Bude mini Windows

Wani yaro ne yake aiki a Business Center sai wani mutum ya ga yadda yake yin aiki ya burgeshi shine yace zai kai shi wani kamfani a dauke shi aiki. Bayan lokacin yi mishi interview yaro ya dau wanka ya shiga wajen Interview, aka tambaye shi kasan computer, yace sosai sosai, ake ce bude windows. Yaron kawai sai ya tashi ya kama bude wundinan ofis din. Idan kaine ya zaka yi?

Related Articles

Mene Modem ya kuma ake amfani da shi?

Modem dai kamar yadda mu ka sani wani dan ƙaramn device da ake amfani da shi wajen haɗa computer da internet, da farko dai modem kala biyu suka fi shahara a Nigeria akwai Huawei da ZTE duk waɗannan modem ɗin ana kiransu da plug and play wato da zarar ka saka su a cikin computer zasu yi installing kansu, kuma su fara aiki kamar yadda aka tsara.

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. Ah ah, wai meye ne na kwafsi anan, ai cewa akai ya bude windows. wannan ai tambaya mai harshen damo. dama cewa sukai ya budo masu windows (BUDO MANA WINDOWS), anan kowa na iya fahimtar cewa na komfuta ake nufi. Amma Yaron really knows what he’s doing, ba laifin shi bane. Loooool

  2. Mhn! Wannan ai laifin masu ganawa da shi ne wato (interviewers), da ba su fayyace masa wanne windows ba. Saboda haka don ya yi haka ba lefi ba ne a ganina amma a juri zuwa rafi…

  3. To, ka san yanzu mutane da yawa za su iya ‘operating’ comfuta ba tare da karatun ta ba. Kamar yadda muke da injiniyoyin da suka kware da kanikanci ba tare ma da sun iya ko da karatu da rubutu ba.
    Don haka a fassara masa abinda ake son ya yi yadda zai gane. Watakila ma ‘wizard’ ne a irin yadda yake.

  4. Kada kuga laifinsa kuma hakan da yayi ai shike nuna cewa yasan computer masu interview din sune basu san aikinsu ba domin in za’abude computer aiba mai kunnawa bane yake bude window ba sai ka kunna computer r ka sannan computer ka ta bude maka window 7 ko window xp din da ke cikinta. Don haka koda nine kace min bude window sai in bude maka .taga. Inkace bude computer sai in kunna maka computer ita kuma computer sai ta bude window din dake cikinta.

  5. Gaskiya wannan yaro ya kwabsa kwabsawama sosai ai duk wanda yake tu’ammali da computer yasan akwai computer language don haka tunda yasan cewa yazo wurin domin ita computar ai bai kamata ba yayi wani tunani wanda ba na computer ba, ni aganina wannan bai cancanta da ko masinja ba

  6. Salam. Allah yayi masa Albarka, yaro ya cika umarni, dominda motar biliyan goma da ta dubu dari duka sunan su mota, da catarpillar da taxi dukan su mota ce amman sai aka ban banta sunayen su. dasunce masabude mana window na kwamfitan nan sai ya bude CD-Rom to sai suce baisan abin da yakeyi ba