Categories
Duniyar Waya

Android – Tambayoyi 7 da mai amfani da Wayar Android ya kamata ya san amsarsu

Android wacce ake furta ta da hausa anduroyid manhaja (OS) ce da kamfanin Google Media Inc da ke kasar Amurka ya mallaki lasisinsa wanda shi wannan manhajar ake amfani da ita akan wayoyin hannun da kuma kananan kwamfutocin hannu da ake kira da Table PC.

Su irin wannan wayoyi na Android ba kamar sauran waya bace kasancewar ita tsarin rike ta da tsarin amfani da ita ba a ko’ina ake yi ba. Shi yasa na ga ya dace in yi mana bayanai akan wadansu tambayoyi guda bakwai da ya kamata mai amfani da wadannan wayoyi ya sani kuma ya san yadda zai amfani da ita.

1.      Dole ne sai na yi amfani da Google Accout kafin in iya amfani da Android?

Haka yake! Dole duk wanda ya sayi waya ko kuma tablet ya zama yana da account tare da kamfanin google kafin ya yi amfani da ita. Amma wannan ba ya kebance cewa akwai wani bangare na google accout wanda ya zama wajibi ne a ce shi ne mutum zai yi amfani da shi ba. Abin da ake so kawai ka yi rijista da kamfanin ta wurin mallakar daya daga cikin abubuwan da suke gabatarwa na ayyukansu, kamar gmail da makamantansu. Kodayake google yana ba mutum damar kara wani imel wand aba google ba, sai dai duk lokacin da mutum yake son ya shiga ya karawa wayar tashi ko tablet dinshi kuzari ko kuma ya kara mata wani application to dole sai in yana da account tare da google. Kuma akwai wadansu abubuwa masu matukar amfani ga mai amfani da wayar android ko tablet wanda idan mutum ba ya amfani da account na google ba ne to ba sai same su ba.

2.      Wace hanya ce ta fi kyau wacce zan bi in kwashe duk sunayen da suke cikin wayata?

Akwai hanyoyin da mutum zai iya bi domin ya ga ya kwafe tsofaffin lambobin cikin wayar sa zuwa wayarsa ta android. Daya daga cikin hayar shine mutum zai iya bude google sai ya shiga dakin aikawa da sakon imel wanda ake kira da gmail to sai ya rubuce dukkanin sunayen da ke wayarsa daga nan lambobin da kansu zasu dawo cikin wayarsa ko kuma tablet pc din shi. Ko kuma ka yi amfani da tsohuwar hanya na kwafe lambobinka a cikin SIM dinka sannan ka saka shi cikin wayar android ko tablet sannan ka kwafe shi cikin ta.

3.      Mene ne dalilin da yasa wayoyin android ba sa kama da juna?

Kamfanin google su suka kirkiri manhajan Android amma kuma sai suka baiwa kamfanonin da suke yin waya damar su yi amfani da wannan manhajar a cikin wayoyinsu. Saboda haka shi yasa ka ke ganin fuskokin da kuma kamanninsu ya banbanta. Kamfanonin da suke da wannan lasisi sun hada da kamfanin Samsung da kuma kamfanin HTC, wanda wadannan kamfanonin kowannen su kera waya da kuma kayan kwamfuta ya ke yi. Saboda haka kowane daya daga cikinsu yana da damar yayi irin kalan waya ko kuma tablet da yake ganin zata amsu a hannun abokanen cinikinsa.

4.      To yaya za ayi in samu android wacce ba ta wadancan kamfanonin ba?

Idan baka son daya daga cikin wayoyin da kamfanin HTC ko Samsung suke yi, to ai kamfanin google yana da nashi wayar mai suna NEXUS. Wanda aka fi sani da Nexus 7 Tablet da kuma Galaxy Nexus Phone. Wadannan guda biyu da manhajar da kuma karafan da suke jikinsu duk mallakar kamfanin google ne. Sannan kuma su wadannan wayoyi kodawane lokaci kamfanin google yana kokarin ingantasu ta wajen manhajin da suke amfani da su, kasancewar suna samun komai kai tsaye daga wurin google. Su kuwa sauran wayoyi kamar na HTC da Samsung wadanda suke amfani da manhajar android sukan dauki wani lokaci mai tsawo kafin a waiwayi manhajar tasu, domin abu ne mai yawa da kuma fadi da kuma abubuwan da wadancan kamfanonin suke yi yana musu yawa.

5.      Mene ne banbanci tsakanin Home Screen da kuma App Drawer?

Shi App Drawer shine wurin da za ka samu dukkanin application da ka daurawa android, an kira wurin da Drawer kamar yadda malam bahaushe ya sani da matsayin rumbu kasancewar nan ne ake samun abubuwan da aka ajiye a ciki. Saboda haka Adroid suna da fallaye guda bakwai da suka baka damar ka fito da dukkanin application da kake yawan aiki da su, domin samun sauki. To wadannan application da ka saka a kan wannan falle shi ake kira da Home Screen. Su kuma application da baka son ganinsu a wannan fallen su kuma suna cikin App Drawer.

6.      Mene ne Widgets?

Widget kamar yadda ake furtasu da hauwa “wijet” suna da amfani matuka domin su ana amfani da su wajen bayyar da wadansu bayanai da kuma tattalin wutar batirin adroid. Su kamar hotuna ne na wadansu application da ka saka a cikin Home Screen din ka wanda za su rika fada maka abubuwan da yake gudana karkashin wadannan application da ka saka su a cikin wijet din. Misali wanda ya dauko application na facebook ko twitter ko na gmail ka saka a cikin wijet to duk sakon da ya shigo daya daga cikin wadannan application din zaka ga matashiya kai tsaye wand aba sai ka bude shi application karan kansa ba.

7.      Ina da abubuwan saurare a itunes zan iya sauraronsu a android dina?

Akwai wani software da ake kira da doubleTwist yana aiki kamar yadda kasan Itunes ya ke yi. Saboda haka idan ka daura shi zai baka damar saukar da duk abin da kake da su a Itunes zuwa Android dinka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *