Categories
Software

Blackberry – Abubuwa guda 10 da mai amfani da ita ya kamata ya sani

An ce kasar Nigeria tana daga cikin kasashen da aka fi amfani da wayar hannu kirar Blackberry ba domin komai ba sai domin a farkon farawa mutane suna amfani da ita saboda isa da mallaka, wasu kuma suna amfani da ita saboda yin kuru da kuma neman ace ina da ita. Wasu kuma sun sayi wayar Blackberry ne domin kawai zamani da kuma abubuwan da ake amfani da su wanda ba kowace waya bace take bayar da irin tsarin shi yasa suka mallake ta. Amma duk da haka sai na lura matuka bayan tsawan lokaci da na mallaki wayar Blackberry kuma tana hannuna amma kuma ban san amfanin ta ba. Sai dai kawai in amsa waya ko in kira, ko kuma aika da sakon SMS da dai kuma daukan hoto. Wannan dalili yasa bayan na sami wani kanina yana da wayar blackberry ya fadamini abubuwa masu amfani wanda na ga ya dace a ce duk mai waya yayi amfani ya sansu.

1.      PIN lambarka da ke jikin Blackberry

Kowace Blackberry da muka ganta tana da wata lamba ta musamman wacce ta kebantu da ita wacce masu amfani da wayar suka sani da PIN Number. To, daya daga cikin abin da ya kamata mu sani cewar wannan lambar ta wayar blackberry da ke hannunka ne kawai kuma babu wayya da za a yi a canza ta. Koda kuwa ka canza wayar ko kuma ka canza SIM din ka to wancan PIN yana can waccan wayar.

Haka idan ka sayi sabuwar blackberry abu na farko da ya kamata ka sani shine mene ne PIN dinta, sannan kuma ya za a yi in gano lambar PIN dinta? Ya danganci wane irin Theme ka ke amfani da shi amma kusan ana samun inda za a ga PIN a wurin da aka rubutu Option a karkashin folda da ke fuskar blackberry ko kuma ka shiga setting sannan ka shiga personal Identification a nan ma zaka iya ganin lambar wayarka.

Wani abu da mafi yawa daga cikin masu amfani da blackberry ba su fahimta ba shi ne a duk lokacin da aika da sako ko da na mene ne to ka sani kana amfani da wannan PIN lambar ne, haka kuma koda kana browsing ko kana aikawa da email ne duk kana amfani da wannan lambar ne. koda yake ba dole bane ka san irin wannan bayanai amma kuma yana da matukar amfani ka san lambar blackberry na abokanka da kuma wadanda kuke yin hulda da su.

Idan ka san PIN number ta abokin ka to za ka iya aika mishi da sako kai tsaye ba tare da wani matsala ba. Duk lokacin da ka aikawa da wani mai blackberry sako ta hanyar yin amfani da PIN din shi to sakon yana zuwa cikin sauri da kuma hanzari. Sabanin email wanda idan ka aikawa da wani sakon imel dole sai imel din nan ya je zuwa ga kwamfutar wani sannan a aika da shi cikin akwai wanda ka aikawa da shi. Irin wannan hanya da ake amfani da ita ta wajen aikawa da sakon daga blackberry zuwa blackberry kamar yadda ake da “PIN Message” yafi kowane irin sako da mutum zai aika saurin isa. Shi yasa a duk lokacin da ka aika da irin wannan sako da zarar sakon ya isa zuwa wurin wanda aka aika zai sa harafin “D” a gefen makin da ke nuna cewar sakon ya isa. Wannan harafi na D shi ke nuna maka cewar wannan sakon ya isa kuma wanda aka aikawa ya ga sakon.

2.      Amfani da Setup Wizard lokacin farko

A lokacin da mutum ya sayi sabuwar Blackberry idan ya kunnan ta abu na farko da zai fito a jikinta shine Setup Wizard. Shi setup wizard wata hanya ce da aka tsarawa mai amfani da wayar blackberry domin  saukaka mishi wajen shirya yadda ya ke son yayi amfani da ita wayar. Amma mafi yawa daga cikin masu amfani da ita wannan wayar sai basu cika da muwa ba wajen su tsaya su cike tambayoyin da shi wannan Wizard din ya ke yi. Rashin tsayawa a cike wannan Wizard din na barin wadansu gurabu da ya kamata a ce ka ciresu ko kuma ka toshe su. Kamar duk lokacin da wayar Blackberry ta zo tana zuwa da yaruka da yawa da mutum baya bukatarsu. To idan a misalin kana son ka rika amfani da yaren turanci ne, to a lokacin da wannan wizard ya zo ya tambaye ka wani yare kake so ka zabi Turanci, to zai cire dukkanin ragowar yarukan da suke cikin wayar. Wannan ciresun da yayi zai taimakawa wayarka wajen rage mata nauyi da kuma kara maka girman ma’ajiyarka a cikinta.

Har ila yau a wurin shirya wayarka akwai abubuwa masu amfani da zaka koya kamar yadda zaka iya shige da fice a cikinta (Navigation) haka a wurin ne zaka iya shirya imel da kake son ka rika amfani da shi a ita wayar taka ta blackberry.

3.      Yi amfani da babban yatsa ba kumba ba

Daya daga cikin kuskuren da masu amfani da blackberry su ke yi shine wajen yin rubutu da maballan blackberry a lokacin da zaka samu mutum yana amfani da kumba wajen yin rubutu maimakon tafin babban danyatsa. Yadda aka tsara maballan da ke jikin blackberry an tsara su ne ta yadda komai fadin babban dan yatsa zai iya hawa kuma yayi rubutu ba tare da ka rubuta harafin da ba ka yi niya ba. Duk wanda ya ke kokarin kiyaye yin rubutu da tafin babban dan yatsar sa to zaka samu ya fi saurin yin rubutu. Amma yin amfani da tsinin dan yatsar ko kuma yin amfani kumba na kawo rashin sauri ga mai rubutu.s

4.      Rage bata lokacin wurin amfani da AutoText

AutoText daya ne daga cikin abubuwan da suke cikin blackberry wanda suke saukakawa wanda ya sani wajen yin rubutu. Domin AutoText shi wanda ya ke lura da mutum a lokacin da mutum ya ke yin rubutu a blackberry. A misali a duk lokacin da mutum ya ke son ya rubuta kalmar can sai yayi kuskure ya rubuta acn to AutoText zai canza ta kai tsaye zuwa can.

Haka shi AutoText yana karawa mutane saurin yin rutubu saboda yana cike wadansu alamomin da mutum ya ke bukatar sai yayi amfani da maballin alt kafin wannan alamar ta bayyana. A misalin idan mutum zai rubuta kalmar can’t dole sai ya latsa maballin alt sannan ya maballin k kafin alamar ta bayyana. Wannan yana kawo cikas wurin yin rubutu da kuma nawa. A blackberry duk lokacin da ka zo rubuta wata kalma wacce akwai alamar (apostrophe) a kanta ka rubuta shi ba tare da ka saka ba, da zarar ka bata maballin space zai saka maka wannan alamar.

Haka har ila yau akwai wadansu karin abubuwa da AutoText ya ke yi fiye da wancan da muka ambata. Domin akwai wadansu abubuwa da aka yi a blackberry wanda zasu kara maka sauri waje yin rubutu. A misali sai kana rubutawa wani sakon imel sai kana son ya kiraka a lambarka. To, idan ka tashi rubuta lambar taka a cikin wayar blackberry baka bukatar ka rubuta ta. Abinda ka ke bukata shine ka rubuta mynumber kana rubuta haka AutoText zai canza ya rubuta lambar wayarka a wurin. Haka idan kana son wani ya rubutawa wani lambar PIN dinka na blackberry to a wurin sakon zaka rubuta mypin kawai shi kuma zai cire ya mayar da lambar PIN din ka ne. sannan idan mutum ya son ka gaya mashi wane irin blackberry kake amfani da shi a halin yanzu kawai zaka rubuta mishi myver wannan zai canza ya fadi irin wacce kake amfani da ita.

Wadanann da muka ambata kamfanin da ya yi blackberry ne ya tsara su. To, kaima da ka samu wannan wayar zaka iya shiga cikin AutoText ka tsara abubuwan da kake son idan ka rubutasu ga yadda kake son fito. A misali sai ya kasance kana yawan amsa tambayoyin mutane amma kuma wani lokacin abubuwa su na cakude maka ya zaman to ba zaka samu damar bayar da amsa a nan take ba. To zaka iya shiga AutoText ka kirkiri wani rubutu da duka sanda ka rubutashi zai fadi kamar haka. Misali ka rubuta llll sai ka rubuta na sami sakon amma a halin yanzu ina cikin uzuru nan gaba kadan za a sami amsa. To duk sand aka rubuta IIII to zai sai canza zuwa ga wancan maganar. Wannan zai taimaka kwarai wajen yin rubutu da sauri.

5.      Karamar hanya wajen yin rubutu (shortcut)

Ana amfani da karamar hanya wajen yin rubutu a blackberry kodayake wannan karamar hanyar ba su da yawa, sai dai yana da kyau mai amfani da blackberry ya sansu domin ya samu saukin rubutu

  • Space bar: wanda ya danna space sau biyu zai sa mashi alamar tsayawa na (.) a lokacin da yake rubutu
  • Rike maballin harafi: wanda ya rike maballin harafi to harafin zai canza daga karamin rubutu zuwa babban rubutu.
  • Rubuta adireshi a internet: idan mutum yana rubuta adireshin wani gida dake internet idan ya gama rubutawa sai ya zo inda zai sa alamar tsayawa idan ya danna maballin space sau biyu zai sa mishi alamar tsayawa ta (.)
  • Rubutun adireshen imel: idan kana rubuta adireshen imel a blackberry inda zaka sa alamar @ to idan ka danna maballin space to zai saka maka wannan alamar idan kuwa ka sake danna maballin zai saka maka alamar tsayawa.

Amma mu sani cewar wannan yana aiki ne kawai a blackberry da kuma application dinta da wanda yayi application din ya bada wannan dama.

6.      Ka sayi memory card

Yana da kyau wanda yake da blackberry ya sayi memory card domin amfanin sa a jikinta yana da yawa. Kasancewar memory da take zuwa da shi ba yawa gare shi ba, ga shi kuma kusan wayoyi suna da tsarin baka damar da saka hotuna da kuma sauti da bidiyo a cikin su. Idan kace za ka yi amfani da wanda yake cikinta to zai kasance ya cika da wuri kuma idan ya kusa cika dukkanin tsofaffin kayayyakin da ka ajiye zasu rika sharewa da kan su.

Shi yasa ya ke da kyau ka sami memory koda dan karami ne ka saka mata domin yin hakan zai ba ka damar zubawa da kuma ajiyar isassun abubuwa a cikin ta.

7.      Kayi amfani da blackberry a matsayin wani ma’ajiya

Idan mutum ya hada wayar sa ta blackberry ta USB da kwamfutarsa to abu na farko da zai fito shine ya tambayeshi ko yana son yayi amfani da blackberry a matsayin wurin ajiya?. To idan mutum ya zabi e to blackberry zata bayyanar da kwakwalwar da take ajiyar abubuwan ka ta hanyar bude wani drive. Idan hakan ya faru zai baka damar da zaka iya dauko kaya kai tsaye da kwamfutar zuwa memory na wayar ko kuma daga wayar zuwa computer ba tare da wani wahala ba. Sannan kuma ta wannan hanyar zai baka damar ka iya diban abubuwan masu mahimmanci daga kwamfutar zuwa wata kwamfutar.

8.      Ka saukar da  software na blackberry (Blackberry Desktop Software)

Zaka iya yin amfani da blackberry ba tare da wani software da zai taimaka maka ba kuma babu matsala. Amma amfanin wannan Blackberry Desktop Software yana da amfani matuka musamma ga wanda yake son yayi wadansu abubuwa da suka shafi amfani da bayarsa a matsayin hanyar samun internet ga kwamfutarsa. Domin kamar wanda ya sami damar shiga internet a wayarsa to zai iya mayar da wayar ta koma a matsayin abin shigarsa internet (modem). Yadda idan kana son ka yi browsing a kwanfutarka ba sai ka nemi wani modem ba, to wannan software zai baka damar mayar da wayarka a matsayin modem sannan kuma ka iya shiga internet ba yi browsing kamar yadda kake yi da wayarka.

Haka ana amfani da wannan software wajen sakawa ita wayar sauti da bidiyo wanda a lokacin daya daga cikin amfanin da yake da shi shine yana iya canza maka tsarin bidiyon ko saution zuwa wani tsari na daban da blackberry. Haka zai baka damar ka ajiye dukkan abubuwan da ya ke cikin wayarka zuwa cikin kwamfutarka. Tun daga sunayen cikin layin wayarka, da wanda yake cikin kan wayar, da sakwannin SMS da ka samu dama dukkan wadansu abubuwa da suke kan wayar taka. Wanda daga baya idan wayar ta lalace ko ta bace zaka koma kan wannan application ka saukar da su.

Haka da wannan software zata iya dubawa ka ga ko kamfanin blackberry sun sake sakin wani sabon Operating System domin ya baka damar ya canza. Domin mafi yawan lokaci kanfanonin waya sukan canza manhajan wayarsu to, da wannan software kawai zaka iya mayar da ita blackberry ta samu sabon manhaji.

9.      Zubawa blackberry software masu amfani

Akwai wadansu software ko kuma application masu amfani da mai blackberry ya kamata ya saka su a cikin wayarsa wadannan application suna da yawa wadansu kyauta ne wadansu kuma na kudi ne. da farko dai idan kana son ka shiga gidan da ake samun irin wadannan application da suke amfani a wayoyin blackberry dole sai ka shiga gidan ajiyar application na su wanda ake kira da App World.

Da zarar ka bude menu dinka zaka ga hoton da yake wakiltar app world wanda da zarar ka taba shi zai bude maka babban shafin nasu. Idan ka shiga zai nuna maga wadansu dakuna kamar guda biyar wanda suka hada da dakin

  • Games a wannan dakin ake samu application na wasanni
  • Apps wannan daki ne da ake samun application kawai
  • Theme wannan daki ne da ake samu themes (riguna) da zaka iya canzawa blackberry dinka.
  • My World idan ka shiga wannan dakin shi kuma zai nuna maka dukkanin application da ka riga ka sakasu a cikin wayarka
  • My Account shine dakinka da zaka iya sharia yadda zaka sarrafa yadda zaka rika biyan kamfanin blackberry kudi a lokacin da ka ga application na saidawa kuma kana son ka siya

10. Mayar da Blackberry ta koma taka

Hakika mutum zai iya mayar da Blackberry din shi ta zama kamar tashi, an baka dama kamar kowace irin waya a blackberry shima zaka iya canza theme da yadda kake son ka ga wayar ta zama yadda kake bukata. Kamar canza sautin kira da sautin shigar sakon SMS da wani irin launi kake son idan an aiko maka da sako ya nuna maka ko kuma ya kake son idan ka bude Bluetooth wani irin launi kake so, da dai makamantansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *