YADDA ZA AYI RIJISTAR KWAS DA MAKARANTA DUNIYAR COMPUTER

https://www.youtube.com/watch?v=Livf5rpTkms

Barka da zuwa Makarantar Duniyar Computer inda zaka iya yin kowane irin kwas kana zaune a gidanka ko ofis dinka a kuma kowane lokaci kake son.

An shirya wannan kwasa-kwasai ne domin baiwa kowa damar ya koyi fannonin ilimin kwamfuta a cikin sauki tare da samun shaidar kwarewa a fannoni da dama.

A wannan makaranta zaku iya yi kowane irin kwas kuma zaku samu kusan kashi 95% na kwasa-kwasanmu a cikin harshen Hausa da kuma bayar da damar yin karatun a kowane lokaci da mutum ke bukata.

Ya ake shiga wannan makaranta?

Ana iya shiga wannan makaranta ne ta hanyar taba wannan link din https://sch.duniyarcomputer.com

daga nan zaka ga inda aka rubuta kwasa-kwasai sai ka taba wurin zaka zabi kwas din da ake su sai ka taba maballin da aka rubuta ENROLL NOW (yana nufin ina son in yi wannan kwas din)

Zai bude maka wani shafin da zaka cikakken bayanai game da wannan kwas din sai ka taba TAKE THIS COURSE (wato na dauki wannan kwas din).

Kana dannawa zai bude maka shafin da zai baka damar turo mana da shi wannan kwas zaka inda aka rubuta ADD TO CART zaka ga wani rubutu ya bayyana yana ce maka wannan program din da kake son yi an kara shi a cikin kwandon siyan kaya.

daga nan sai ka dannan VIEW CART

Daga nan sai ka danna PROCEED TO CHECKOUT (wato muje inda zan cike bayanai na in biya kudi).

Shafi zai bude wanda yake dauke da form da zaka cike bayanan ka

Bayan ka cike kowane bayani sai ka taba PLACE ORDER (wato na siya wannan kwas)

Daga nan shafin da ke dauke da bayanan mutum zai fito tare da bayanin BANKIN MU idan kana Najeriya ne sai ka biya a account din Duniyar Computer idan kuma kana kasar waje ne zaka biya a account din DOLLAR SALISU HASSAN. Kada a manta wurin biyan kudin ayi amfani da ORDER NUMBER domin tabbatar da biyan kudi.

Sauran bayanai game da yadda zaka yi kwas din zai zo a bidiyo na gaba.

Wannan shine Bidiyon yadda za a mallaki kwas a Duniyar Computer tare da biyan kudin kowane kwas.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published.