Categories
Daga Edita

Barka da zuwa Duniyar Computer mai DVD

Alhamdulliah! Muna miƙa godiya ga Allah maɗaukakin sarki da ya nuna mana wannan lokaci da muke sake gabatar muku da Mujallar Duniyar Computer kashi na uku wanda yake haɗe tare da DVD da aka saka mishi darussa har guda goma ko fiye da haka.

Mun ɗauki tsawon lokaci wannan mujalla bata fito ba kamar yadda muka yi alƙawuri saboda abubuwan da zamu iya kira na yadda al’amura suke tafiya da kuma yadda muka kasa gane kan zaren da zamu iya kamawa, amma In Sha Allah mun ɗauki wani irin mataki wanda zai taimaka na ganin muna iya fitowa koda sau hudu ne a shekara.

A cikin wannan mujallar mun yi kokarin kawo kashi saba’in da biyar cikin ɗari na abin da ke cikin DVD a rubuce a cikin ita mujallar. Saboda haka wanda yake riƙe da wannan mujallar lallai yana buƙatar wannan DVD domin akwai darussa da suke cikin DVD amma basu a rubuce a mujallar.

A cikin tsokaci da muke yi na musamman wannan karo mun yi gamsasshen bayanai ne a kan jagora kuma shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iƙamatus Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau mai taken Gajiyawar Ahlussunna Wajen Cin Gajiyar Shugabancin Sheikh Bala Lau.

A wannan fitowa mun kawo muku bayani mai tsawo kuma gamsasshe game da abin da ake kira SOFTWARE wanda a mujallarmu ta farko da ta biyu tayi bayanai gamsassu a kan abin da ya shafi Mece ce Computer da kuma Hardware. A wannan fitowa mun kawo darussa masu matuƙar muhimmanci a kowane fanni kamar Programming Language: Wanne ne ya kamata na fara koya a wannan darasi mun yi bayanai a kan yaren kwamfuta da ya kamata duk wanda yake da sha’awa ya manar da hankalinsa wurin koyonsu. Kamar yadda kodawane lokaci ake ƙorafi akan matsalar Idanu tare da Kwamfuta mun yi bayani akan Hanyoyi goma na magance matsalolin Idanu.

Daga cikin manyan mukalolinmu kuma wadanda suke cikin DVD akwai Kurakurai goma da Sabbain masu amfani da kwamfuta suke yi sannan kuma akwai Abubuwa bakwai da bai kamata yara na yi a Intanet ba. Mun yi cikakken bayani game da sabuwar Babbar Manhajar Kwamfuta data shigo kasuwa a karshen shekarar 2015, mai suna Windows 10: Abubuwa goma muhimmai da ya kamata kowa ya sani.

Idan muka tsallaka bangaren wayar tafi-da-gidanka wannan karon mun kawo muku darussa da kuka daɗe kuna tsumaya irin Yadda ake raba data/MB a layukan Najeriya. Sannan mun yi magana a kan Kurakurai goma da mutane suke yi a group chat.

Waɗannan kadan ne daga cikin abin da wannan mujalla ta ƙumsa. Da fatan Allah ya yi mana jagora amin.
Na gode.

Salisu Hassan
Babban Edita

Categories
Daga Edita

JAMB COMPUTER BASED TEST – Duniyar Computer

Cikin ikon Allah ganin yadda jama’a suke ta yin korafi a kan cewar su basa garin Kaduna ballantan su ci gajiyar wannan shirin da muke son fara gabatarwa na yadda mutum zai iya amfani da Computer domin ya amsa tambayoyin da za a yi mishi a jarabar Jamb mai zuwa.
 
Cikin kokarin da muka yi mun yi kokarin ganin mu shirya shafi na musamman wanda zai dauki tambayoyi da aka yi na jarabawar jamb da ta gabata kuma wadanda aka riga aka amsa su, mun shirya su kamar yadda Jamb take shirya nata jarabawar, haka mun tsara lokaci kamar yadda ya ke a can.
 
A halin yanzu zaku iya shiga cikin babban shafinmu na Duniyar Computer domin gwada wannan jarabawa wacce duk wanda ya gama zai iya ganin amsa da kuma shin daidai yayi ko kuma kuskure ne?
 
Idan kana son zaban jarabawar sai ka shiga www.duniyarcomputer.com sai ka duba daga sama zaka ga JAMB CBT sai ka taba domin zaban darasi. Amma a halin yanzu guda hudu muka gama shiryawa gasu kamar haka.
 
 
1) Domin Use of English taba wannan link din USE OF ENGLISH
 
2) Domin Mathematics taba wannan link din MATHEMATICS
 
3) Domin Physics taba wannan link din PHYSICS
 
4) Domin Chemistry taba wannan link din CHEMISTRY
 
Da fatan duk wanda yasan yana wajen garin Kaduna zai sanar da duk wani dalibi da yake kokarin rubuta jarabawar Jamb da ya shiga wannan shafi namu domin ga gwada.
 
Muna nan zamu sakar muku bidiyo na musamman na abubuwan da ya kamata mu kiyaye a lokacin da muke son rubuta jarabawa da kwamfuta.
 
Muna rokon Allah Ya baiwa dukkan dalibai sa’ar jarabawa, ya kara buda mana kwakwalanmu domin fahimtar ilimi cikin sauki ya sanya albarka cikin al’amuranmu.
 
Salisu Hassan Webmaster
Babban Edita
Mujallar Duniyar Computer
Categories
Daga Edita

PROGRAMING LANGUAGE WANE NE YA KAMATA NA FARA KOYA? – (1)

Mene ne Programing Language ?

Wani tsararren rubutu ne da ake yi domin kurman mashin, amma kuma ya sanya shi ya kasance mai ji kamar mai kunne.

Daga ina ya kamata ka fara?

Mene ne dalilin da ya sa ka ke son ka fara yin Programing Language ? Wannan ita tambayar da ya kamata ka fara yi wa kanka da kanka, kasancewar kowane Programing Language  akwai abin da ya ke yi, da kuma abin da ake iya yi da shi, da kuma irin mashin ɗin da ya ke iya sarrafawa, da kuma alaƙar da take tsakanin sa da sauran Programing Language da ake da su.

Programing Language nawa ne a duniya?

Programing Language suna da matuƙar yawa, tun daga wanda ake amfani da shi a cikin ƙananan na’urori da kuma manya, da waɗanda ake amfani da su a cikin gida da kuma ma’aikatu da kuma waɗanda ake amfani da su a harkokin mu na yau da kullum. Sai dai a cikin waɗannan Programing Language  ɗin akwai waɗanda suka sami karɓuwa akwai waɗanda ko sunan su ma ba mutane da yawa ba su san su ba.

A wannan muƙalar zamu ɗauki yaren Kwamfuta waɗanda su ka fi shahara guda tara (9) a wannan zamani, waɗanda kuma da su ne duniya ke taƙama kuma kusan duk wani abu da za ka gani a wannan lokaci idan dai na’ura ce, tun daga kayan wasan yara (games) da na’urorin da manya suke amfani da su kamar wayoyin tafi-da-gidanka, da ma manya da ƙananan manhajoji dukkaninsu ba sa wuce ɗaya daga cikin waɗannan Programing Language  ɗin.

Wadannan programming guda tara ne, waɗanda suka hada da

 • Python
 • JAVA
 • C
 • PHP
 • C++
 • JavaScript
 • C#
 • Ruby
 • Objective-C

Mene ne dalilin ya zai sa na koyi Programing Language ?

Akwai ra’ayin mabambanta ga masu koyon yaran kwamfuta. Waɗannan dalilai sun sha bambam, sai dai daga baya ra’ayin yana komawa ga mataki na karshe amma kuma dukkansu babu matsala ga wanda mutum ya ɗauka.

An tattara ra’ayoyin jama’a masu koyon Computer Programming har gida shida (6), ta hayar la’akari da ta ina mutum ya ɓullo da kuma ina yake son ya ɓulla a wannan harkar.

 • Ba su san dalilin da ya sa suke koyon programming
 • Domin amfani yara.
 • Domin jin daɗi da nishadantar wa
 • Yana da ra’ayin yin programming
 • Yana son ƙarawa kanshi sani a cikin Programing Language
 • Domin ya sami kudi.

A darasin mu na gaba za mu ɗauki kowane ɗaya daga cikin waɗannan ra’ayoyi mu bada shawara ingantacciya ga duk mutumin da yake son ya koyi programmig language cikin wadannan ra’ayoyi shida.

In Sha Allah.

Categories
Daga Edita

Zamu sami mabiya 200,000 a Shafinmu na Facebook – Zamu Warware Wadansu Dabaibayi

In Sha Allah muna sa rai gobe 22 ga watan Satumba 2015, zamu sami mabiya har kusan dubu dari biyu (200,000), a shafin sada zumunta na Facebook. Wannan zai sanya shafinmu zama daya daga cikin shafuka da zasu sami hatimin yarda a shafin facebook. Alhamdu Lillah!
Godiya ga Allahu Subhanahu Wata’ala da ya nuna mana wannan lokaci, da kuma daukaka mana wannan shafi da ya zama daya tamkar da dubu a wurin warwarewa al’umma matsalolinsu da ya jibinci harkar Computer, Waya da kuma Internet.

Muna mika godiyanmu ga dinbin mabiyanmu wadanda suke kokari kodawane lokaci wurin yada dukkan wani rubutu da muka yi a wannan shafi, ta hanyar yin sharing da likes da kuma yin comment. Gaskiya masu yin wannan aiki suna da matukar yawa, akwai wadanda sun fi shakara hudu suna yiwa wannan shafin hidima, da kuma wadanda su kuma a wannan lokaci suke kokarin yada mu. Dukkanin ku muna yi muku fatan Alkairi, da kuma fatan Allah Ya iya mana.

Muna mika sakon godiya ga babban marubucinmu, babban Shehi a fannin Addini kuma haziki, marubuci, mai bincike a harkokin mu na yau da kullum a fannin Kimiyya da Fahasar Kera-kere, wato Mal. Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq). Haka muna godiya ga Hajiya Salaha Wada Wali wacce ta zamo mana kallabi-tsakanin-rawuna, domin ita ce mace ta farko wacce take kokarin yin rubutu a fanni abin da ya shafi waya da matsalolinta. Adamu Abdullahi Kano wanda shima yana yin kokari matuka wurin yin bayanai akan a bubuwan da suka shafi waya da makamantansu.

Haka wannan shafi ba zai manta da irin su Mal. Tukur Kwaironga wanda shi ne babban malami wanda yake kokarin koyar da mu yadda ake motsa hoto da kwamfuta. Shima Mal. Salisu Ibrahim Kano wanda yake yi mana rubutu a kan kwamfutoci a cikin motoci da abin hawanmu. Haka ba zamu manta da irinsu Pro. Ibrahim Malumfasi, Bashir Bature, Muhammad Sulaiman, Muhammad Uba Bauchi, Al’amin Jibrin Hadison, Dahiru Saleh, Abubakar Sadiq Sodangi, Mal. Kamal Isah Kano, Balarabe Yusuf Babale Gajida da dai makamantansu.

Ba zamu manta da ambato jagororin wannan Mujalla ba irinsu, Mal. Abdullahi Haruna, Mal. Isiyaku Sani, Mal. Salisu Umar Salinga, Mal. Dalhatu Khalid, Alh. Nasiru Ibrahim Dan Sani, Mal. Magaji Galadima (Mai Tsidau Kano), Alh. Abubakar Abdullah Hassan (Optimum Trainers Limited), Mal. Tukur Mamu (Babban Edita Desert Herald).

Haka ba zamu manta da manyan Editocinmu ba, musamman babban Edita a bangaren Hausa, Mal. Zubairu Abdullahi Sada, da masu taimakamasa kamar su Mal. Bashir Hadi Ashara da Abdullahi Maikano.

Muna yi muku godiya, Allah Ya saka muku da alkairi ya kuma albarkaci iliminku, ya kuma biya bukata.

Daga karshe muna fata jama’a zaku ci gaba da yi mana hakuri a wuraren da muka kasa, ta dibin tambayoyin da muka kasa amsawa, da kuma alkawuran da muka yi saboda mutuntaka da ajizanci ba mu iya cikawa. Muna kuma fata zamu inganta ayyukanmu nan gaba In Sha Allah.

Nan bada jimawa ba, zamu fada muku wadansu sababbin canje-canje a babban shafin mu na Duniyar Computer, wadanda suka zamo mana dabaibayi a harkar duniyar computer, kuma mun san zaku ji dadin wannan canji.

Godiya muke yi Allah Ya bar zumunci.

Salisu Hassan (Webmaster)
Babban Edita
Mujallar Duniyar Computer

Categories
Daga Edita

Daga Teburin Edita – Mujalla Ta biyu

Mujallar Duniyar Computer fitowa ta biyu a cikin kundi na daya
Mujallar Duniyar Computer fitowa ta biyu a cikin kundi na daya

Da farko muna yi wa Allah maɗaukakin sarki da Ya nuna mana lokaci na biyu domin fitowar wannan mujalla ta mu ta Duniyar Computer, sannan muna bai wa sauran al’umma haƙuri na jinkiri mai tsawon gaske na rashin fitowar wannan mujalla kamar yadda muka faɗa a cikin manufofinmu.
Mun sami matsaloli a fitowarmu ta farko wanda ya sanya dole muka sake yin ɗammara domin ganin In Allah Ya yarda ba za a sake samun irin wannan matsalar ba.
Mutane da dama sun yaba matuƙa da yadda aka yi wannan mujalla ta farko, amma kamar yadda muka faɗi cewar Ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, to, mun sami ƙorafe-ƙorafe daga ɗimbin masoya da kuma shawarwari na yadda za a inganta ita wannan mujalla, kuma dukkanin shawarwarinku abin karɓa ne da dubawa.
Mun yi alƙawari da kuma faɗa wa al’umma cewar fitowar nan za ta fito tare da faifai amma kuma hakan bai yiwu ba, kasancewar rashin kammaluwar ingantaccen faya-fayen da za mu saki ya ƙara taimakawa wajen tsaikon fitowar wannan mujalla.
A cikin wannan fitowa kamar yadda muka sani cewar dukkan wani ilimi yana farawa ne daga matakin farko, a wannan fitowar mun saka muku muƙaloli na ilimi wanda dukkansu babu abin yadawa, kuma kowanne sashe abin lura ne. A waccan mujalla ta farko babban muƙalar mu ita ce “Mece ce Kwamfuta” wacce muka warware ilmoma masu yawa a kan haka. A wannan fitowar mun zakuɗa gaba sosai domin mun kawo muku cikakken ilimi a kan abin da ya shafi cikin ita kwamfutar mai taken “MENE NE SYSTEM UNIT?”. Haka akwai muƙalar da take biye da ita wanda suka yi kama sai dai ita kuma ta shafi abin da ake buƙatar mutum ya sani ne idan yana son ya san yadda zai haɗa kwamfuta da kansa mai taken “KOYI YADDA AKE HAɗA KWAMFUTA DA KANKA A AIKACE”. Sannan kuma har ila yau a wannan fitowar mun koyar da “ILIMIN SANIN YADDA AKE ƊORA OPERATING SYSTEM”. Ga kuma cikakken bayanin “Banbanci Tsakanin Adobe Reader da Adobe Acrobat”, sannan daga cikin karatuka masu sha’awa akwai “Yadda za ka kashe Kwamfuta ba tare da amfani da maɓallin kashe ta ba”. Wannan da waɗansu bayanai masu yawa duka a cikin wannan mujalla ta ‘Duniyar Computer’.
Idan muka dawo ta ɓangaren ‘Duniyar Waya’ akwai muƙaloli masu ban sha’awa da ilimantarwar da ya kamata duk mai amfani da wayoyin Blackberry da Android ya kamata su sani a cikin muƙala mai taken “Abubuwa 10 da mai amfani da wayar BlackBerry ya kamata ya sansu” Sannan da muƙala mai taken “Tambayoyi 7 da mai amfani da Android ya kamata ya san amsarsu”. Haka mun warware taƙaddamar da ke tsakanin masu rikicin wayoyin Symbian da Android “Me ya sa Wayoyin Android suka fi Wayoyin Symbian?
Haka idan muka koma ta ɓangaren ‘Duniyar Waya’ mun samu rubutu masu zurfi da kuma ilimi mai gamsarwa dangane da abin da ya shafi ilimin “MENE NE NETWORKING” wannan ilimi ne da ya ƙunshi dukkan abin da mutum yake buƙata ya sani domin ganin ya ƙulla alaƙa tsakanin kwamfutoci guda biyu ko fiye. Har ila yau a cikin wannan ɓangare mun koyar da “Yadda Shafukan Internet Suke yin aiki” sannan kuma mun yi bayanin “Yadda ake amfani da Dandalin Twitter”. “Intanet A Matakin Farko” darasi ne da duk wanda yake shiga intanet ya kamata ya sani domin cikakken bayani ne game da abubuwan da ke faruwa kafin ka iya buɗe shafi a cikin Intanet. Daga ƙarshe mun yi ƙarin bayani game da “Hanyoyi guda biyar da za ka iya kare kanka daga Keyloggers”.

A sha karatu lafiya, Allah ya ƙara fahimtar da mu, amin

Salisu Hassan (Webmaster)
Babban Edita

Categories
Daga Edita

Yadda Ake Ƙirƙirar FOLDER Da Kuma Amfanin Ta A Computer

Folder za a iya kiranshi da mazubi da ake tattara ko kuma ajiyar kayan computer waɗanda aka fi sani da ‘data’. Ita folder ta na daga cikin abubuwa masu mahimmanci a cikin computer, domin kusan da ita folder ake shirya dukkanin document na computer a shirya su kamar yadda ka san ake shirya kaya a file na ofis.

Ita folder kamar yadda muka faɗa kamar ma zubi ne, saboda haka, kusan ita kanta Kwamfutar an shisshirya komatsenta ne a cikin foldoji daban-daban. Haka kuma folder ta na iya shiga cikin wata folder, wa ta ma a cikin wata.

Kusan dukkanin application da suke cikin computer duk suna cikin folder ne a shirye. Shi ya sa kake iya ganin kayan computer suna ba ka sha’awa domin sun killace ne. Ɗauki misalin ofis ne babu drawer da za a iya ajiyar takardu, duk takardar da ta shigo wannan ofishin sai dai a ajiye ta a ƙasa, ko’ina takardu sun yi kaca-kaca a ciki. Na san ba sai an faɗama mai karatu ba cewar wannan ofishin komai kyanshi ba kintsattse ba ne. To, da waɗanda suka ƙirƙiri computer ba su yi tsarin folder ba to da wanda zai yi amfani da ita da bai san inda zai fara ba.

A misalin mutumin da yake amfani da computer kuma shi mai ɗaukar hoto ne, to waɗanda su ka ƙirƙiri Operating System sun tsara mashi a kan ya yi amfani da ‘My Picture Folder’ a cikin ita wannan folder zai kuma iya ƙirƙirar wata folder ya kira ta da misalin sunan shi, sannan kuma zai iya ƙirƙirar wata folder a cikin ita folder ya saka ma ta sunan hoton da ya ɗauka a misalin ya kira folder da BIKIN SALLAH, sannan ya zuba waɗannan hotuna a ciki. Yin haka ya tabbatar da cewar duk lokacin da ya zo neman hotunan da ya ɗauka da bikin salla to zai shiga my picture – folder mai sunansa – bikin sallah.

Haka wanda yake son ya zuwa karatu a cikin Kwamfutar shi, kamar yana son ya saka karatun tafsiri na Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da na Sheikh Abubakar Gumi da na Sheikh Jafar Adam to zai shiga cikin folder ‘my music’ daga nan sai ya ƙirƙiri wata folder ya saka ma ta suna Tafsir daga nan sai ya shiga cikin wannan folder ya ƙara ƙirƙirar wata ya saka mata sunan malamin farko. Misali Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi 2012 bayan ka gama sa ka sunan sai ka buɗe ta ka zuba karatun. To, duk lokacin da kake son ka ɗauko ko ka saurari karatun ɗaya daga cikin waɗancan malaman sai ka shiga my music – tafsir – Sheikh Abubakar Gumi 1982.

Haka rubuce-rubucen da mutane suke yi a cikin computer ko kuma abubuwan da ka ɗauko na karatu a intanet suma haka ake son ka shirya su daki-daki a cikin kowace folder ta na wakiltar document da suke cikin ta.

Yaya Ake Ƙirƙirar Folder

Ana iya ƙirƙirar folder ta wurare da dama a kuma kowane wuri a cikin computer sai dai yana da kyau duk lokacin da kake son ka ƙirƙiri folder to ka tabbatar wurin ba shi da alaƙa da wurin da ba a son a ajiye wani abu ‘reserve place’. Waɗannan wurare ne da waɗanda su ka yi Operating System ba sa son kowa ya saka wani abu domin saka wani abu a cikin wurin zai iya cin karo da wani tsari da zai hargitsa computer.

Wanda yake son ya ƙirƙiri folder a Desktop zai bi wannan hanyar >> Right Click a jikin sararin Desktop >> New >> Sai ka latsa Folder. Za ka ga ya kawo maka folder amma wurin sunanta ya sa ka ma ka suna ‘New Folder’ nan take sai ka rubuta sunan da kake buƙata, kamar ‘Salisu’s Files’. Sai ka danna ‘Enter Key’ da ke jikin ‘keyboard’ ko kuma ka latsa wani wuri a jikin Desktop ɗinka da ‘left click’.

Wannan shi ne hanyar da ake bi a ƙirƙiri folder a cikin computer kuma da wannan hanyar ce a kowane wuri ka ke son ka yi folder haka za ka yi. Wanda kuma ya yi kuskuren sa ka suna kuma yana son ya gyara sunan, to, zai je kan ita foldar ne ya yi right click a kanta sai ya taɓa rename sai ya gyara sunan sannan ya taɓba wani wuri na daban gafen folder ɗin.

Categories
Daga Edita

Hanyoyin Sanin Ciki da Wajen Computer

Kadan daga cikin abubuwan da ake samu a bayan na’ura mai Kwakwalwa, takaitaccen bayanin abubuwan da suke a bayan computer, da amfanin su da kuma yadda ake jona su.

 1. Wuri ne da aka saka wayar da zata aika da wutar lantarki daga jikin bango zuwa matatar wuta (Power Supply Unit)
 2. Ana amfani da wannan wuri domin sarrafa yanayin karfin wutar da ake son ta shigo cikin power supply, sau tari zaka samu an daidaita tsarin karfin wutar 230v amma idan kana irin kasar da wutar su bata kai haka ba zaka canza shi zuwa 110v.
 3. (Mai Sarrafa Wuta) wuri ne da ake sawa na’ura mai kwakwalwa wutar lantarki, shine abinda yake baiwa dukkanin abubuwan dake cikin uwar allo wuta (Motherboard), shike iya tace wutar da za’a baiwa dukkanin sauran kayan karafan dake bukatar wutar zuwa wutar da bazata lalatasu be, Kamar, CD/DVD Rom, Floppy Disk, Hard Disk da dai makamantansu. Kuma shi Power Supply yana da hakora uku wanda ake kira da three-pin connector. Haka wani lokaci a jikin shi Power Supply akan samu abinda ake kunnawa da kashewa (on/off), wanda yake taimakawa wajen kunnawa da kashe na’urar.
 4. Wadannan wurere ne da ake jona keyboard da mouse, babu wani abu da ake jonawa ta wurin sai su, kuma suma a na’urori na zamani an musanyasu da USB.
 5. ga al’ada ana amfani da shi wajan jona Printer, do yake shi parallel port bashi da saurin tafiya, ma’ana idan aka jona printer ta parallel port to sai an kashe na’urar an kunnata sannan ta fahimci cewar an samata printer, amma yanzu an musanya shi da usb port domin saurin hadawa da na’ura
 6. wannan shine ake hada monitor da CPU domin ganin abinda yake faruwa a cikin na’urar. Ana iya samun wurin a zaka jona TV wanda ake kira da S-Video.
 7. ETHERNET PORT:- kuma ana kiranshi da Network port, wannan wuri zai baka dama da hada na’urarka da sauran naurori ta hanyar internet ko network ko ya baka dammar hada naurarka da broadband modem ko router.
 8. kayi amfani da kananan ramuka nan wajen jona speakers da kuma microphone. Amma idan kai ma’abocin son amo ne (sound) ko kana amfani da kayan amo manya, tun daga manyan speakers, kayan kide-kide (instrumental), to kana bukatar karin sound card a naurar ka, domin Audio connectors basu da karfin da zasu dauki irin wadannan kayan amo.
 9. A wannan zamani mafiya yawan kayan na’ura mai kwakwalwa ana hadasu da na’urar ta USB wanda cikakken ma’anarshi tana nufin (Universal Serial Bus). Ana jona mafiya yawan kayan na’ura ta wannan wuri, kuma masana sunce a jikin USB guda daya, za’a iya jona kayan computer sama da 75, kamar su Printer da kamar su Scanner. Na’urorin computer na zamani suna da USB 2.0 wadanda suna da karfi wajen tafiyar da kowane irin kayan na’ura da sauri.
 10. Wannan shima wata mahadace mai tsananin sauri, firewire yana taimakawa wajen cire abida ke cikin wadansu na’urori wadanda ba computer bane, kamar kamara ta majigi, ko kamara ta daukar hoto mara fim, da kuma abin sauraron sauti na Mp3 (player). Idan na’urarka bata da firewire a jikinta zaka iya sayan devices masu USB ajikin su, amma dole ya zama saurin USP dake jikin devices ya zama saurin shi ya kai karfin tafiya ko saurin 2.0.
 11. Wannan itama mahadace ta na’ura wanda mutum kan iya jona wayan tangaraho ajikin na’ura. Idan mutum yana san samun mahada ta internet da abinda ake cewa dial-up internet wanda yake amfani ta wayar tangaraho, to ta wannan ramin ake hadawa.