Bill Gates ya sha ruwan ba-haya

Mai Kamfanin Microsoft Bill Gates, ya sha wani ruwa da aka sarrafa da wata na’ura wanda kuma asalin sa daga ba-haya aka samo shi.

A cewar Gates, wanda ya nuna amincewar sa da na’urar da ta sarrafa ba-hayan zuwa tsabtacaccen ruwan sha, fasahar za ta iya taimakawa wajen samar da ruwan sha ga kasashe masu tasowa.

Haka itama kungiyar nan mai suna WaterAid dake fafutukar ganin an samar da tsabtacaccen ruwan sha a duniya, ta ce ta amince da wannan kimiyya.

A cewar kungiyar, akalla mutane miliyan 748 a duniya ba su da hanyar samun tsabtaceccen ruwan sha.

A wani hoton bidiyo da ya sa a shafinsa na intanet, Gates ya shaida lokacin da aka zuba ba-hayan a na’urar ta kuma sarrafa shi ya koma tsabtataccen ruwan sha.

“Ruwan ya na da dandanon da kowane irin ruwan sha yake da shi, kuma bayan da na yi nazarin irin fasahar da aka yi amfani da ita wajen sarrafa ruwan, zan dinga shan ruwan kullum.” Gates ya rubuta a shafin na sa.

Har ila yau a hoton bidiyon, wanda ya kera na’urar, Peter Janicki, ya ce da farko nau’rar tana kona ba-yahan ne, sannan sai ta tace ruwan dake jiki daga gudajin ba-hayan.

Ya kara da cewa daga nan ne kuma sai nau’rar ta kona ruwan ta yadda zai koma tsabtacacce ruwan sha.

Gates ya kara da cewa idan aka samar da hanyoyin kawar da ba-haya, za a iya kaucewa cututtuka da dama da ke hana yara kanana girma.

Daga BBCHAUSA.COM

Related Articles

Yadda ake gyara wayar hannu idan ta jike da ruwa.

Haka nan babu yadda za ayi ace na sayi waya kimani kudi N3500 yadda gari yake ciki ne har-har kume ace in yi sakaci wa ta matsala ta same ta. Na san wani zai yi dariya ya ce ji wannan a na maganar wayoyi N90,000 yana maganar N3500. Haka ya ke kamar yadda ka ke ganin kana iya ri ke wayar N90,000 kuma ka na gani cewa ka rike waya to ai kai iya karfin ka ke nan. Domin hausawa suna cewa garin da kowa makaho ne, to mai ido daya ai sarkine. Wanda ya ke da wayar dubu daya da dari biyar da wanda yake da ta taro ko sisi dukkansu ba za su so wani abu da zai bata su ba ko kuma ayi masu fatan lalacewa.

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *