BUHARI MARAYA NE – Mu Ne komai na shi

Dama ce muka samu ta samun canji na Shugaba wanda ba azzalumi ba. Ba barawo ba. Ba matsafi ba. Ba mashayin giya ba. Ba almubazzari ba. Ba jahili ba. Ba mazinaci ba. Ba kasasshe ba.

Ga shi kuma yana zagaye da kuraye, ɓeraye, karnuka, Aladu, macizai, angulu, kunamu amma na jama’a masu irin halayen waɗannan dabbobi.

Mu saka shi cikin addu’oinmu mu ta yau da kullum, masu yin azumi su buɗe baki da yi mishi Addu’a, na kan hanya su haɗa da shi, masu ayyuka na ƙwarai su haɗa da shi masu ziyayar marasa lafiya mu haɗa da shi dukkan mu mu cigaba da yi mishi addu’a.

Kada mu bada kafar da wasu za su riƙa ci mishi dudduge, ta hanyar bata shi da rubutu a jaridu, mujallu, internet da dai makamantansu. Mu riƙa bashi uzuri, mu gode kaɗan na canji daga wurin sa, mu yaba ƙoƙarin sa, mu kyautata masa, mu karbi shawarwarin sa.

Haka waɗancan suka yi wa nasu, to yau abin ya dawo wurinmu, namu ya samu.

Wannan ita ce gata da za mu bai wa wannan marayan Shugaba na mu domin barinshi shi kaɗai a cikin komai da rashin taimaka masa tamkar ihune bayan hari.

A bari ya huce shike kawo rabon wani, mun dai ga ƙarfin addu’a kuma mun ga yadda take matse bakin mutane masu ƙarfi su koma marasa ƙarfi.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *