Akwai Virus a Wayar ka KA SANI KUWA?

Virus Na Waya (Phones)

Virus na wayar-tafi-da-gidanka kamar virus na computer ne, abin da ake nufi da virus shine wani file ne da yake yin aiki musamman domin ya bata ko lalata wani bangare na computer ka ko kuma wayarka. Ko da yake computer virus yana yaduwane a sanadiyar email da kuma downloading daga internet, shima virus na waya yana yaduwa ne ta downloading daga internet ko kuma ta karbar sakon na MMS (Multimedia Messaging Service) ko kuma ta turo sako daga bluetooth. Sau tari a wannan lokaci virus da suke shiga wayoyin hannu suna shiga ne ta wajen turo maka wani abu daga computer. Ko da yake virus da yake shiga daga wata waya zuwa wata har yanzu bai gama shaharaba.

Virus na waya da zai iya shiga ta wata waya yafi yawane ga masu amfani wayar da take amfani da tsari na Symbian, ko da yake wadanda suke rubuta shi wannan virus na waya basu wani samu karbuwa ba a duniyar kamfanonin da suke yin waya ballantana su sami wani karfi, dalilin haka yakasance ko da anyi wani virus na waya zaka samu bai cika bata wayar ba gaba daya.

 

Ya aka yi suka yadu?

Duk wanda yake amfani da wayar da kawai sai dai a kira shi ko kuma ya amsa waya ko kuma ya kira ya aika da sakon SMS ya kwantar da hankalinshi babu wani virus da zai sami wayar shi.

Amma dukkanin wata waya da take da Bluetooth sannan kuma zaka iya karbar sakon MMS ko kuma kayi browsing da wayarka zata iya kamuwa da virus na waya. Waya tana da virus da dama wadanda suke iya yaduwa ta hanyoyi guda uku

·        Downloading a Internet – virus na waya yana yaduwa ta internet kamar yadda aka sani virus na computer yana yaduwa. Mutum zai shiga internet da wayarshi yaga wani file ko game ko kuma hoto ko kuma theme yayi mishi ya saukar da shi zuwa wayarshi ashe yana tattare da virus bai sani ba.

·        Karbar sako ta Bluetooth – virus na waya yana iya yaduwa a sakamakon Bluetooth din wayarka da ka bude domin wani ya aiko maka da sako, sai aka yi rashin sa’a ita wayar tashi akwai virus a ciki to duk sakon da ya aiko maka da shi zai taho tare da virus.

·        Multimedia Messaging Service (MMS) – wannan wani dama ce da wayar ka take baka idan kana son ka aika da sokon hoto ko kuma sakon video ga wani abokin ka ko kuma wata waya ba tare da Bluetooth ba ko kuma internet, kamfanin da kake amfani da layinsu su suke da alhakin baka wannan dama ko da wayar  tana supporting MMS, wanda shi virus da ya shigo a sakamakon MMS yafi hadari sabo da zai shiga cikin contacts dinka ne kai tsaye ya rinka aikawa sauran mutanen ka wannan virus din.

Kada ka manta dukkanin wani virus na waya ko na computer mataki daya suke bi shine dole sai ka yi installing dinsu a cikin wayar ko kuma computer zasu iya yin aiki, da wannan dalili ne ya kasance mafi wayan virus sun fi zuwa tare da games ko kuma wani program da za a ce idan ka sakashi zai iya tsare ka daga wani abu.

Commwarrior Virus an samu bullowar shi a Junairun 2005 kuma shine virus na farko da ya fara shiga wayar tafi da gidan ka har ya iya yin ta adi, kuma wani abun mamaki zai iya watsa kanshi a dan kankanin lokaci ga kusan duk mutumin dake da waya kuma yabar wayar a bude kusa da wanda yake da wannan virus din. Yadda yake yada kanshi shine ta hanya ta Bluetooth da MMS, da zarar ka sami sakon wannan virus sannan kuma kayi installing dinshi, kai tsaye zai fara neman wata wayar da Bluetooth dinta yake a kunne, da zarar ya samu zai aika da wannan virus ga wannan wayar. Haka shi wannan virus na Commwarrior zai kuma shiga cikin contact list dinka ya tura musu sakon MMS da shi wannan virus. (ya kake ganin idan kaga sako daga webmaster zaka karba ko zaka ki karba?). shi yasa commwarrior virus ya zama shahararren virus da ya damu mutane a wancan lokacin tunda yana amfani da hanyoyi biyu ne wajen yada kanshi.

Sabo da haka ya virus din yake yi idan har ya shiga wayar ka?

Barnar da yake yi.

Virus na waya na farko da aka sani shine Cabir duk da yake ba ya wani cutarwa ko kada, a binda kawai yake yi shine zai shiga wayar ka ne kawai yayi ta kokarin yada kanshi. Ko da yake daman mafi yawan virus na waya basu cika cutarwa ba. sosai

Kadan daga cikin abinda virus na waya ke iya yi shine ya shiga ya share dukkan wani contact da kake da su, ko kuma ya goge wani calendar da ka shirya a wayarka da makamanta haka, sannan kuma zai iya kwashe sunayen mutanen da suke cikin yawar ka gaba daya ya dauki wani hoto a cikin wannan wayar taka ta dauka virus a cikin shi ya kuma aikawa kowa da yake cikin contacts naka. Wani abin haushi da irin wannan MMS virus shine baya da watsa kanshi da yake yi, haka kuma yana yin amfani da kudin da kake da shi a waya tunda shi MMS ba kamar SMS bane, ana cire kud da dan dama. Abu kuma mafi muni shine zai iya neman wani application dake cikin wayarka ya lalata shi, ko kuma ya lalata wayar gaba dayan ta ta zamanto bata da amfani.

Ga wasu daga cikin virus na waya guda biyar da bayani game da su.

Sunan Virus: Cabir.A

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: June 2004
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian Series 60 phone
 • Hanyar da yake yada kanshi: updating
 • Irin cutarwar da yake yi: Baya cutar wa
 • Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/cabir.shtml

 

Sunan Virus: Skulls.A

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: November 2004
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian phones
 • Hanyar da yake yada kanshi: Downloading a Internet
 • Irin cutarwar da yake yi: yana hana ka komai a wayar illa kira da amsa kira
 • Karin bayani: http://www.f-secure.com/v-descs/skulls.shtml

Sunan Virus: Commwarrior.A

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: January 2005
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian Series 60 phones
 • Hanyar da yake yada kanshi: Bluetooth da MMS
 • Irin cutarwar da yake yi: yana aikawa da sako MMS ga duk wanda yake cikin contact
 • Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/commwarrior.shtml

Sunan Virus: Locknut.B

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: March 2005
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian Series 60 phones
 • Hanyar da yake yada kanshi: Downloading ta Internet
 • Irin cutarwar da yake yi: yana lalata system ROM, sannan ya hana dukkan wani abu aiki a cikin ita wayar, sannan ya sake saka maka wani malware acikin wayar ka
 • Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/locknut_b.shtml

 

Sunan Virus: Fontal.A

 • Lokaci da ka fara jin labarin shi: April 2005
 • Wayar da yake kaiwa hari: Symbian Series 60 phones
 • Hanyar da yake yada kanshi: Downloading ta Internet
 • Irin cutarwar da yake yi: yana hana ta tashi, idan kuma an samu ta tashin sannan ya hana dukkan wani abu aiki a cikin ita wayar, sannan ya sake saka maka wani malware acikin wayar ka
 • Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/fontal_a.shtml

 

Yadda zaka tsare wayar ka

Babbar hanyar da zaka iya tare wayar ka daga kamuwa da wani virus tayi daidai da hanyar da ake tsare computer daga kamuwa da virus, wannan ba wata hanya bace illa kada ka bude wani abu ba ka san daga inda yake ba ko kuma baka da garantin waye ya aiko maka da shi

 • Matakin farko ka kashe Bluetooth, ka saka ta a ‘hidden’ wato kada kowa ya ganta.
 • Mataki na biyu shine ko da wani lokaci ka rinka shiga kamfanin da suka yi wayar ka kana dubawa idan sun yi wani sabon program (update) na wayar ka ka saka domin da yin haka ne suke toshe dukkan wata kafa da masu rubuta virus suka samu suke cutarwar.
 • Mataki na uku Kayi installing wani anti-virus ko kuma wani program da zai tsare maka ita wayar taka daga shigowar virus

Daga karshe nake kira ga dukkan wanda yasan yana amfani da waya musamman wayar da take da dan tsada ya rinka yin software update na wayar domin mahimman cin sa, da fatan wannan rubutu zai anfanar.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 1. assalamu’alaikum. malama wanna fadakarwa hakika ta gamsar dani da duk wanda ya zauna ya karanta. don haka gaskiya in da tambayoyi kamar haka. malama yanzu sai na shiga yanar gizo sannan inyi installing din anti-virus? kuma gashi kince dauko abu daga yanar gizo yana sa ma waya- cutar naura mai kwakwalwa(virus)