Abubuwan da ya Kamata ka Sani Game da Anti-Virus Software

Idan kabar naurarka ba tare da ka tsareta daga miyagun Virus ba, abubuwa marasa kyau za su fara damun na’urar.

Anti-Virus Software mai kyau shine kawai maslaha ga dukkanin yamutsi da mugayen virus da suke damun computer da irin manyan wayoyin tafi-da-gidanka, irinsu Raila-Odinga da sauransu. Saboda haka, kada wata computer ta yi aiki ba tare da Anti-Virus ba.

Anti-Virus yana aiki ne ta wajen tace dukkanin na’urarka daga virus da worms ta hanyoyi guda biyu.

Kai tsaye ‘On-access’ da zarar ka kunna na’urar ka shi anti-virus din zai fara scanning ta karkashin kasa, ba tare da ka sani ba, zai bi dukkan kusurwoyin naurarka ya bincika yaga ko akwai bako wani cuta ko wani program da bai gamsu da shi ba ya cireshi, haka ma idan ka bude akwatin wasika wato email zai shiga ya duba ya gani ko akwai virus.

Wani lokaci, shi mutum ne da kanshi zai umarchi anti-virus din ya yi scanning babbar kwakwalwa ko kuma wata folder da kake so ya bincika ko akwai virus.

 

Ka tsare kanka daga sababbin Virus da suka shiga gari

Dukkanin wadannan bangarori na bincike virus na iya ganin virus ne da abinda aka sanar dasu cewar Virus ne (Defination), wato dukkan anti-virus yana iya gane cewar wannan virus ne, idan akwai bayanin shi wannan virus din a cikin computer. Shi yasa zaka ga idan aka sa wani abu acikin na’urarka mai virus, kamar USB Flash, Floppy Disk zaka ga anti-virus software ya gaya maka cewar akwai virus mai suna kaza, ga karfin da yake da shi wajen lalata na’ura, ga kuma irin barnar dazai iya maka, sai ya tambayeka ya cireshine, ko ya gyara shi, ko ya ajiyeshi a wani wuri da bazai iya cetar da na’urar ba, ko kuma kadama yayi komai. Zabi ya rage gareka.

To idan sabon virus ya shiga gari, ko aka sameshi a wajen canjin file daga wannan system zuwa wani system, ko kuma ta hanyar sakon email, to idan ba ka yi updating shi definition din ba to shi anti-virus din bashi da wani amfani. Saboda haka ya kamata karanchi a kalla sau daya a sati kayi updating definition na antivirus din.

Wani abin murna! Wasu daga cikin sanannun anti-virus kamar su Norton da Kerspasky da irin su McAfee, su kanyi updating kansu da zarar suka fahimci akwai haduwa tsakanin naurarka da internet (Connection).

To amma idan kana amfani da anti-virus na kyauta (Free Anti-Virus) to, shi baya yin updating da zarar kana kan internet, dole sai kace was shi anti-virus din yayi updating.

 

Kayi cikakken scanning yafi

Ka sa anti-virus yayi scanning da kanshi yafi kyau da kuma dacewa akan shi anti-virus din yayi scanning ta karkashin kasa. Saboda haka, yana da matukar mahimmanci kasa anti-virus yayi cikakken scanning na computer dukkanta, sannan a koda yaushe, kamar a kowane sati sau daya. Yadda ko zaka yi, zaka kunna anti-virus dinka  sannan ka zabi inda kake son kayi scanning sannan latsa Ok ko makamancin shi.

Wadansu anti-virus software za ma ka iya ware wasu lokuta da zaka gaya mishi cewar kana son duk sa’adda wannan rana da lokaci suka zagayo, to, yayi scanning din na’urar dukkanta, ba tare da ya shawarceka ba, ko kuma ma ya tuna maka cewar ka sani yayi scanning a ranar, yayi ko kada yayi?

 

Yadda zaka yi idan Virus yafi karfin Anti-Virus din ka

Wani lokacin koda kayi updating definition na anti-virus akan samu wani virus ya zama su kamfanin anti-virus dinka basu samu maganin shi wannan cuta ba, sabo da haka sai ya zama gashi kana da anti-virus kuma ka yi updating definition din shi ga shi kuma ya kasa cire maka virus din. To, idan haka ta faru, akwai wadansu kayan aiki (tools) wadanda suke iya cire irin wadannan virus, zasu cire kuma suyi kokarin gyara duk wata barna da virus din yayi. Idan kuma aka yi rashin sa’a babu wannan irin kayan aiki, to, zaka iya shiga internet ka samu ka samu irin wadannan kayan aiki na kyauta da suke iya cire kowanne iri virus kyauta (duba http://securityresponse.symantec.com/avcenter ko kuma http://www.vil.nai.com/vil/avertools.asp).

Wani lokacin za ka  ga saboda karfin virus din sai ya hana ka shiga ko kuma dauko irin wadannan tools din, to shima idan haka ta faru, sai ka sami computer wani, koda abokin kane, ka sauko da wannan tools (downloading) ka kwafeshi a CD sannan ka mayar da shi Computerkar.

Idan ita computer taki tashi saboda karfin virus din, domin sharrin virus yana da yawa, kaga zai iya hana na’urarka tashi, ko ya hana ta hada ka da internet ko kuma ya hana duk wani program dake da alaka da anti-virus aiki, ko ma yana asa ko a cire wani program. To shi ma idan haka ta faru, hanyoyi biyu ne, kodai ka dawo da na’urarka zuwa lokacin da tayi aiki, zuwa lokaci da ita na’urar bata sami matsalarba, ko kuma ka duba cikin kwalin da aka kawo maka na’urar akwai  CD da ake kira recovery CD ko kuma ka tashi na’urar ta safe mode .

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *