Barka da zuwa Duniyar Computer mai DVD

Alhamdulliah! Muna miƙa godiya ga Allah maɗaukakin sarki da ya nuna mana wannan lokaci da muke sake gabatar muku da Mujallar Duniyar Computer kashi na uku wanda yake haɗe tare da DVD da aka saka mishi darussa har guda goma ko fiye da haka.

Mun ɗauki tsawon lokaci wannan mujalla bata fito ba kamar yadda muka yi alƙawuri saboda abubuwan da zamu iya kira na yadda al’amura suke tafiya da kuma yadda muka kasa gane kan zaren da zamu iya kamawa, amma In Sha Allah mun ɗauki wani irin mataki wanda zai taimaka na ganin muna iya fitowa koda sau hudu ne a shekara.

A cikin wannan mujallar mun yi kokarin kawo kashi saba’in da biyar cikin ɗari na abin da ke cikin DVD a rubuce a cikin ita mujallar. Saboda haka wanda yake riƙe da wannan mujallar lallai yana buƙatar wannan DVD domin akwai darussa da suke cikin DVD amma basu a rubuce a mujallar.

A cikin tsokaci da muke yi na musamman wannan karo mun yi gamsasshen bayanai ne a kan jagora kuma shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iƙamatus Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau mai taken Gajiyawar Ahlussunna Wajen Cin Gajiyar Shugabancin Sheikh Bala Lau.

A wannan fitowa mun kawo muku bayani mai tsawo kuma gamsasshe game da abin da ake kira SOFTWARE wanda a mujallarmu ta farko da ta biyu tayi bayanai gamsassu a kan abin da ya shafi Mece ce Computer da kuma Hardware. A wannan fitowa mun kawo darussa masu matuƙar muhimmanci a kowane fanni kamar Programming Language: Wanne ne ya kamata na fara koya a wannan darasi mun yi bayanai a kan yaren kwamfuta da ya kamata duk wanda yake da sha’awa ya manar da hankalinsa wurin koyonsu. Kamar yadda kodawane lokaci ake ƙorafi akan matsalar Idanu tare da Kwamfuta mun yi bayani akan Hanyoyi goma na magance matsalolin Idanu.

Daga cikin manyan mukalolinmu kuma wadanda suke cikin DVD akwai Kurakurai goma da Sabbain masu amfani da kwamfuta suke yi sannan kuma akwai Abubuwa bakwai da bai kamata yara na yi a Intanet ba. Mun yi cikakken bayani game da sabuwar Babbar Manhajar Kwamfuta data shigo kasuwa a karshen shekarar 2015, mai suna Windows 10: Abubuwa goma muhimmai da ya kamata kowa ya sani.

Idan muka tsallaka bangaren wayar tafi-da-gidanka wannan karon mun kawo muku darussa da kuka daɗe kuna tsumaya irin Yadda ake raba data/MB a layukan Najeriya. Sannan mun yi magana a kan Kurakurai goma da mutane suke yi a group chat.

Waɗannan kadan ne daga cikin abin da wannan mujalla ta ƙumsa. Da fatan Allah ya yi mana jagora amin.
Na gode.

Salisu Hassan
Babban Edita

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *