An kirkiri manhajar waya ta tiyatar ido

Masana ilimin kimiyya a Birtaniya sun kirkiro wata manhajar wayar komai da ruwanka, da za ta kawo gagarumin sauyi a bangaren kula da idanu a kasashe masu tasowa.

Manhajar za ta baiwa ma’aikatan lafiya damar duba wa ko akwai cuta a ido, kuma su yi gwaji da na’ura ‘yar karama mafi araha.

a matsalar ido a kasashe masu tasowa na yankunan karkara, inda likitocin idanun da za su taimaka musu ba sa iya zuwa.

Mutane fiye da miliyan 285 ne a fadin duniya, ke fama da matsalar gani ko kuma makanta.

Ana tunanin cewa za a iya rigakafi ko magance hudu zuwa biyar na matsalolin ido, ta hanyar yin tiyatar yanar ido mai sauki, ko kuma ma amfani da tabarau.

A yanzu haka ana kan gwajin wannan manhaja a kan mutane 5000 a wasu kauyuka na kasar Kenya.

Daga BBC HAUSA

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *