Adalacin Buhari Na Rana Daya Ya Fi Alheri Akan Ibadarka ta Shekara 60

Wane ne Adali? Duk wanda aikinsa mai kyau ya fi yawa a kan maras kyau

Rashin fahimtar yadda Musulunci ya tsara a yiwa shugabanni biyayya da kuma neman basu uzuri a kan yadda suke gudanar da shugabancinsu na daya daga cikin matsalar mu. Da kuma sanin fahimtar hanyar magabata wurin yadda suka yi mu’amala da shuwagabanni, mutanen kirki ko akasin haka.

Ina mamakin daliban ilimi da suke iya tsoma bakinsu a cikin al’amuran shugabancin kasannan wanda maganar ba ta iya barin facebook ballantana ta sami wuri a internet, amma sai ka ga mutum ya zake ya na ta kokarin fito da kanshi, ko domin neman iyawa, shahara da sauransu.

Shin a matsayinka na mai kokarin rubutu a facebook, kofofi nawa ka bude wadanda suka fi abin da kake magana sharri, da batanci ga wannan addini?

Mutane da yawa suna ganin idan aka ce bin magabata, ya ta’allaka ne kawai da dage wando, barin gemu, cin asuwaki, kullun da Jallabiyya, da dunkule hannu a cikin sallah. Bayan bin magabata ya na nufin rayuwa kan akidar da suka rayu akai da hanyar da suka rayu, hadi da yadda suke yin mu’amala da jama’a da kuma shuwagabanni. Dole ayi koyi da su ba kirkiran na ka za ka yi ba.

Amsar da Shugaba Buhari ya bayar a lokacin da aka yi mishi tambaya a kan maganar cewar masu kai Harin Kunar Bakin Wake suna yin amfani da Hijabi ne, ko kana ganin ba za a hana sanya Hijabi ba domin ganin an tsare rayuka ba. Wannan shi ne babbar fassarar da zaka iya baiwa duk wani mutum da ya shigo da irin wannan maganar.

Wanda ya yi wannan tambayar bai yi ta da niyar ya taba mutuncin addini ba, bai kuma yi ta da niyar tsokana ba, idan kuma kace ya yi ta ne domin dayan biyun wannan a matsayinka na Musulmi mai riko da Kitabu Wassunnah, fada mana inda ya furta haka. Irin wannan tawili shi ne kodawane lokaci Musulmi mai kyakkayawar akida ya ke iya yi.

Amsar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar, na tabbatar da irin zakin mulki, da karfin mulki, da kuma ganin cewar babu wani a sama gaba gare shi a wannan kasa, amma bai yi amfani da wadannan ba sai ya bayar da amsa mai harshen Damo. Duk wani Musulmi da bai san abin da sharadin magana ya ke nufi ba, to don Allah ya koma makaranta, domin tun daga kalmar Shahada sharadi ya shigo LA ILAHA ILLALLAH. Wannan kalmar ta ILLA ita ce sharadin cewar wanda ya fi cancanta da a bauta masa shi ne Allah.

To wannan amsar da Muhammad Buhari ya bayar ya yi amfani da kalmar SHARADI wanda shi ne ake kira da ‘IF STATEMENT’, wannan rubutu da kake karantawa a wayarka ko Kwamfutarka bai fito ba sai da aka yi amfani da Sharadi. Saboda haka, wannan sharadi da Shugaban Kasa ya yi amfani da shi, bayan ya yi ajiyar numfashi ya bayar da amsa cewar IDAN DAI wannan ita ce hanyar KAWAI da ake kai wannan hare-hare to za mu iya DAKATAR da saka Hijabi. Kamar yadda ake dakatar da salla jam’i a wani lokaci idan wani abu ya faru.

To a nan ya kamata mutane su fahimci cewar babu wani al’amari da bashi da asali a cikin Addini, shi wannan Addini ba bako ba ne, kasancewar shi kanshi Addinin Musulunci ba bakauyen Addini ba ne. Shi yasa a ke kallon CUTARWA GUDA BIYU.

Ga kisan kai, ga kuma Hijabi, wanne ne ya kamata a fara lura da shi, ya kamata mu tambayi kanmu, wai yaushe ne aka saukar da hukunci saka hijabi, wani hijabi ya fi cancanta mata su saka, wane lokaci da kuma wane wuri, wannan amsar tana cikin litattafan magabata na kwarai.

Shi dai addinin nan na Musulunci an gina shi ne akan kare abubuwa guda shida, abu na farko da na biyu su suka fi karfi, wato tsare martabar Addini da kuma tsare rayukan al’umma. Shi kuwa Hijabi ya na kare Mutuncin Mace ne, to idan har za ayi amfani da mutunci domin a kashe rayuka to lallai dole a nemi wata mafita.

Babu yadda za ayi a kasa wacce ta ke da Musulmai sama da miliyan 150 ace rana tsaka za a yanke hukunci hana sa Hijabi, ina ganin cewar dole sai shugaba ya zauna da Malamai, Sarakuna, Gwamnoni da kuma ‘Yan Majalisu Musulmai domin fitar da wannan hukunci, hasali ma ni sani cewar Muhammadu Buhari ba zai bada wata kafa ba ko min kankantarta ba domin a take dokar Allah.

Kuma Wallahi alkairin da wannan shugaba ya ke da shi, ya fi sharrin da ni da kai muke iya gani, sannan tsare martabar addini da zai iya yi a minti guda sai an sami malamai sama da Dubu ba su iya yin haka a Shekara Sittin ba. Shi ya sa Annabin Rahama ya fada cewa “Yini daya na shugaba adali, ya fi alkairi a kan ibadar shekara sittin” – Ibn Abbas.

Idan akwai wadanda za su baiwa wannan shugaban uzuri barin jama’ar Musulmai ne, domin sama da shekaru Talatin ake zagin iyalan Manzon Allah da Sahabbansa, amma yau an wayi gari sai dai mutum ya yi tsiyarsa a boye, saboda dokar kasa ta hana ta.

Ita wannan dokar fa da kuke ganinta ita ce zamam lafiya a wurin musulmin kasar nan. Mutane nawa ne Musulmai a wannan lokaci su ke samun natsuwa a zuciyarsu idan suka tuna, Musulmi ke mulkinsu. Ire – iren wadannan ni’imomi ba za su lissafu ba.

Allah ya kan gyara barna ta hanyar shugaba, da abin da baya gyarawa ta hanyar alkur’ani.

Babbanci tsakanin ilimi da hauka da hamasa ke nan.

Don Allah duk wanda ya ke son ya tsoma bakinsa akan abin da ya shafi shugabanci musamman na musulmi ya taikama ya karanta koda wannan littafin mai suna ‘Mu’amalatul Hukkam Fi Dau’il Kitabu Wassunnah’ – Na Abdussalam Barjas, wanda Sheikh Nasiruddeen Albani ya ce da Allah ya yi mishi tsawon rai (mawallafin wannan littafi) da ya zama aya (abin mamaki da buga misali).

Mumini kullum kyautata zato ya ke yi kuma ya bada uzuri (Don me a lokacin da kuka ji shi muminai maza da muminai mata ba su yi zaton alheri game da kansu ba kuma su ce: “Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?)

Munafuki kuwa shi ne bai kyautata zato kuma bai bayar da uzuri.

A karshe ina so mutane su sani, yadda muke da hakki a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari, haka ya ke da hakki a kan mu, hakki mafi girma da ke kanshi namu, murinka yi masa addu’a ta gari.

 

Salisu Hassan Webmaster
Shugaban Mujallar Duniyar Computer
31/12/2015

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *