Antivirus Guda 4 Na Kyauta wanda suka fi kowanne kyau a 2019

Kasancewar wayoyin hannun mu sun zama wani bangare na tafiyar da harkokin rayuwar mu, mutane a yanzu ba kawai don su amsa kiran waya suke amfani da su ba. Maimakon haka mutane na ajiyar muhimman bayanai na sirrinsu a cikin wayoyinsu. Abin tambaya shine shin babu matsala idan na ajiye bayanai masu muhimmanci a waya ta? Amsar ya danganta da irin lura da tsaron ta da kayi ta hanyar saka mata Antivirus mai inganci.

Saboda haka mun dauko muku wadansu manhajoji na kariya ga wayoyinku (antivirus) wanda suke aiki a wayoyin kirar Android wanda ake samunsu a Google Play Store na kyauta domin kariya ga wayoyin ku.

1.    Kaspersky Mobile Antivirus

Kaspersky Anivirus yana da matukar muhimmanci da kyau musamman ga masu amfani da wayoyin android. Duk da cewar shi wannan manhaja ta kudi ce, amma kuma suna da na kyauta wanda yake yin aiki tamkar na kudi.

Duk da na kyauta abin da yafi mayar da hankali shine zakulo malware da virus, sai dai na siyarwar yana baka cikakken tsaron masu satar waya, anti-theft, anti-phishing wato ‘yan dandatsa masu neman satar bayanai ta sirri, sannan kuma zai baka damar karin tsaro na kulle dukkan wadansu manhajoji da suke cikin wayarka.

Zaka iya gwada saukar da kudin kayi amfani da shi kyauta kwana 30 ba tare da ka biya ba.

Domin sauke wannan antivirs akan wayarka taba nan

 Download Kaspersky Mobile Antivirus

2.    Avast Mobile Security

Miliyoyin mutane ne suke amfani da wannan manhaja ta Avast kuma cikin sauki domin da tabawa sau daya kacal zai baka damar lalubu dukkan wani mugun virus dake cikin wayarka ko ma wata manhaja da wani virus yayi kutse a cikinta, ko kuma manhaja masu trojan. Haka da wannan avast din zaka samu cikakken tsaro daga dukkan wani manhajar leken asiri spyware da kuma kowane irin virus ake da shi.

Duk da suma suna da na siyarwa amma wannan na kyautar zai maka dukkan wadancan abubuwan da muka lissafo, sai dai na kudin zai karawa wayar naka tsaro da kuma cire talla da zai rika shigowa wayar taka, sannan ya kara maka da manhajar lura da kulle ita wayar kamar lura da SIM da kama barawon wayar ta amfani da Camera da dai makamantansu.

Domin sauke wannan manhaja ta Avast dannan link dake kasa

 Download Avast Mobile Security

3.    Bitdefender Antivirus Free

Shima Bitdefender manhajar kariya ce da ke zuwa da kayan aiki masu mutukar tsare wayoyin daga dukkan wani irin virus da zai iya shigowa wayar mutum. Yana daga cikin manhajojin marasa nauyi a wayoyi wanda kuma yake amfani da fasaha ta zamani wurin bincikar gurbatattun manhajoji cikin sauri da matukar hanzari.

Bitdefender bayan shanyewa mutum batirin wayarsa ba kuma ya sa wayar ta rika yin nauyi wuri aiki a lokacin da yake yin wannan bincike domin ya gano virus dake cikin wayar. Haka kuma yana yin aiki tukuru domin ganin ya binciki dukkan wata manhaja da aka saka cikin ita wayar.

Shima kamar sauran Bitdefender yana da wanda ake siyarwa wanda ake kira da Bitdefender Mobile Security & Antivirus, wanda zaka iya gwada amfani da shi na kwana 14 domin samun karin kariya ga irin bincikar Malware da tsaron wayar bayan an sace ta anti-theft, tsaron sirrin kayan da aka ajey a cikin ta, manhajar rufe manhajoji duk zaka iya gwada amfani da su a lokacin da kake yin gwajin kwana 14.

Domin sauke wannan manhaja ta Bitdefender dannan link dake kasa

 Download Bitdefender Antivirus Free

4.    Norton Security & Antivirus

Karin tsaro da Norton suka kara a kwanan nan ya karawa wannan manhaja karfi da kuma ikon binciken virus har a cikin bangaren Norton na kyauta. Shi wannan manhaja ta Norton taka baka kari dari bisa dari wurin cire kowane irin malware ne a cikin wayarka. Haka wannan manhajar ta Norton idan ka saka ta zata tsare ka ga dukkan wata manhaja ta leken asiri wato spyware wanda irin wadannan manhajoji suna sabbaba wayoyi su rika yin nauyi lokacin da ake amfani da su.

Haka da wannan Norton zaka iya kiran wayarka lokaci da kake nemanta ko ta bace ko kuma an sace, kana zaka iya rufe wayar idan wani yana amfani da ita ko kuma an sace ta, haka zaka iya hana shigowar waya ko sakon karta kwana na SMS.

Haka kuma yana da wata manhaja mai zaman kanta wacce ake amfani da ita domin lura da manhajojin da suke waya da kuma password manager wato manhajar lura da password da ba sai kowane lokaci ka rubuta password ba. Akwai karin abubuwa ga wanda ya biya Norton na kudi, ko shakka babu Noton Security yana daya daga cikin Antivirus da bashi da na biyu.

Domin saukar da wannan application na Norton sai ka taba link dake kasa.

 Download Norton Security and Antivirus

Wannan sune Antivirus mafi shahara wanda ya kamata ace babu wata waya ta Android da ya kamata ace babu daya daga cikin su.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *