar da ake kira da USB. Na san mai karatu zai iya cewa wadannan abu guda biyar kacal mutum zai yi amfani da su wajen yin Flashing, wannan haka yake akwai program masu matukar yawa a internet wanda za ka iya saukar da su ana’urarka kuma su taimaka maka wajen yin Flashing din wayarka.

Saboda haka duk wanda yake da ilmin computer, kuma yana da program na Flashing sannan kuma yana da USB Cable lallai zai iya yin Flashing na waya. Da farko, sai ka fara saukar da shi program din idan baka da shi a computer ka, ko kuma ka yi amfani da program na YOUR CELLULAR daga http://www.yourcellular.net/need help.htm Idan ka rubuta wannan adreshin internet  zai kai ka zuwa ga shafin da za ka saukar da wannan program din da zai baka damar ka yi Flashing na waya.

Da zarar File din ya sauko za a gan shi a zuge zai zo (zipped) sai a warware shi, idan kabi wannan tsari da za mu nuna maka tare da bidiyo da zamu saka nan gaba kadan za ka iya Flashing din waya cikin mintina ashirin (20).

Daga cikin abin da ya kamata da take tsaro CDMA wanda bayanin sa zai zo nan gaba.

ME ZAN BUKATA DOMIN INYI FLASHING DIN WAYATA?

1.            Software na Flashing (wanda za ka sauko da shi daga internet).

2.            USB cable wanda za ka hada wayarka da computer domin yin Flashing.

3.            Computer wacce take da a kalla OS Windows 2000 zuwa sama sannan ta zamanto tare da USB port a jikinta sannan kuma ya zama tana da akalla 256 RAM, da kuma saurin 800Mhtz.

4.            Ya zama CDMA ce.

SHI NETWORK DIN ME YE AMFANIN SHI A FLASHING NA WAYA

Dangane da abubuwan da muka lissafa a baya na abubuwa guda hudu da ake bukatar ka mallaka kafin ka iya yin Flashing na waya sannan kuma dole ne ya zamanto kana da account tare da daya daga cikin Alaro guda biyu wadanda ake amfani da su a harkar sadarwar waya. Idan kuwa baka da su kana bukatar ka yi rajista da su don samun wannan dama. Wadannan manya manya alaro (carrier) da na fadi guda biyu cewar su suke bada network na waya, su ne: Global System For Mobile Communication (GSM), su ne kamar AT&T da T-mobile. Sannan Alaro na biyun su ne CDMA ko kuma ka ce Code Division Multiple Access, misalinsu shi ne Quest da Metro da Sprint da kuma Verizon. wadannan su ne tsari da ake da su na harkar sadarwa na Wayar-Tafi-Da-Gidanka, wanda wayar ka in ba GSM bace to dole ta zama CDMA wanda so da yawa ba mai iya banbancewa tsakanin su.

Saboda haka wadannan su ne hanyoyin fasaha da ake da su guda biyar wadanda suke bayar da dama a samu network a wayoyin tafi da gidanka kodayake a yanzu ana samun wayoyi masu karbar network  biyu a lokaci guda.

Wannan shi ne a takaice abin da ake nufi da Flashing na Wayar-Tafi-Da-Gidanka a ilmance. ta daga wani tsari na kamfani. Misali a ce ka sayi wayar MTN wadda dole sai da layin MTN ko kuma bata ma zo da shi ba kawai tana karbar service dinta kai tsaye daga MTN, sai aka wayi gari kana son ka yi amfani da wannan wayar amma kuma ba tare da ka canza waya ba, shi ne sai ka bi wannan tsarin, wanda idan ka je ka saukar da program da ake Flashing din waya ko dai GSM ce ko CDMA ce to za ka samu cewar idan ka sauko da file din akwai bayani dalla-dalla da zai nuna maka hanyar da za ka bi ka canza wayar ka ta koma tana amfani da kowane layin waya, ko kuma kowane irin service wanda a najeriyance ake kiran shi da cracking wanda a ilimi na computer ake kiran shi da  Flashing. Zamu dakata a nan tukunna kafin fitowar mujallarmu ta gaba idan mai kowa da komai ya kai mu lokacin, za mu ji yadda ake yin Flashing a Najeriya da kuma wasu ilmomi da suka shafi wayar tafi da gidan ka.