Categories
Laptop

Abubuwan la’akari wajen sayan sabuwar laptop

Salam. Wai shin, menene abubuwan la’akari in inason in sayi sabuwar laptop kuma wani brand yafi inganci? Not advert..lol.02 August 2011 at 16:36 Mustapha Adamu

Duniyar Computer Malam Mustapha Adam, akwai abu na farko da ake la’akari da shi a lokacin da mutum zai sayi kayan wuta ba ma dole sai computer ba, shine suna da inganci? idan aka zo ga maganar computer laptop kusan gaskiya campanoni da dama a wannan lokaci  suna matukar kokari wajen ganin sun wuce tsara, amma idan maganar wace irin laptop zaka ka siya saboda ingancinta to ya danganta da aljihunka domin kare da kudin shi ai zai sha lahaula. Idan kuwa ka zo siya ka duba mene ne girman processor dinsu, kuma mene ne girman RAM din su, mene ne kuma karfin batirin ta awa nawa take yi, domin a wannan lokacin karanci ka samu sabuwar laptop tana yin awa hudu da rabi cikakke kafin ta dauke, daga baya sai ka duba girman HARD DISK dinta, sannan kuma ka duba girman ta domin wata ta fiye kankanta wata kuma tafi girman da yawa ka duba matsakaiciya wacce ba zata baka wahala wajen dauka ba. sannan bayan ka biya ka lura da yi mata charging kafin fara amfani da ita domin rashin yi mata charging da farko yakan lalata batir, sannan kuma kada ka rinka saka mata program da ba zaka yi amfani da suba kuma ka guji saka games da video da baka san daka inda ta suke ba. Kuma tunda ka yi kokari ka saya laptop da kudi mai yawa to ka daure ka siya sabon antivirus daga company kaspersky ko kuma norton domin duniya anyi ittifaki babu wanda ya fisu defination na virus. A sha ruwa lafiya Allah ya karbi Azumin mu. 03 August at 14:36

Categories
Laptop Tambayoyi

NI SYSTEM DI NA BA SHI DA SAURI KUMA BAI DAUKAR DVD PLATES SAI WANDA YAGA DAMA

Yusuf Dauda  Ina yi wa Duniyar Computer godiya. Don Allah NI SYSTEM DI NA BASHI DA SAURI. KUMA BAI DAUKAR DVD PLATES SAI WANDA YAGA DAMA. Sa’an nan yana dadewa wajen booting. Ina amfani da Window 7 ne a hp6735s na gode

To gaskiya akwai matsala a computer domin wannan specification da ka fadi ya cancanci  Windows 7 ya hau ba matsala sannan ba za ta yi nauyi ba kodayake a ka’ida ana son computer da za a dora mata Windows 7 ta zama 2GB RAM ne karanci a kanta, amma gaskiya da ram da ke kan Kwamfutarka babu matsala, sannan matsalar rashin daukar DVD da Kwamfutarka take yi a wani lokaci, matsalace ta software kana bukatar ka yi amfani da software na musamman da aka yi su domin su rinka playing DVD suna da yawa a Internet wasu kyautane wasu kuma ba kyauta ba ne. Sannan kamar yadda ka ce tana dadewa wajen booting ina ganin ka duba cikin darasi da muka yi a kan hanyoyin da za ka bi ka warware matsalar rashin tashi computer da sauri, idan ka bi darasin,  Idan Allah ya taimaka za ka warware matsalar ba tare da ka kaita wajen mai gyaraba. idan kuwa kana da halin da za ka iya sayan Application na musamman da aka yisu domin cire irin wannan matsalar, bana baka shawara ka shiga internet ka yi searching domin za ka iya fadawa hannun ‘yan baranda. Akwai guda daya da za ka yi amfani da shi ana kiran shi da TUNEUP UTILITY SOFTWARE za ka iya downloading dinshi a http://www.tune-up.com/products/tuneup-utilities/ ka yi amfani downloading trail version na kwana talatin, ka yi installing ka yi running dinshi zai cire dukkan wani abu da yake hana na’urarka tashi kai tsaye.

Categories
Laptop Tambayoyi

Na Ga Wani NOTEBOOK Ne Kuma Ya Yi Mini Kyau, Sai Dai Kash Bashi Da CD/DVD ROM. Shin Akwai Yadda Zan Iya Hada Shi Da Dvd/Cd Room?

Kwarai da gaske malam Mustapha Adamu ai daman NOTEBOOK Computers an yi su ne domin yin karamin aiki da kuma ayyukan dalibai na makaranta wanda ya shafi rubutu da jotting, to amma babban abin da kowa yake korafi akanshi shi ne CD/DVD Room, wanda daman ita computer ba a yi mata muhallinshi ba. To amma wani hanzari ba guduba, dukkan wata computer da bata da dvd ko cd a jikin ta, ko kuma ya lalace, masu kere-keran kayan computer sun yi abin da ake kira da EXTERNAL PERIPERAL wato duk abin da ka gan shi tare da computer ana aiki da shi akwai irin shi wanda ake amfani da PORT ake jona shi, MISALI ita wannan NOTEBOOK irin ta  da bata zuwa da EXTERNAL CD/DVD amma ta yanzu idan sabuwace ka siya tana zuwa da shi, haka kuma ko da wacce ka gani ba ta zo da shi ba to za ka iya shiga kasuwa inda ake sayar da kayan computer ka ce kana bukatar EXTERNAL CD/DVD, amma fa yana da dan tsada domin shi ma tafi da gidan ka ne. za ka iya amfani da shi a kowace computer. Da fatan ka gamsu.