4G da LTE: Shin daya ne?

Lokacin da kake shiga internet ta hanyar mafani da wayar hannu, iya saurin da take yi wurin bude shafuka yana yin jin dadin amfani da intanet din. Idan ana maganar 4G to magana ce ta hayar da ta fi kowace saurin bude shafuka a intanet da ake da ita domin aikawa da sakon data da musayar bayanai ta hanyar kimiyar kere-kere. To mene ne 4G din nan? Sannan mene ne LTE? Mene ne bambamci dake tsakaninsu?

Mene ne 4G?

4G shine karni na hudu na ilimin yadda za a iya musayar bayanai ta hanyar kimiyar kere-kere na waya, wanda aka fi sani da 4G wato (4th Generation). Shi wannan karni Radiocommunication Standardization Sector of the International Telecommunication Union (ITC) sune suke bayar da ka’idojin da suke son kamfanonin da suke kirkirar wayoyi da su cika kafin ace waya takai wannan mataki na 4G.

Kasar da tafi shahara yanzu wacce take amfani da 4G network ita ce North America, kamfanin Gearbest yana sayar da wayoyin masu zubin 4G. Kodayake wadansu abokanan kasuwancinsu basa samun wannan damar kasancewar shi 4G din ba ko’ina yake ba a wannan kasa dole sai mutum yazo wurin da akwai wannan tsari na 4G kafin ya samu romonsa.

Mafi yawan masu ikirarin suna bayar da 4G idan masu irin wannan wayar suke zo inda wannan network yake sai kawai wayoyinsu su nuna musu 3G, amma babu damuwa idan wayarka na amsar 4G duk lokacin da ka shiga wurin network mai 4G zata koma tayi amfani da 4G mai karfi.

Musayar bayanai ta hanyar 4G ya fi sauri sosai ga mai amfani da 3G. 4G LTE wireless broadband shi kuma ya ninka 3G saurin musayar bayanai har sau goma. Karfin saukar da bayanai da LTE yake yi yana kaiwa har 12Mbps, tura bayanai kuma yana kaiwa har 5Mbps, wanda saukar da abu daga intanet yana kaiwa wani lokaci har 50Mbps. Ta bangaren saurin aikawa da bayanai da 4G yake mafi karanci 100Mbps wanda idan mutum yana wurin da network din yake da karfi saurin saukar da bayanai yana kaiwa 1Gbs.

Mene ne LTE?

LTE na nufin Long Term Evaluation wanda ake rubuta shi kowane lokaci da 4G LTE. Kodayake mutane suna daukar LTE a matsayin 4G amma shi LTE daya ne daga cikin ayyuka ko ‘ya’yan 4G, sai dai LTE muna iya saka shi a cikin sababbin karni na shiga intanet da waya.

Shi wannan technology na LTE wani hadin gwiwa ne na kungiyoyin samar da bayanai na telecommunication domin ganin an kara ingantawa da samar da sauki wurin sarrafa bayanai wanda suka kira shi da suna 3GPP ko 3rd Generation Partnership Project.

Saboda haka shi LTE kusan cigaba ne a karfafawa GSM/UMTS wurin karbar bayanai da aikasu ta waya, domin daman makasudin yin wannan LTE din domin a samu karfi ne wurin aikawa da sakonni ta hanyar wireless wanda aka fi sani da Digital Signal Processing (DSP).

LTE ba 4G ba ne

Kodayake mafi yawan mutane da suke amfani da LTE suna tsammanin shine 4G amma a bayanan mu na baya ya tabbatar da cewar LTE ba 4G bane.

Matsala da rudu da aka samu tun farkon shigowar LTE shine sunan da aka saka mishi na 4G-LTE amma inda matsalar take shine shi wannan technology na LTE bai cika sharuddan da waccan kungiya ta International Telecommunication Union (ITU) ta shardanta ba.

Saboda haka shi LTE zaka iya kiran shi da kanin 4G tunda saurin shi yafi na 3G amma kuma bai kai 4G din ba. Domin a ka’idar da ITU suka shardanta shine dole a matakin farko sai karfin shiga da fitar bayanai na intanet yakai 100Mbps. Saboda rashin kaiwar LTE wannan mataki kuma yafi matakin 3G shine 3GPP suka fitar da sabon ka’ida wacce suka kirata da LTE-Advanced.

Mene ne LTE Advance

LTE advanced kusan shine ne tsarin 4G a ka’idojin da 3GPP suka fitar. Wannan ya kara karin yazo ne a karshen shekarar 2009, amma sai dai a lokacin shi kanshi LTE din yana a kan zango ko karni na takwas ne a wurin yinsa wanda hakan ya samar da sharudan da duniya ta yarda da shi, kodayake har yanzu duniyar ba ta yarda da ka’idojin da aka daurawa LTE Advanced ba.

Shi LTE Advanced yanzu yana karnin shi na 10 ne kuma ya hada sharudi da ka’idojin da ITU suna sakawa 4G wanda a yanzu LTE Advanced yana kaiwa 1Gbps wurin musayar bayanai

Rufewa

A yanzu haka da muke magana mafi yawan kamfanonin da muke amfani da su wurin shiga intanet ko kiran waya (Internet Service Provider) suna amfani da 3G ne da LTE ne ana kuma iya fahimtar haka ne ta alamar da yake nunawa a samar wayarka domin yana rubuta karfin network din. Amma dai maganar 4G musamman mu da muke a Najeriya sai dai watakila nan gaba.

Related Articles

Responses

Your email address will not be published. Required fields are marked *