BIOS da CMOS Dan Juma da Dan Jummai

Mene ne CMOS?

CMOS wanda cikakken ma’anarsa shine Complimentry Metal-Oxide Semiconductor shi kuwa BIOS na nufin

Motherboard

, gaskiya ne suna da alaka kusa da juna amma ayyukansu ya babanta. Shi BIOS Firmware ne,wato wadansu umarni ne na software da ake sasu a jikin wani chip da yake jikin motherboard. Aikin da BIOS yake yi yana duba dukkanin Hardware da aka hada da na’ura a duk lokacin da aka kunna ta, kafin ma OperatingSystem ya fara aiki.

Ka lura da kyau a lokacin da kake kunna na’urarka, farko wani baki ne ya ke farawa a jikin monitor, daga baya sai sunan kamfanin da suka yi motherboard sunansu sai ya bayyana, misali ya nuna HP ko Compact ko Mercury da dai makamantansu, to idan ka ga haka, to, yana fada maka cewar, kamfani kaza suke da alhakin yin wannan Motherboard. Ko da yake ba dole bane ace su suke yin komai da komai da ya ke jikin ita wannan computer ba.

Bayan ya nuna sunan Motherboard, da nunawar da kuma wucewar shi duk bai wuce dakikoki ashiri. Ka sake lura da kyau za ka ga ya fara rubuta kananan rubutu, wadannan rubutun suna fitowa daya bayan daya, idan ka lura da kyau a dai-dai wannan lokacin yana fada maka cawar ya duba ya ga akwai Hard Disk iri kaza, ya ga akwai CD/DVD duk a jikin wannan computer, da dai makamantansu. Shima wannan nunawa da yake yi bai wuce ‘yan dakikoki ashirin idan ya dade dakika talatin. To wannan abubuwan da suke nunawa BIOS shike da alhakin bincikar su da kuma duba lafiyarsu.

Wani abin sha’awa shine, ba ya na duba sune kawai ba don jin ko suna nan ko ba sa jiki ba ne, yana lura hatta da lafiyarsu, yanayin yadda suke yin aiki, da karfin yadda aikin na su ya ke, da kuma duba wane kamfani yayi su, da dai makamantan haka. A lokacin da ka kwance computer, ka canza mata Hard Disk, ko kuma ka cire Floppy Drive to bayan ka kunna computer, a wani lokaci kafin ta fara Loading Windows sai ka shiga wurin da ake shirya BIOS domin ka tabbatar mata da wannan canje-canjen.

Matsalar guda ce, kana bukatar cikakkiyar masaniya game da yadda za ka shiga wajen shirya BIOS sannan idan ka shiga ka kuma san me za ka taba, mene ne kuma bai kamata ka taba ba, domin kusan dukkan hanyoyin da ake sarrafa computer a nan ake shirya su. Kama tun daga keyboard, Mouse, Monitor, Hard Disk, Floppy Drive, da karfin CPU dama wadanda ban ambata ba dukkansu a BIOS ake shiryasu da kuma yadda ita na’urar zata fahimce su har tayi aiki da su. Da za ka shiga wajen da ake shirya shi BIOS sannan ka cire keyboard ko CD ROM, to ko da na’urar za ta tashi, za ka samu keyboard ba zai yi aiki ba, domin na’urar tun daga lokacin da za ta tashi an gaya ma ta cewar babu shi a jikin ta.

Amma fa a sani BIOS yana da dan karamin RAM da ya ke jikin motherboard, wanda yake ajiye ko wane irin bayanai da aka shirya wa BIOS domin yayi aiki kamar yadda ya kamata, su kuwa wadannan bayanai da suna zama ne cikin wannan dan karamin RAM.

To mene ne aikin CMOS a jikin Motherboard?

CMOS wani dan karamin circuit ne da shima ya ke jikin Motherboard wanda ake amfani da shi wajen tunatar da ita na`urar abubuwan da aka tsara a jikin BIOS. CMOS RAM ba shi da girma a jikin Motherboard, sannan baya jan wuta, kusan dukkanin na’urorin da suke da Processor ko kuma suke da duk wani abu da yake aiki digitally, misali agogo “kifta kato” ko kuma Calculator na aljihu dama memori na computer dukkanin su akwai CMOS a jikinsu. Zaman CMOS a jikinsu shi ke basu damar tunawa da abin da aka aji ye ko aka shirya a jikin BIOS.

Saboda haka, abubuwan da ake shiryawa BIOS na maganar Hard Disk, gudun da CPU ya ke yi a jikin na’ura da makamantansu suna zama ne a kimtse a cikin CMOS RAM, saboda idan da za a sake tayar da ita na’urar ba sai an sake gaya ma ta abubuwan da su ke jikinta ba.

Kamar yadda na fada a baya cewar ana shiga wajen shirya BIOS’ to, idan ka shiga wajen BIOS akwai yan kananan shirye-shirye da zaka yi wa abin da ake kira CMOS RAM, kamar abinda ya shafi saita lokaci a jikin na’ura, rana da kwanan wata da shekarar da ake ciki, manya-manyan Hard Disk da ke cikin na’ura, Floppy Drive dake jikin ta wani irin VGA/VIDEO (wato Monitor kenan) za tayi amfani da shi, da dai makamantan ire-iren su kusan dukkanin su suna zama ne a cikin CMOS RAM, shi ya sa a wasu na’urori sunan da zaka ga an ambata a jikin bangon shafin da zaka shirya BIOS za ka ga an rubuta BIOS/CMOS setup, wato wajen shirya tsare-tsaren BIOS da CMOS.

 Idan aka tuna da CMOS RAM mun san cewar dukkanin abinda aka sa a RAM idan aka kashe wutar computer hakika komai ya tafi, ko kuma muce ya goge, to amma me ya sa idan an kashe computer take tuna duk wadancan abubuwa? Wannan haka yake domin in tabbatar maka da haka, wadannan shiri da yake ajiye akwai dalili da yasa ba su shafewa a lokacin da aka kashe ita computer, saboda akwai wani dan karamin batiri da ya ke jikin Motherboard wanda shi ke da alhakin baiwa CMOS RAM wuta a lokacin da ka kashe computer, wanda ka’ida shi wannan batiri ya na kaiwa tsawon shekara biyar yana aiki, ba tare da ya lalace ba. Idan har batirin yana aiki sai aka kashe Computer,  har wani dalili ya jawo aka kai kamar tsawo shekara goma bai kunna ta ba duk randa aka sake kunna ta zata tuna komai da komai da ke hade da ita, kuma ba za tayi batan kwanan wata ba, ballantana tayi batan lokaci. Amma idan aka yi rashin sa’a batirin ya lalace baya aiki, to, zaka ga duk sadda ka kunna ta sai ka sake shirya komai da ke jikin computer, kuma dole ka rinka canja kwanakin wata a jikin na’urar.

Wannan shine a takaice banbancin da ke tsakanin CMOS da BIOS kusan Dan Juma ne da Dan Jummai. Tabbacin daya shine zaman lafiyar daya, domin ka ji dai kusan dukkan wadansu mahimman kaya da zaka yi aiki da su ajikin na’ura suna bukatar ka sa su, su tashi tare da ita na’urar, shi kuma CMOS shi ke da alhakin hardace abubuwan da BIOS ya karanto.

Kafin in kulle nasan wanda zai karanta wannan mukala ya ce, ‘To ai yanzu ina iya cire Keyboard ko Mouse a jikin na’ura sannan in canza su da wasu kuma suyi aiki’ wannan gaskiya ne amma hakan tana yiwuwa ne kawai idan kana amfani da USB ba PS/2 ba.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. AssalamuAlaikum,
    Don Allah Duniyar computer ina son ku taimake ni da yanda zan gyara matsalar computer ta. Dafarko idan na kunnata zata nunomin sunan kamfanin da yayi wannan computer, sannan ta rubuto WELCOME daga nan sai ta nuno min wellpepar da cusor kawai duk wani shortcut nawa bazai fitoba hatta da window start bazai fito ba cusor kadai ke motsawa in ka tada mouse. Ina fatan don Allah ku taimakamin.