Categories
Facebook

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka. Hakan fa na faruwa cutarwar da kuma zayi zai iya shafarka ko abokanan huldarka ko kuma ‘yan uwanka da suke amfani da intanet bama facebook ba.

Inda tsoron yake, wani lokaci zaka samu wani yana amfani da shi wannan account din naka amma kuma kai ba ka ma sani ba. Wani lokaci kuma sai mutum ya tashi budewa sai kawai yaji ance an canza masa passoword ko kuma yaga sunansa ya canza daga nashi zuwa na wani.

Madalla da wadansu hanyoyi da mutum zai iya bi ya gane cewa wani yana amfani da shafinsa kuma da hanyar da zai iya bi domin ya dakatar da wannan mutumi amfani da shafinsa.

Yadda zaka gane idan anyi hacking account dinka.

Wani lokaci ana iya fahimtar anyi hacking accout din mutum ne ta hanyar ganin tallace-tallace na shiga shafukan abokan ka a facebook da sunan kaine kake yi musu wannan tallan, wanda a ciki kana basu shawara ko ma tursasawa da su sayi wannan abin da kake yin tallansu.

Account din facebook da aka yi hacking wani lokaci yakan yi amfani da email address din da suke cikin facebook dinka ya rika aikawa da wadansu sakwanni da baka sani ba.

Wani lokaci idan kaga an canza maka suna ko wani bayani a profile dinka ko imel dinka ko password to lallai wannan account na facebook ba naka bane wani ke da iko da shi.

Hanyar da zaka gane cewar wani yana amfani da facebook account dinka shine ta hanyar shiga security setting na facebook dinka

Ka shiga settings>security>where you’re Logged in sannan ka taba Edit zai fito maka da hoton bayanin na’urorin da suke amfani da facebook dinka. Idan kaga bakuwar waya to sai kayi blocking dinta.

Categories
Facebook

Manhajar Facebook da Facebook Lite: Wanne ya kamata in yi amfani da shi?

Ba kowa bane yake da damar samun internet mai karfi, ko kuma wayar da take da RAM 3GB ko kuma 4GB. Har ila yau mutane da yawa suna iya samun damar shiga internet da 2G network tare da anfani da karamar waya mai amfani da 1GB ko kuma 2GB RAM kawai.

Kasanya a ranka cewa mafi yawan kafanonin kimiya a duniya sun fara yin kananan manhajojin da zasu wakilci mafi yawan shahararrun mahajojin su, domin anfanin masu kananan wayoyi.

Duka manyan manhajoji kamar na Twitter da  Facebook da LinedIn da Google suna samar da kanan manhajoji domin wayoyi masu karancin girman RAM ko karfin internet wadanda ake kira da Lite apps ko Go apps a manhajojin Google.

A bangaran Facebook yana da  karamar manhaja wato (Lite app) wacce take wakiltar babbar manhajar da kuma karamar manhajar tura sakonni wato (messenger).

Ita wannan manhajar ta shigo hannun mutane ne a shekarar 2015 wanda aka takaitata ga kasashe kamar Bangaladash da Ingiya da Sirilanka da makamantansu. Amma yanzu harda kasashen masu girman tattalin arziki suna amfani da wannan manhajar kamar kasar Amurka da Faransa da Ingila. Haka ana samun wannan manhajar ta Facebook Lite a wayoyi kirar Android da wayoyin Apple wato iOS.

Saboda haka bari mu duba wadannan manhajojin guda biyu muga da me daya tafi daya sannan kuma wacce ya kamata kai me karatu yayi amfani da ita a wayarsa.

SHAN BATIRI DA CIN WURI

Babban banbanci dake tsakanin wannan manhajoji shine cin wuri da suke yi a cikin wayar mutum. Misali ita babbar Manhajar ta Facebook  tana da nauyin 58-50MB amma ita kuma Facebook Lite iya girman wurin da take ci shine 2MB.

Tunda girman 2MB wannan Lite take ci a waya wannan ya nuna cewar zata yi saukin girkewa a cikin wayarka kuma ba zata dibi wani yanki mai yawa ba na RAM din wayar haka zai taimaka wurin sarrafa wayar da sauri.

Shidan wannan Lite din baya cin batirin wayar idan aka hada da shi babban Manhajar ta Facebook.

GINI MAI SAUKIN SARRAFAWA

Tun daga kwankwalatin (icon) da ginin fuskar manhajar (User Interface) na su wadannan manhajoji na Facebook guda biyu kana ganin kana sun gamu sun banbanta.

Babban Facebook kwankwalatinsa yana zuwa da laurin shudi, shi kuwa Lite kwankwalatinsa yana zuwa da farin launi, sannan a wurin sunan ana rubuta Lite ne kawai ba wai Facebook Lite ba.

Shi Facebook Lite yana da kananan rubutu da maballai, ita wannan manhajar bata da tsarin motsi na Animation, babu hotuna masu nauyi, ba kuma abubuwan ado da ake samun a manhajar Facebook din ta asali.

SHAN DATAR INTANET

Bayan cewar shi Lite din na taimakawa wurin saukin cin RAM, an kuma gina shi wannan manhajar ta Facebook Lite domin ta iya yin aiki a wurin da babu sinadarin shiga intanet mai karfi kamar 2G.

Dalilin yin saurin shi saboda kamfanin Facebook sun cire dukkan wadansu hotuna da basu da muhimmancin a cikin manhaja, amma sun lura da wadansu kananan wadanda zasu karawa manhajar karfin shiga Intanet.

SAURIN BUDE ABU

Idan ana maganar saurin bude abu Lite baka hada shi da Manhajar Facebook ta asali, domin kamfanin yayi kokarin rage mata duk wani abu da zai sa ta yi nauyin budewa.

Duk da akwai wadansu tsare-tsare da idan kana son ka bude a cikin wannan karamar manhajar Facebook Lite yaka dan dauki lokaci kasancewar babu asalin sinadarin da ke sa wannan abun ya bude da sauri kamar yadda ake samun shi a cikin Manhajar Facebook ta asali.

Haka a wannan karamar Manhaja ta Lite ta rasa tarin sinadarin motsi mai kyau tsakanin bude shafi zuwa wani shafi a cikin manhajar (instant transition) wanda ake samun shi a cikin ita Manhajar ta asali.

WARWARE MANHAJA

Facebook Lite bashi da tarin nan na warware da bayyana sabon abubuwan da suka shigo a cikin wayarka. A babbar manhaja ta Facebook da zarar sabon abu ya shigo ita manhajar da kanta zata warware kanta ta zuko sababbin bayanai.

Amma ita Facebook Lite ba tada wannan tsari dole sai ka taba bata wani maballi da shi zai warware da kuma zuko bayanai sababbi.

MANHAJAR AIKAWA DA SAKO

Ba kamar yadda aka sani ba a shekarun baya da manhajar aikawa da sako (Facebook Messenger) take zuwa tare da Facebook App. Amma yanzu kowane yana zaman kansa ne.

Amma abin jin dadi shi Lite yana zuwa da likakkiyar manhajar aikawa da sako wacce baka bukatar ta musamman domin aikawa da sakonni.

Kodayake shi wannan manhajar ta messenger dake jikin Lite bashi da kayan aiki masu yawa kamar ba zaka iya kira da shi ba, babu stickers, da game. Amma dai yana aikawa da sako kuma zaka iya karbar sako kamar kowa.

AMFANI DA EMOJI

Duk da Facebook Lite yana bada damar amfani da reaction da stickers, abin mamaki shine wannan manhajar bata baka damar amfani da emojis.

TO WANNE ZAN YI AMFANI DA SHI?

Idan kana amfani da waya mai 1GB ko 2GB RAM ko kana garin da ba network mai karfi, to kayi amfani da Facebook Lite.

Amma idan kana amfani da waya mai baban RAM ko kana inda network yake da karfi sosai kayi amfani da babbar Manhaja Facebook.

Categories
Facebook

Facebook Me ‘Yan Jaridun Bogi

Daga cikin abin da ke ci mini tuwo a kwarya har ya shanye mini miya dangane da yaduwa da bunkasar dandalin sada zumunta, akwai yaduwar wata sabuwar kasuwar ‘yan jaridu, amma na bogi. Kasancewar fasahar Intanet na da wani gamammen tsari ne wanda kowane lokaci ka hau, za ka samu masu sauraronka, shi yasa wannan lamari yayi kamari sosai. Abin da nake nufi shi ne, a yanzu an samu wadanda ke amfani da Intanet wajen yada labaru da sunan wai su ma a matsayin “yan jarida” suke.

Da farko dai tukun, masu wannan aiki za ka samu basu da wani ofishi nasu na kansu inda idan kaje za ka same su. Sannan ba su da tsarin tace bayanai, ko labarum da suka samo (ko suka ci karo dasu a Intanet). A takaice dai ba su da abinda ake kira “Editorial Board,” wanda aikinsu ne tace duk wani labari da wani jami’insu ya kawo, kafin a watsa shi. Abin da zai baiwa mai karatu mamaki ma shi ne, mutum daya ne ko wasu gungun “gayu” ne ke farautar labaru su yada; ba tsari, ba kintsi, ba ka’ida.

Abu na biyu, za ka samu ba su da ginannen shafin gidan yanar sadarwa (Website) inda ta nan ne za ka iya sanin waye su. Abu na uku, ba su da wani kamfanin yada labaru mai rajista da hukuma. Abu na hudu, shafin da suke amfani dashi wajen aiwatar da aikin duk bai wuce shafin Facebook, ko Twitter ko wasu makamantansu.

Abu na biyar, wanda shi ne yafi hadari, za ka samu masu wannan aiki da sunan aikin jarida, galibinsu a Dandalin Sada Zumunta (Social Media) suke kalar labaru, wallahi. Da zarar wani yace anyi kaza a unguwarsu, sai suyi wuf su cafke labarin, su yada. Idan ya sanya hoto ma nan take za su dauki hoton, duk su yada. A wasu lokuta ma ba su jira sai abu ya faru, da zarar sunji jita-jita, sai kawai su yada a Facebook, musamman. Su ambaci sunan gari da unguwa, har da wasu sunaye na wasu mutane da suka ji a jita-jitar. Akwai wanda ya yada wani labari na bogi, bai faru ba, yace abin ya faru. Ya ambaci sunan gari da unguwa, abin mamaki, sai wani dan unguwar ya aika masa sako ta Inbox cewa shi fa a unguwar yake, amma ba abin da ya faru. Sai “dan jaridan” yace zai kara bincikawa. Can ya sake tuntubarsa, yaya? Sai yayi wuf yana ba da hakuri, wai kuskure aka samu.

Darasi:

1. Ba duk labarin da ka gani an yada da sunan wani kamfani mai kama da na aikin jarida ko kafar yada labaru za ka dauka a matsayin gaskiya ba, musamman idan ba kamfanin yada labaru bane sananne;

2. A kul ka kuskura ka rika yada (ta hanyar “sharing”) labaru daga ire-iren wadannan kafafe, ba tare da neman tabbaci ba. In kayi haka, za ka zama cikin masu yada karya, in har abin da suka yada karya ne;

3. A karshe, haramun ne mutum ya siffatu da siffar da bai cancanceta ba, don neman suna ko don neman duniya. Idan babu wanda ya gane, Allah ya sani, kuma duk abin da mutum ya mallaka ta wannan hanya zai zama ya ci haramun ne, kuma sai Allah ya titsiye shi ya biya a ranar kiyama.

Allah kiyashe mu tabewa, amin.

Categories
Facebook

HATTARA DA ABOKAN FACEBOOK DA BAKA SAN SU BA

Daga Malam Yasir Ramadan Gwale

Wani abu ya faru a wannan Makon da wani matashi a sanadiyar facebook. Yana da kyau mutane su dinga sanin hakikanin da su wa suke mu’amala a facebook kafin sakin jiki da mutum. Domin kuwa halin da ake ciki yanzu rashin aminci yayi yawa tsakanin wannan al’umma.

Wani matashi mai suna Salman ya hadu da wani a facebook har ta kai su ga yin magana a Inbox. Suna tattaunawa da wannan mutumin mai suna Micheal amma ba ainihin sunansa Micheal din ya rubuta a facebook ba, ya sa wani suna daban. Suna hira har dai shi Micheal yake tambayar Salman cewar me yake yi na neman kudi a matsayinsa na matashi? Salman yace ba abinda yake yi. Anan ne shi Micheal ya yiwa Salman alkawarin samar masa aiki anan Kano.

Bayan haka, shi Micheal yasha daukar hoton office da gida da mota yana turawa shi Salman yana bashi labarin irin rayuwar da yake ciki ta jin dadi. Wannan ta sanya shi Salman nuna zilama da kwadayi akan abinda Micheal ke nuna masa. Anan ne suka sanya lokacin da shi Salman zai zo Kano tunda yana zaune ne a jihar Adamawa. Salman yazo bisa romon bakan da Michel yayi masa cewar zai sama masa aikin yi a kamfanin da yake aiki.

Ranar Juma’a sai Salman yayi niyyar zuwa Kano, dan haka ya kira Micheal ya sanar masa cewar gashi nan zai Taho. Shi kuma ya amsa masa da cewar ba matsala Allah ya kawo shi lafiya. Da isowar Salman Kano da yamma ana dab da Magriba, sai ya kira Micheal yake gaya masa cewar gashi ya sauka a Kano. Anan ne shi kuma ya shaida masa cewar baya nan yana wajen aiki, amma zai sanya kan in yazo ya taho da shi zuwa masauki.

Salman na tsaye a tasha wajen karfe 7 na Yamma wani yazo ya same shi bayan da suka yi waya yayi masa kwatancen inda yake a tsaye. Yace masa shi kanin Micheal kuma yazo ne ya kaishi masauki, Salman ya bashi suna tafiya har cikin unguwar Sabon gari a Kano. A lokacin da suka shiga wani layi mara kwalta wanda kuma baya bullewa (close) sai shi Salman ya lura wasu mutum hudu na biye da su a baya, da ya fahimci lallai wadannan matsa bin su suke yi sai ya tsorata. Yayi nufin ya dawo da baya ya gudu, sai sukai masa ishara da cewar zasu yanka shi idan ya gudu.

Suka nuna masa wani gida suka ce ya shiga, suna shiga gida suka nuna masa wani daki suka ce ya shiga. Ya dan tsaya gardama sai daya ya hankadashi cikin dakin. Bayan da suka tura shi ciki sukai masa mugun duka, suka kwace masa wayoyin sa guda uku, suka kwace masa Agogo da Zobe da kuma kudin sa. Sannan suka tambaye shi Katin cire kudi na ATM yace bai zo da shi ba. Suka caje kayan sa basu ga katin cire kudi ba.

Daga nan suka sanya shi ya tube kayan sa tsirara suka dinga daukar hoton sa, sannan suka ce masa, sai ya sayi wannan hoton Video da suka dauke shi ko kuma su yada video din a Whatsapp da Facebook. Suka ce sai ya saya dubu 70000. Ya amince zai basu kudin, a lokacin da yake yana hannunsu duk abinda suka ce masa baya musantawa. Da suka gama haka, wajen 8:30 na dare sai suka riko shi wai ya hau mota ya koma ya kawo musu kudin video din.

Suka fito da shi suka ce masa idan ya kuskura yayi magana ko yayi wani motsi zasu illata shi, haka ya basu. Suna tafiya da shi suna ce masa bi nan bi can, har dai da Salman yaga sun zo inda Jama’ah suke, kawai sai yayi ta maza ya rumbaci daya daga cikin su suka fadi kasa yana ihun Jama’a ku taimake ni b’arawo ne. Ganin haka sauran suka gudu shi kuma yaci Nasarar damke dayan katamau. Nan ne fa jama’a aka taru ana tambayar me ya faru. Da yake mutanan wajen kabilu ne suna magana da shi yaron da Turanci, sai suka nemi su bawa shi Salman rashin gaskiya.

Nan ne fa, shi Salman yace wallahi ba zai sake shi ba sai an je wajen ‘yan sanda. Suka yi juyin duniya ya cika shi, amma Salman yace sai dai a gaban ‘yan sanda sannan zai cika shi. Haka kuwa aka yi, aka kira ‘yan sanda suka tafi da su. Ana zuwa caji ofis Salman yayi bayanin abinda ya faru, aka ci Nasarar kama dukkan wadannan matasa a daren, aka tsare su. Da yake a lokacin wajen 11:30 sai ‘yan sanda suka ce shi Salman yaje ya dawo da safe. Yace shi bai san kowa ba, suka ce masa ba wani wanda ya sani da zai iya zuwa ya tafi da shi.

Nan ne kawai shi Salman ya tuna cewar ya sanni. Kawai sai naji ‘yan sanda sun buga min waya, suka bani labarin abinda ya faru dan haka suke rokon nazo na tafi da Salman. To nima a zahiri ban san Salman din ba sani na hakika, domin a facebook kawai muke gaisuwa, kuma ko a facebook maganar mu bata wuce gaisuwa. Amma da yake naje Adamawa da Azumi Salman yazo har inda nake ya gaishe ni.

Ganin haka, na kira abokaina guda su uku na basu labari nace su rakani wajen ‘yan sandan. Bayan da muka je na gabatar da kaina a wajen ‘yan sanda sannan aka sake yi min bayanin ainihin abinda ya faru. Suka ce na tafi da shi Salman na dawo da shi da safe. Na karbi Salman na kaishi ya kwana. Anan ne nake yi masa fad’a, nace wanne irin hauka ne zai sashi haka kurum ya dauki kafa yaje wajen mutanan da bai san su ba.

Anan ne yake ce min, ai shi yaudarar sa sukai, domin hoton da suke sakawa a facebook ba nakasu bane, sannan sunan da suke amfani da shi shima ba ainihin sunansa bane. Sai daga baya ne ya gane wanda suke magana din ashe sunan sa Micheal. Alhamdulillah mun bi dukkan hanyoyin da suka kamata muka nemawa shi Salman hakkinsa. Dan haka, anan nake amfani da wannan damar wajen kira ga mutane lallai suyi taka tsantsan wajen sanin su waye zasu yi mu’amala da su.

Bayan haka, kuma tilas mutane su rage kwadayi da son banza. Domin a garin kwadayin abin da mutum yake tunanin zai samu zai jefa rayuwarsa cikin garari. Don shi Salman wanda suka yi masa wannan abu zasu iya yin Kidnapping dinsa ko ma su kashe shi, ba abinda ba zai faru ba. Dan haka, mutane ayi hattara.

Yasir Ramadan Gwale
04-09-2016

Malam Yasir Ramadan Gwale marubuci ne kuma mai kokarin wayar da kan al’umma akan al’amuran yau da kullum. Haifaffen garin Kano kuma mazaunin garin, zaku iya samun wasu daga cikin rubuce rubucansa a shafinsa na sada zumunci da ke facebook ko a shafinsa Blog Spot 

Categories
Facebook

Yadda ake goge account din mutumin da ya mutu a Facebook

Wannan lamari na barin account da mutumin da ya rasu a social network yana bai wa mutane da dama haushi da takaici, musamman waɗanda suke kusa da wanda ya mutu. A wani lokaci za ka ga mutane suna jingina (tagging) hotunan banza ko na batsa ga shi wannan mamaci, haka za ka samu duk shekara mutane su yi ta masa murnar cika shekara (birthday) amma alhali shi yana lahira, wasu waɗanda suka saba wasa da shi, idan suka yi magana da shi bai amsa ba su yi fushi ko zagi da dai makamantan su.

Muna yawan samun ƙorafe-ƙorafe a wurin jama’a musamman waɗanda suka damu da makomar ‘yan uwansu waɗanda suke da account a Facebook ko Twitter ga shi kuma Allah Ya yi musu mutuwa dangane da ya za a yi su iya goge wannan account domin yadda hankalinsu yake tashi duk lokacin da suka ga hoton shi ko kuma wani abu makamanci haka.

Wannan dalilin ne ya sa muka yi bincike muka gano ashe tun tsawon wancan lokacin da muke ganin haka tuni kamfanin Facebook suka fito da wani fom wanda shi ne kawai abin da kake buƙata domin goge irin wannan account ɗin.

A GYARA HALI KAFIN A MUTU.

Yana da kyau duk wanda yake karanta wannan takarda ya sani wata rana shi ne wanda mutuwa zata riske shi, kuma bai san wani lokaci ba ne, kuma bai san a wani hali ba ne. Yana da kyau mu riƙa tsaftace abubuwan da muke saka wa  social networks domin duk abin da ka saka yana nan kuma wani ya killace shi. Kuma da ni da ku duk mun san watan wata rana za a tambaye mu, kuma sai mun bayar da bahasi a kai.

Mutane da dama basa la’akari da cewar duk abin da na rubuta ko na saka a social network Allah Zai tambaye ni, idan na saka wata magana ta ƙarya wani ya yaɗa to zunubin yana kaina, haka idan na yaɗa abin da yake na alkairi ladan yana kaina. Mu guji yiwa mutane ƙazafi, saka hotunan da basu dace ba, da kuma yaɗa jita-jita da zarge-zarge domin waɗannan abubuwan suna da wahalar tuba kuma suna da wahalar kankarewa.

INA ZAN SAMI FOM DA ZAN CIKE

Shi wannan fom da za ka cike, yana da waɗansu ƙa’idoJi da ya kamata mutum ya sani, kuma aKwai abu mai muhimmanci da kowa ya kamata ya kiyaye.

Kamfanin Facebook basa la’akari da garinka ko kuma addinin ka, suna la’akari da addininsu da kuma al’adunsu, saboda haka abin da suke buƙata wurin cike fom ɗin shi ne takardar shaidar cewar wannan mutumin ya mutu wacce kotu ko Asibiti suka tabbatar da haka. Saboda haka kafin ka fara cike wannan fom sai ka je ka karɓi takardar shaidar cewar wane ya mutu, sannan ka yi scanning sai ka fara cike fom ɗin.

Za a iya buɗe wannan fom ɗin ta bin wannan link kamar haka https://www.Facebook.com/help/contact/228813257197480

Fom ɗin wanda da Turanci aka rubuta shi yana buƙatar ka amsa tambayoyi guda takwas (8) kafin ka aika shi wanda su kamfanin Facebook za su duba su gani sannan daga baya su goge shi wannan account ɗin.

TAMBAYOYIN DA AKA AMSA

 1. Cikakken Suna: A wannan ɓangare ana son kai da za ka cike wannan fom ɗin ka saka sunanka cikakke misalin Salisu Hassan
 2. Sunan wanda ya mutu: Shi kuma rami na biyu sai ka rubuta cikakken sunan wanda kake son a gogeaccount ɗinshi, namiji ne ko mace.
 3. Imel ɗin mamaci: a na son ka saka imel ɗin da kake tunanin cewar da shi wannan mamacin ya buɗeaccount, kodayake wannan imel ba dole ne ka san shi ba, kuma idan ma ba ka cike wannan ramin ba saboda rashin sani babu matsala, amma saka imel ɗin zai baiwa kamfanin sauƙi zaƙulo account ɗin kuma su goge shi.
 4. Link ɗin mamaci naFacebook: Duk mutumin da ya buɗe Facebook, suna bashi wanilink (hanya ko rariyar liƙau) da ita ce hanyar shiga shafin ka kai tsaye, kuma wannan hanya babu mai ita a Facebook sai kai. Misali nawa shine https://Facebook.com/salisuwebmaster duk mutumin da ya rubuta wannan link a jikin browser to zai kaishi shafi na Facebook kai tsaye. To idan ba ka san na wanda ya mutu ba, abin da za ka yi shi ne ka nemo shi a cikin abokanenka, sai ka taɓa sunan shi, zai kai ka kai tsaye cikin shafin sa, sai kayi amfani da browser ka kwafe link ɗin da ka gani sai ka saka a wannan ramin.
 5. Dangantar ka da mamaci: LallaiFacebook suna buƙatar su san dangantakar ka da wannan mamaci kafin su cire wannan shafi a gidansu. Saboda haka za ka zaɓi dangantakar ka, a cikin kashi uku da suke da shi.
  1. Iyalai mafi kusa: Kai ɗan uwansa ne, ko baban sa, ko matarsa ko kuma yayansa da dai makamanta su.
  2. Dangantakar jini: Kamar kaka, goggo, baffa, da kawu da dai makusanta na jini
  3. Abokantaka: Idan wanda ya rasu, abokinsa ne ko kuna aiki wuri guda ne ko kuma aji ɗaya kuka yi, ko kuma ma dai ka san cewar ya mutu ne, sai ka zaɓi nan.
 6. Me kake sonFacebook su yi da account ɗin: A nan Facebook suna son ka faɗa musu abin da kake son a yi maka da account ɗin domin ba goge shi kaɗai za su iya yi ba, a nan aƙwai abu guda huɗu (4) da za ka iya ba su dama su yi.
  1. A faɗa wa abokansa ya mutu: Wannan zaɓi ne da za ka baFacebook na su saka a cikin shafinsa cewar wane fa yanzu ba shi, ya mutu, kuma su saka alamar da kowa zai iya ganewa cewar yanzu da gaske babu shi.
  2. A gogeaccount ɗin sa: wannan shi ne ɓangaren da ya fi kyau a yi amfani da shi, domin zai ba Facebook dama su share dukkan abin da wannan mamacin ya saka a cikin Facebook, tun daga rubutunsa, likes da comments da sharing da hotuna da video da ya sa a Facebook, yadda ba shi suna ba su.
  3. Ina da buƙata ta musamman: idan kuwa aƙwai wani abu da kake buƙatarFacebooksu yi maka ba sharewa ba to sai ka zaɓi wannan ɓ
  4. Ina da tambaya: wannan kuma idan kana da tambaya da kake son kayi waFacebooksai ka zaɓi wannan ɓ
 7. Yaushe mamacin ya rasu?:A wannan ɓangare suna son ka zaɓi rana da wata da shekarar da ya mutu ka saka musu.
 8. Takardar shaidai mutuwarsa: A wannan wurin shi ne za ka sakawaFacebooktakardar shaida daga kotu ko asibitin da mutum ya mutu cewar wannan mutumin ya mutu, ko shaida da mutane gidansu cewar su suka ba ka izini cewar Facebook su cire shafinsa.
 9. Da zarar ka gama cikewa sai ka aika musu da wannan fom domin su duba su gani sannan su yi abin da ka ce kana so.

Ba kamar yadda mutane suke tsammani ba, zai ɗan ɗauki lokaci kafin kamfanin Facebook su waiwayi takardar, domin kamfanin da yake da mutane sama da biliyan ɗaya da rabi yana buƙatar lokaci kafin ya aiwatar da wani abu. Kai dai tun da ka aiki sai ka jira.

Kuma babu laifi idan mutane mabanbanta suka aika, misali a sami mutane da yawa su aika domin hakan zai sa Facebook su gane cewar wannan bawan Allah da gaske ne cewar ya mutu.

Muna rokon Allah Ya jiƙan waɗanda suka riga mu mutuwa da imani, Ya kyautata ƙarshenmu ya yafe mana kurakuranmu, ya amintar da mu baki ɗaya. Amin

Categories
Facebook

Bari ba Shegiya ba ce! Facebook ta amsa kiran ‘Yan Afirka

Bayan da aka kai harin ƙunar baƙin wake a ƙasar Faransa a ranar Juma’a 13/Nuwamba/2015 mutane da dama ba su ji daɗin yadda babban shafin sada zumuncin nan mai suna Facebook ya fito da wani tsari na canza hoton da ke wakiltar mutum zuwa tutar ƙasar Faransa.

Mutane daga kowane ɓangare na duniya sun nuna baƙin cikinsu dangane da wannan mummunan hari na ranar Juma’a sai dai a wani ɓangare kuma an samu ƙorafe-ƙorafen jama’a kasancewar kamfanin Facebook ya nema jama’ar duniya da su yi wa kasar faransar addu’o’in zaman lafiya.

Wannan kira da kuma neman jama’a su san hotunan su ya baƙanta wa mutane da dama rai musamman mutanen yankin Larabawa da kuma nahiyar Afirka, musamman saboda ganin irin zubar da jini da ake yi ba dare babu rana a yankunan amma kuma daidai da nuna wani abu yana faruwa wannan kamfani bai taɓa nunawa ba.

Hakan ya san wani shahararren marubuci mai kishin ƙasa Jafar Jafar ya rubuta zungureriyar wasiƙa zuwa ga Mark Zuckerberg wanda shi ne shugaban wannan kamfani yana mai nuna damuwarsa da ko in kula da bai nunawa ga jama’ar Afirka musamman idan aka dubi cewar mutane kusan sama da dubu goma sha takwas sun rasa rayukansu a hare-haren da ƙungiyar Boko Haram take kai wa a Arewacin Najeriya.

Ba ma Jafar da ya yi wannan rubutun ba kusan mutane sun yi amfani da wannan kiran da shi Mark Zuckerberg ya yi suna canza hotunan su zuwa hotunan ƙasarsu, kuma suka riƙa yin amfani da kalmar bai ɗaya (Harsh Tag) suna cewar ayi wa duniya baki ɗayanta addu’ar neman zaman lafiya.

SAFETY CHECK

Wannan shi ne tsarin da kamfanin facebook suka fito da shi a yau Labara 18/Nuwamba/2015 bayan da aka kai harin da ya hallaka mutane a ƙalla talatin a garin Adamawa.

Wannan tsari ne da yake bai wa duk wanda yake kusa da inda abin ya faru ya sanar da al’umma irin halin da yake ciki na yin mamakin cewar yana lafiya ko kuma shi babu abin da ya same shi.

Wannan ba ƙaramin ci gaba ba ne idan muka yi la’akari da irin ƙorafe-ƙorafen da jama’a suke yi na cewar ana nuna musu launin fata.

Duk da haka, wasu jama’a suna ganin cewar wannan fito da wannan tsari ba wani abin a zo a gani ba ne, domin har zuwa yanzu kamfanin bai dawo da tsarin da zai ba ka damar ka canza hotonka zuwa ga tutar Najeriya ba. A nasu ra’ayin, jama’a suna ganin idan dai ba nuna wariyar launin fata ba ya kamata a ce shi ma wancan tsarin na canza hoto yana aiki, kuma suna ganin kamar yadda ya yi magana a cikin shafinsa na a nema wa Faransa zaman lafiya, ba wai dawo da tsarin faɗin yanayin da mutum yake ciki za suyiba, magana zai yi.

Sai dai mu ce Allah Ya kyauta kuma ya gafarta wa waɗanda suka riga mu da imani amin.

Categories
Facebook Social Media Tambayoyi

Facebook dina yana da matsalar password ya zan yi in gyara shi.

Tare da fatan alkhairi don Allah ina son ku yi mini karin bayani a kan facebook  a inda ake sa address din email da password da neman abokai wai shin wani password ne za a sa na email ne ko na facebook?

To Malam Isa Abba Askira idan na fahimci tambayarka shi ne a wani lokaci idan mutum yana searching na Friends yana haduwa da irin wannan amma hakan ba komai ba ne sai domin tantancewa a kan ko mai amfani da wannan facebook shi ke da account din, ko kuma ba shi ba ne, amma dangane da password da kake gani a lokacin da kake searching friends sai ya ce ka saka email account yana nufi email dinka sannan kuma password na shi wancan email din yake nufi, domin idan ka ba facebook daman shiga email dinka za su duba contact dinka suka ga wasu abokanai kake hulda da su, idan suka same su sai su aika masu da sakon cewar kana da accout na facebook su yi hulda dakai ta facebook. ILLA IYAKA MUNA GODIYA da fatar ka gamsu.

Categories
Facebook Tambayoyi

An Yi Blocking Dina A Friend Request na Facebook yaya zanyi?

Don Allah ina so a gyaramin An Yi Blocking Dina A Friend Request ne kuma ance final block ne inda hali don Allah ina jira

Ana sanmun wannna matsala ne a lokacin da ka aika da freind request da yawa ba a amsaba, ko kuma ka aika wa wadansu wadanda suke hana mutane aika wa da request. Idan hakan ta faru, dole hakuri za ka yi zuwa tsawon lokacin da suka tsareka idan lokacin ya kai abin da za ka yi shi ne ka daina aika wa da sako wajen wanda baka sani ba. da fatar ka gamsu

Categories
Facebook Tambayoyi

Me Yake Kawo Blocking Na Facebook?

Assalamu alaikum Duniyar Computer me yake kawo blocking na facebook alhalin wanda ka Turawa request ka san shi, ba wanda baka sani ba ne?  

Kusan wannan matsala nima kaina na fuskance ta wanda ya kawo da farko aka kulle ni na kwana 3, bayan sun bude mini friend request na sake requesting aka sake kulleni na sati guda, da haka har aka kulleni na wata daya, a yanzu ina cikin warning na karshe ne.

Abinda kuma ke kawo shi shi ne idan ka Turawa mutumin da ya shirya cewar duk wanda ya aiko mashi da sakon friendship to sparm request ne, to, idan ka yi rashin dace ka aika wa da irin wadannan mutane har sau uku to za a yi tsammanin kana daga cikin masu damun mutane a facebook.

Wani dalili na biyu idan ka aika da request ya yi yawa kuma wadanda ka aika wa misali ka aika wa mutane 70 aka yi rashin sa’a 3 zuwa biyar ne kawai suka amsa, sannan kuma ka ci gaba da aika request, to sai facebook su dakatar da kai tura request.

Kuma irin wannan matsala anfi samunta idan ka aika da request ga ‘yan mata. Ayi hattara idan suka yi maka gargadi har sau hudu, na biyar za su dakatar da kai ne. Da fatar ka fahimta.