Banbanci tsakanin WAN da LAN

Ina son sanin banbancin WAN@ LAN

Malam Sadiq idan kaji ance LAN ana nufin LOCAL AREA NETWORK wato shine misalin kamar networking din yake hada computoci a jikin gini guda ko kuma kamfani guda, wanda iya binda ake iya yi shine a rinka sharin files da wasu document ko kuma messages da makamantan su irin wannan irin LAN shine ake danganta computocin da cewar suna kan ethernet network. AMMA shi WAN shine ake kira da WIDE AREA NETWORK shi networking ne da yake hada computoci da dama ba a wuri daya ba, misali shine lokacin da ka dauki computer ka hadata da internet tana hade da WAN ne domin tana hade da wadansu computoci miliyoyi a duniya, wanda ita kanta computer ka da ka hada ta da internet kaga tana hade da wata computer da ke wata kasa ko kuma wata jiha. Sabo da haka, BANBANCI TSAKANIN SU shine shi LAN yana hada computer a wuri daya kamar a ofice ko company, shi kuwa WAN yana hada computoci ne daga wannan yanki zuwa wannan yanki, daga wannan kasa zuwa wannan kasa, mi sali lokacin da nake rubuta maka wannan amsa, ina hade da computer FACEBOOK da fatar ka gamsu.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *