Categories
Auto Mobile

An Kera Mota Mai Aiki Da Iska

Gaba daya motar da robar Lego aka kera ban da tayoyi.

An fara gwajin wata mota mai aiki da iska maimaikon man fetur ko gas, da ake kera da robar Lego a garin Melbourne na Australia inda take tafiyar kilomita 20 cikin sa’a guda.

Wani mutumin Australia ne ya kera motar tare da hadin gwiwar wani masanin kere-kere dan Romania wanda ya yi amfani da bulo na roba na wasa da ake kira Lego guda 500,000 wurin hada motar.

Motar ta na amfani ne da injina hudu dake aiki da iska.

Komai a jikin motar har da injinan an yi su ne da robobin Lego in ban da tayoyi.

Injin motar na aiki ne da iska maimakon mai ko gas

Dan Australia Steve Sammartino ya ce ta intanet ya hadu da Raul Oaida dan Romania wanda ya shaida ma sa kudirinsa na kera motar.

Ya kara da cewa ya shiga shirin ne saboda aniyarsa ta karfafawa matasa gwiwa a fagen fasahar kere-kere, sai dai kuma ba shi da kudin da zai dau nauyin aikin.

A kan haka ne ya aike da sakon twitter inda ya bukaci mutane 20 da za su sa jarin $500-$1,000 a harkar.

‘Yan Australia 40 ne suka aiko da kudinsu, abinda ya ba su damar fara aikin.

An nuna fasaha

Sai dai kera motar ya dauke su watanni 18 da kuma dimbin kudin da su ka zartar abinda suka samu da farko, in ji Sammartino.

Shi da Raul Oaida suka kera motar a Romania sannan suka aike da ita Australia inda nan ma suka sake yi mata garambawul.

Mr Sammartino ya shaidawa BBC cewa: ” Mun tukata a garin Melbourne. Injin ba shi da kwari tun da na roba ne don haka babu fargabarmu ita ce ka da ya yi bindiga ya tarwatse.”

Mataimakin editan mujallar motoci ta Autocar, Matt Saunders ya ce: “Kera wanann mota ba karamin aiki ba ne, balle a yi batun sa ta tayi tafiya. Musamman ma injin, lalle an nuna fasaha.”

“Sai dai ban ga alamar za ta yi dadin tukawa ba, kuma ba zan so in tuka ta da nisa ba. Ko kuma in yi karo da ita.”

Daga BBC Hausa

Categories
Auto Mobile Duniyar Waya Rahoto

Wayar salular da ruwa baya lalata wa

Kamfanin Sony ya samar da wayar salularsa wadda ruwa baya lalatawa.

Wayar samfurin Xperia Z na da wasu abubuwa da ba kowacce wayar salula ce ke da su ba.

An gabatar da wayar ne a wurin bikin baje kolin fasahar kere-kere na CES a birnin Las Vegas na Amurka wanda ake yi duk shekara.

Kamar kowacce shekara, abana ma manya da kananan kamfanonin kere-kere a duniya sun baje kayayyakin su.

Akwatunan talbijin da suka fi fito da hoto rangadadau su suka fi jan hankali a bikin baje kolin, inda wadanda suka kerasu ke baje sabon samfurin da suka samar.

Kamfanin Samsung dai ya fito da tasa talbijin din wadda ita ce ta fi sauran a duniya.

Sannan kamfanin samar da katunan wasa na nVidia ya kaddamar da wata na’urar wasa mara nauyi.

Na’urar na dauke da manhajar wayar salula mafi sauri a duniya.

Sai dai ana ganin kwamfiyutar hannu ta Razor Edge Pro, ce za ta yi gogayya da ita. Ita dai tana amfani ne da manhajar Windows 8, kuma wannan na’urar ta Joystick na bada damar yin wasa da ita.

Labari: Daga BBC Hausa

Categories
Auto Mobile

COMPUTER A MOTOCINMU: YAYA SUKE?

Computer na da matukar amfani a duniyarmu ta yau. A yau amfani da Computer ya wuce wurin rubuce rubuce da lissafe lissafe da kalle kalle da koyar da ilmi da dai sauran ayyuka da muka fi sanin na’urar da aikatawa.

Abin da yawancin mutane basu sani ba a yau shine; a na amfani da Computer a motocin da muke hawa domin zirga zirgarmu ta yau da kullum. Kusan duk motar da ka gani a wannan zamani ta dogara ne da wani nau’i na Computer wajen gudanarwar ta. Akan yi amfani da wannan na’ura a motocin ne ta hanyoyi da yawa kamar yadda bayanin su ke tafe

Na’ura mai kwakwalwa da ke aiki a jikin mota

Wadannan  Computer na aiki ne domin tabbatar da aikin mota ba tare da wata matsala ba, da kuma tabbatar da tsaron matuki, da ma sauran mutanen da ke cikin motar, tare da tsare muhalli daga gurbata. Cikin irin wadannan na’urori akwai masu sarrafa inji da masu sarrafa kofofin mota da hasken wuta da makullai da masu sarrafa gudun mota da masu sarrafa bangaren lantarkin mota da masu sarrafa aikin birki da dai sauransu.

Mafi mahimmanci cikin na’urori da ke jikin mota itace wacce ke sarrafa aikin injin motar. Wannan na’ura ta kunshi abinda ake kira ‘Engine Control Unit’ ko kuma ‘ECU’ a takaice, wadda yake shine kamar ‘Micro Processor ‘ a irin na’ura maikwakwalwa da muka fisani. Sannan kuma akwai sauran makarrabai da ke karbo sakonni daga sassa-sassan mota wadanda sune kamar ‘Input Devices’ a Computer da muka saba. Akwai kuma masu isarwa ko kuma aiwatar da sako wadanda su ne kamar ‘Output Devices’.

Masansana ko kuma ‘Sensors’ a turance

Masansana sune bangarorin da suke karbo sako daga jikin mota domin aikawa zuwa kwakwalwar computer  motar wato ‘ECU’. Misalan masansana sune: abin da ke sansano yanayin zafin inji da abin da ke sansano yanayin iskar da ke zuwa cikin inji da abin da ke sansano yanayin taka totir (throttle pedal) da direba ke yi da abin da ke sansano yanayin zafin ruwa da ke sanyaya mota da dai sauransu. masansana sune kamar ido da hanci ga injin mota.

 motar wato ‘ECU’. Misalan masansana sune: abin da ke sansano yanayin zafin inji da abin da ke sansano yanayin iskar da ke zuwa cikin inji da abin da ke sansano yanayin taka totir (throttle pedal) da direba ke yi da abin da ke sansano yanayin zafin ruwa da ke sanyaya mota da dai sauransu. masansana sune kamar ido da hanci ga injin mota.

daya daga cikin hanyoyin da za ka gano cewa wani daga cikin masansanan motarka baya aiki shine ta kamawar wata ja ko rawayan wuta a ‘Dashboard’ din motarka.

kwakwalwa ko ‘ECU’

‘ECU’ ne ke karbar sakonni daga masansana ya sarrafa sakonnin sannan ya aika da bayanin da ya dace ga bangaren da ya kamata. Alal misali, idan abin da ke sansano yanayin zafin inji ya aiko da sako cewa injin mota na da wani nau’i na zafi, ‘ECU’ zai aika da sako izuwa abin da ke fesa mai cikin inji domin ya fesa yanayin man da ya dace da wannan nau’in zafin. Wani misalin kuma shine, idan abin da ke sansano yanayin yadda direba ya taka totir ya aiko da sako izuwa ga ‘ECU’ akan cewa direba ya taka totir din sosai to ‘ECU’ din zai aika da sako izuwa ga abin da ke fesa mai da sauran wuraren da suka kamata domin bada mai da karfin wutar lantarki da ya kamata ga injin motar. Aikin wannan na’ura kan sanya injin mota ya yi aiki sosai ba tare da wata matsalaba.

Aikin Computer ga yadda injin mota ke aiki na da matukar mahimmanci. Ta na taimakawa sosai wajen rage shan mai a mota da kuma kare muhalli daga gurbata, ta hanyar rage yawan hayakin da mota ka iya fitarwa.

Na’ura mai kwakwalwa da ake aiki da ita don gyaran mota

Shigo da Computer cikin  mota ya sanya dole ake amfani da ita na’urar wurin gyaran motar. A yanzu akan yi amfani da Computer wurin gano matsala a mota, kai, wani lokacin ma harda a wurin gyaran motar. Kyera ita motar ko, a yanzu ba ya yiwu dole sai da injina da na’ura mai kwakwalwar ke sarrafawa.

Akwai motoci da dama a wannan zamani wadanda baya yiwuwa a gano mai ke damunsu sai an yi amfani da Computer. Wannan ke nuna cewa akwai alamun kanikanci nan gaba zai gagari da yawa daga cikin kanikawanmu na yau, sai dai in har sun nemi ilmin Computer.

Ana amfani da wata na’ura da ake kira ‘OBD Machine’ wato ‘Onboard Diagnostic Machine’ wadda akan jona a wani bangare na mota sannan a jona ita na’urar a jikin na’ura maikwakwalwa. Ita na’urar za ta gano matsalar da ke damun mota sannan ta fito da abin da ta gano a fuska ko kuma ‘screen’ din na’ura mai kwakwalwar da aka yi amfani da ita.

Na’ura mai kwakwalwa da ake amfani da ita don ganowa da kuma sarrafa mota akan hanya

Wani amfani kuma da za a iya yi da Computer a mota shine wurin sarrafa motar daga nesa, ma’ana sarrafa ita motar ba tare da mutum yana cikinta ba. Wannan fasaha kan ba ma mutum damar sanin yadda wani ke sarrafa motarsa daga wata uwaduniya. Ta yin amfani da wannan fasaha mutum zai iya gano wurin da wata mota da aka sata ta ke inhar motar na dauke da na’urar da mu ke magana akai. Kuma za a iya amfani da wannan fasaha wajen kashe injin motar ko kum kulle kofofinta ko kum kunna amsa kuwar tsaron motar. Wannan na’ura kuma kan taimakama mutum sanin wurin da motarsa ta ke daga wata uwaduniya.

Akan yi amfani da wata fasaha da ake kira GPS wajen cinma wannan buri. Ana amfani da wata na’ura ne da akan makala a jikin mota wadda ita na’urar kan aika da sako ga wata Computer wadda ita kuma kan shigar da sakon cikin yanar gizo ta inda shi kuma wanda ke son yin wani abu ga motar zai shiga yanar gizon ta yin amfanida na’urarsa mai kwakwalwa wajen cimma burinsa.